Sashe 25
Kutkale Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
...........saura kirisssssss *KUTKALE* *(PRISON)* NA *SAJIDA* Marubuciyar DUK KARYAR KADA YAR MAHAUKACIYA DAGA TAFIA DAUKAR SOJA NEMAN NA KAINA BANI DA ZABI IDAN KA RAINA INDA KAKE BAK'A CE INA KUKE MASOYAN NOVELS DINA, GANI NA DAWO DA SABON SALO, SABUWAR TAFIA, NA ZO MAKU DA SABON NVL DINA MAI TAKE *KUTKALE* WATO GIDAN PRISON, WANNAN NVL ZAI ZO MAKU DA LAMURA DA YAWA, KU BIYO NI KU SHA LABARI........ *WANNAN NOVEL NA SIYARWA NE, DU MAI SO ZAI IYA TURA KUDINSA TA wannan acct NAIRA DARI BIYU : Usman Muhammad 3072998062 First bank. Sai ya turo shaidar ya biya ta wannan number +22791466605....sannan a yi adding dinsa cikin grup, MUTANENA NA NIGER KUWA SANADIYAR RASHIN SAMUN ORANGE MONEY DA KUKE YI, KUNA IYA TURO HOTON KATIN SAHELCOM KO NA AIRTEL TA NUMBER KAMAR HAKA 91466605 SAI A SAKA KU A GRUP DIN, .....* taku ce, Sajida 1 Yannayin shigarsa , ba zai tabatar maka da shi din ko wanene ba koda kuwa ka saba gannin jalabiyoyi masu tsada, A yau , ranar da aka daura aurensa, suka dauki hanyar zuwa dauko mutanen da zasu kasance masu basu tsaro, cikin tawagarsu, da mutanen Muhammad amininsa, da mutanen Elhaj, da auntynsa da amaryar tasa kanta wace ta sha abaya sai walwali take goshin amare na kara haskata, sai shi, Jalabiya mai shigen milk ce ya saka, Bai wani gyara kasumbar da ya ajiye ba, tana nan yanda take, saima kara cajeta da ya yi ya dora hirami saman kansa, Sai takalmi da ya zura mai shige da silifas inda Muhammad ya sha farar shada ta karbe shi sai annuri yake bazawa tamkar shi ne angon, Dubansa ya yi a lokacin da ya gama shirin ya ce da shi" daurin aurenka ne zamu je fa Abdul? Abdul ya dage girarsa guda yana dubansa sannan ya ce" na *Shida* ba, ina cike da zumudin ku gama jana a kasa ku bani macen ta sakar min mara! Kansa kawai ya girgiza, domin kuwa lamarij na abdul tamkar wanda akaiwa asirin da mace? Baya iya boye bukatuwarsa da harkar mace ko a gaban waye, wannan abin ba da shi aka haife shi ba, domin ya san shi ba yau ba, sun yi karatu tare sun yi yawo tar, wannan lamari ya same shi ne daga baya, yana mai binsa da kyakyawar adu.a......yana mai cike da tausayin Ni.ima da ya fahimci irin yanda take rawar kai da murnar samunsa a matsayin miji, bai san yaya zata iya da tashin hankalin jarabar mijin nata ba bale idan suka daga baki daya suka kara yin nesa da iyayenta, wato suka juya saudiya GN ne da kansa ya laya Bodyguard din da yake ji da su maza da matan biyu rak dake iya tafia, domin kuwa biyun suna asibiti wannan rigimar sai da ta kaisu da shan matsiyacin dukan da aka kwontar da su! Da kansa Elhajin ya bi layin mazan dake tsatsaye, cikin sannin aikinsa da irin kwazonsu ya zakulo maza biyu da BS cikon na ukun domin kuwa har shi ya nemi da a laya duda irin tsadar aikinsa, A haka ya dawo wajen yan matan, dayar ta fi Hafsat tsayi, da yannayin alamun karfi, Hafsat a yannayin jikinta ba zaka taba tunaninma wai zata saka kafa a wajen nan, Dan haka ya juyo wajen GN ya maida shi gefe cikin yannayin damuwa ya ce" GN, wannan yarinyar ba zata iya aikinmu ba, ana son yarinya daya da namiji daya su baiwa Ni.ima tsaro, yarinya daya da maza biyu kuwa su baiwa mijinta tsaro ne, dayar da alamun karfi a tatare da ita, aman wannan bana jin zata wani iya wanu abu, GN cikin yannayin son a yarda da maganarsa ya ce" na yarda da formation din yarinyar, na matukar yarda da ta tsaya saman kaina a lokacin da ba bace cikin jeji, in sha Allah kwakwaluwarta mai ja ce, Yar gidan waye? Sai da gaban GN ya fadi, domin Elhaj na daya daga cikin wa.inda suka so bashi wahala sosai kan a fitar da ita a sakata wannan aikin, Aman ya ya iya, ya fada masa gaskiyar ita ce wace aka fitar daga *KUTKALE* kana nufin, matar dan ta.adan zaka bamu a matsayin wace zamu je da ita da yarda ta baiwa iyalina tsaro?, GN ya sada kansa, domin mai gidansa ne, bashi da bakin wani daga murya ko wani abin, A tausashe ya ce" *a bakin raina* Sosai abin ya bashi mamaki, a bakin ransa fa ya ce? Idan ta aikata wani abin a kama shi , idan ta kashe a kashe shi? Ya yarda ya daukarwa kansa wannan baban hatsarin a kan dan adam mai iya canzawa saboda kudi? Ko wani ra.ayi nasa mai girma ko marar girma? Kansa ya jinjina kafin ya kai hannunsa ya daki kafadar GN ya ce" zamu yo signed kan ran ka! Aman kuma ba ita zata baiwa Ni.ima tsaro ba, sai dai ta hadu da baban yaronka su baiwa Oga Abdul Jabar tsaro! Ka ga a wajen namijin mun dauki wanda ya kware mun hada da Abdul, a wajen macen mun dauki wace ta kware mun hada da Ni.ima, Murmushi GN ya yi a fili mai cike da ma.anoni, kafin su tatara su je a yi du abinda za.a yi, a tarkata su su dauki hanya , suna zuwa cikin gari suka dauki jirgi suka juya inda suka bar Aunty da mijinta, Suna dira baban gidansa suka zarce, Kowa na neman hutu banda masu tsaron su, da kuma shi kansa uban tafian, A lokacin da ya ga Hafsat tsaye a bayansa matsayin wace du inda ya kutsa ta kutsa sai da ya rike kugu ya dafe habarsa ya kare mata kallo tun daga kafarta hat kanta sannan ya yi kwafa a ransa ya ayyana....yanzu wannan ai almubazaranci da sakani a uku ne, toh mana, maimakun na yi ta raina kadai sai na hada da ta jaririyar nan, idan ba son banza irin na iyayenta ba, ya zasu dauketa su kaita irin wannan aikin da sai mazan wajen sun gama kwakule masu yaya sannan a koya masu abubuwa irin na karti, su juye su dawo bawa karti tsaro? Wai yanzu wannan yar jaririyar ce zata kare wani abu ya same ni, ni wannan uban da ni, da na yi imanin da na yi aure da wuri da na zubawa matar cikin yan hudu irinta? Haka ya juya ya shige inda Hafsat ta sha mamakin ashe wannan bakin mutumen mai sifar samudawan ne za.a baiwa tsaron? Ita walahi du ji take wancen balaraben mai sifar yayan gatan ne za.a baiwa tsaron, domin sam ba.a basu fuskar wata tambaya ko wani cikaken bayani a kan wannan aikin ba, dan kuwa Oga ne da kansa a tsaye a wajen wanda ita saima a ranar ta fara ganninsa da sannin matsayinsa a Niger. Biye take da shi a lokacin da ya fito daga dakinsa, inda BS ya bita da kallo, ya so ace shi aka baiwa wannan aikin mai hatsari na ko menene sai ta fara duba zai iya anfani da shi, ko zai ci kai koma menene, ya so ace shi ne da wannan abin ba dan komai ba sai dan a yannayin aikin, wannan mutumen na cikin hadari sosai, wanda sai an yi da gaske, an baza ido, an baza komai kafin idan da rabo a samu galaba.... Kansa ya sada ya sauke ajiyar zuciya sannan ya juya ya ja dayan suka ci gaba da bincikar gidan lungu lungu da kayan aikinsu...... Shi dai bai ce da ita ta koma, ko ta tsaya ba, har suka karaso kofar dakin Ni.ima, wanda suka tarar da Bodyguards dinta tsaye bayin Allah kowanne a kame waje guda, Sai da ya tsaya ya kara kama tsatso, wanda yake kamar sabonsa ne, ya kare masu kallo, Murmushi ya yi a fili, shi walahi an kawo masa nishadi, yo nishadi mana, wanna lamari kamar gunkina? Ba um bare umum, du sun kame suna jiran uwar gidansu, shi ko a million goma a wuni ba zai iya irin wannan aikin ba! Bude masa namijin ya yi ya shiga, sai dai ga mamakinsa, yarinyar dake biye da shi itama ta shigo, Tsayuwa ya yi ya juyo ya dubeta, sannan ya kai dubansa wajen Ni.ima da ta mike da sauri daga ringeshen da ta yi cikin riga da wandonta na barci , Sai da ya ciro harshen sa , ya lashi lebensa na kasa sannan ya kara dubansu a tare, Wani murmushin yan duniya ya yi, ya rike tsatsonsa ya dubeta da kyau kafin ya ragewa idannuwansa girma su dawo kalar baci ya ce" ni dai a sanina mace daya aka daura min aure da ita a yau, kuma wajenta na zo dan ta kama wannan abin ta rage masa nauyi ( ni dai wannan labari a hargitse yake dan sakin magangannun ciki), Da hannunsa ya nuna inda yake nufin a ragewa nauyi, wanda hakan ya saka su a tare rintse ido daga Hafsat din har Ni.imar, dan kuwa ba warda ta yi tunanin, ko a tsuman ranta cewa abinda zai aikata kennan, Ci gaba ya yi da magana bayan ya wani rausayar da kai ya ce" zuwa na yi na kwonta da matata, ko yar biyu za.a yi? Ya fada yana mai fitarwa da Hafsat gaba daya idannuwansa, sai kuma ya ja wani yaji yaji ya ce" ko a zina ba kyai hada biyu, bale yanzu na bar zina, kin ga ki dan fita na gama sai ki maida ni daki ko? Hafsat kam, yau ta ga ubanta a rashin kunya, yau ta ga ikom Allah, da hasken gari ba wai dare ya yi ba, kiri kiri, ra.aine da ra.aine, kunne da kunne, ya dubi tsabar idannuwanta, da na wace a tunaninta a yau aka daura aurensu, ya gangantsaro wadinnan gantsara gantsaran magangannun? Sai da ta lumshe idannuwanta ta hadiye wani yawu makwat, sannan ta daga kafafuwanta ta shiga kara saka kanta cikin dakin tana mai nufar....... Comment plz *KUTKALE* *(PRISON)* NA *SAJIDA* Marubuciyar DUK KARYAR KADA YAR MAHAUKACIYA DAGA TAFIA DAUKAR SOJA NEMAN NA KAINA BANI DA ZABI IDAN KA RAINA INDA KAKE BAK'A CE INA KUKE MASOYAN NOVELS DINA, GANI NA DAWO DA SABON SALO, SABUWAR TAFIA, NA ZO MAKU DA SABON NVL DINA MAI TAKE *KUTKALE*