← Book details Kutkale Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 22 OF 94

Sashe 22

Kutkale Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

irin tasa rayuwar ta yanzu, wace yake tantiri fitinane a idon mutane da yawa, Kai innalilahi wa.ina ilaihi raj.une, shi kam bai ga ranar kudi ba, Kudi sun saka familynsa a halaka, Shi da kudin nan na haramun ne, ba zai zauna a cikinsu ko na second daya ba, Sai dai kudin irin gadon nan ne na iyaye da kakani, Irin kudin nan na da, manyan kudade da kadarori masu albarka, shi shi daya, A hankali ya kai idannuwansa kan wandon dake jikinsa, Jikinsa ya ga ya canza yannayi kamar yanda ya ji a jikinsa.... *mace* yake bukata, mace yake so a yanzun! Wannan lamari ya saka shi dora hannauensa gaba daya saman kansa, wannan wace irin masifa ce aka hada shi da shi? Shi kennan za yana jin bukatar mace kamar yanda yake da bukatar cin abinci a kowani lokaci? Ni.ima ce ta fado masa a rai, Ya yi mata zuwan biji biji, wanda bata taba sannin.harkar nan ba aman sai da ya mata zuwa biyu, wai a hakanma ya mike yana shan iska ya koma ne yarinyar nan ta fado masa daki, Juyawa ya yi ya kurawa waje guda ido, kafin kuma ya saki murmushi, a fili ya ce" makashi, baka da mutunci, wato so ka yi ina ciki ka kashe ni, na jibgunma yarinyar mutane sannan kowama ya ga tsiraicina ko? Harda wannan piciciyar yarinyar domin sai an zare ni daga jikin Ni.ima.... Murmushi ya yi ya juyar da kansa yana mai hangen maganin da ya saya da niyar fara sha, domin ba zai koma harkar da yake a da ba, baya son komawa, ya gwamace ya yi ta kawo matan a matsayin na aurensa yana bin dakin kowace kowani dare har ruwan jikinsa ya kare idan ya mutu ai shikenan kowama ya huta! Haka ya yi ta abu, bayan ya sha maganinma shi dai ya ji ya dan rage nauyi, aman ba wai wani sakayau ya ji shi ba, Dan haka alwallah ya dauro ya zo ya hau darduma ya shiga gabatar da sallah. Ta jima tsaye wajen da ya fice, idannuwanta lumshe, gaba daya ta raja.a tunaninta kansa , yannayinsa, irin abubuwan da yake yi tamkar mai aljannu, kai harma da irin yanda ya shigo da ita da niyar kowace wace, aman kuma da ta tabata ta tabo gaskiya cikin lamarinsa sai kawai ya fice a dakin, He's a brave man? Or Bodyguard? A wannan tunnanin ta silale jikin karfen ta jinginar da kanta, Zurfafa ta yi a tunanin da kulawa da kuncewa, A fili, kuma muryarta na rawa tamkar zata fashe da kuka ta ce" *shi, nasa iyayen basama duniyar*, Hawaye ne suka shiga bin kumatunta, hawayen tausayin kanta, da kuma kulaliyar maganar da ta tsinta tasa, innalilahi-wa-ina-ilaihi-raj.une. Lamarinka, lamarinka ya fi nawa hargitsi..........zan san ko kai waye! Washe gari karfe tara na safiya ya fito daga dakinsa da ya sakawa kys ya gama ibadarsa ya huta , Tun da ya bude ya fito, su su uku dake tsaye suka dan juyo dan gannin wanda ya bude dakin, Su duka sun sha mamakin a yanda ya bayana yau kuma, Hashin kansa da ya taran nan ya zauna ya bashi lokaci wajen yi masa gyara irin na samarin america , wato askin nan na yan basket ball mai salo da kyan kallo a ido, sai dai sak irin na yan duniya ne! Ya rage bajewar sajen fuskarsa ya siririnta shi a fuskar tasa, haka kuma gemunsa ya rage shi sosai ya bar dan kadan da ya yiwa fuskar das da ita ta bada kala, Lebensa na kasa ya fi na sama girma, yau wajen broshing ya sha garzar da ya saka ya dawo fresh yanda yake da, wato kalar pink mai dan duhu duhu da shi na kasan na saman kuwa baki, Kamar wanda ya caje gashin idonsa, yannayin kulawar da ya bashi da kayan kulawar ya saka harta da gashin idon nasa ya yi tsai kamar barkonon tsohuwa kirikiri ba tsoro ba kunya yana kallon mutane, haka kuma dara daran idannuwansa sun kara fitowa suna kallon du wanda ya kale su ido cikin ido, BS da jibrin suka juyar da kansu daga dubansa inda Hafsat gabanta ya yanke ya bada wani irin sautin da bata shirya ba, hakan ya sa ta lumshe idannuwanta tana adu.ar da ta bata karfin gwuiwar controling din abinda take ji wanda ta baiwa kanta amsar hakan ya faru ne dan jiya ta ji wani yanki na sirrinsa , yau da take tunanin ba zai iya mikewa bisa kafafuwansa ba sai gashi ya fito a ba zata, cikin yannayi na karfi,.....eh ta yarda da abinda Ni.ima ta fada a yanzu da safe da ta je gannin ko can ya kwana dan ta dora masa break fast ta tarar da ita zaune bakin bed ta fito a wanka daure da tawul tana gyara fuskarta cikin yannayi na kamar ba abinda ya dame ta, Da ta tambayeta sir fa? Sai ta tsura mata ido, can kuma ta girgiza kai ta ce" bai shigo ba tukunnan, Har hafsat din zata juya ta ji ta ce" Bodyguard, Juyowa Hafsat din ta yi tana kallonta, nan Ni.ima ta mike daga zaunen da take, ta nufota da wata irin tafia ta tatata ta tsaya gabanta ta ce" ki kular min da tashinsa, zaman sa, motsin sa, cin abincin sa, komaima, hakin kula da shi a wuyan ki, idan har suka cin masa....ke kika kashe shi, ni kuwa ina numfashi ne da numfashin sa, kin ga kin kashe rai biyu! *Ina son mijina, komai irin halayensa* tunaninta ne ya katse, sanadiyar jin an dauke hular gashin da ta dora ta yau mai shigan blonde, Da sauri ta zaro ido sakamakon farar rigar dake cikin Costume din jikinsa da ta hanga domin ya matse mata waje irin sosai din nan, Da sauri ta saka hannayenta ta tare hular gashin wace a lokacin da tana kanta tamtar irin fararan americain din nan, aman yana cirewa ta dawo kamaninta irin filanin nan masu dukan ido da zuciyar mai kallon su. Da wani irin yannayi ta dago da dubanta ta kai wajen hular gashin, ya riketa taf ya ki sakar mata abinta, Dubanta ta maido kansa, Sai da gabanta ya yanke ya fadi sanadiyar idannuwanta da ta saka cikin nasa, Wani nauyi ta ji idannuwanta na neman yi mata , sai dai ta ki ta cire dubanta a kansa danma kar ya dauka wani tsoronsa ko wani abin ne, Tana kallonsa shi ya lumshe nasa idannuwan, sannan ya fuzge hular gashin ya jefawa BS da ya kuma juyowa jin shirun ya yi yawa, A gimtse ya ce" ni da ba arne ba, yaya za.a ringa bina da gashin arnawan! Shi dai BS tarewa ya yi ya mikawa dayan abokin aikinsa, shi kuwa ya juya da gudu ya koma ya ajiyeta ya dawo, Gaba yake, tafiya yake hankalinsa kwonce, takalman kafarsa sau ciki bakake sidik sababi fil sai bada kala suke a cikin yannayin tafiarsa, Bayansa Hafsat ce itama sanye da bakaken kayan wando da riga, sai bakin gashin kanta dake fili ba dan kwali, sai gilas baki da ta saka dan madaidaici tana lure da dukan wani motsins, wanda gilass din na aiki ne. Motocin da aka janyo ne ya saka shi dubansu, wasu motoci ne da ba nasa ba, Aman bai yi tambayar ko na waye ba, dan ya san ba zai fice su suka kawo su ba, Maduban motar da aka bude masa ya shiga ya duba, Bayan ya zauna Hafsat na zaune facing dinsa, BS na gaba kusa da direban da su suka kawo abinsu, ya mika hannu ya daki madubin motar wanda hakan ya saka su kallon shi gaba dayan su, Murmushi ya sakar masu ya dage girarsa guda ya ce" dan na kara yarda idan har wanda bulet din baya ratsawa ne, Kunfa fara jan attention dina, ba laifi kuna kokari..m Ba wanda ya bashi amsa, saima hankulansu da suka maida bakin titi ana jan motar, Irin kallon da yake binta da shi, irin tsareta da idannuwansa da yake ne ke sakata tsarguwa walahi, Banzan kallo ne da shi, irin kallon nan na kurewa mutun waje, A hankali ta sosa keyarta , Ta kale shi a sace ta ga dai shi ko.ina na jikinta ne yake bi da kallo, Gashin kanta ta saka hannunta sosa, ta kara sosawa irin ta samu kwarin gwuiwa ko zai gane ya daina yi mata wannan kallon, Aman tana kuma dubansa ta ga ita din dai yake kallo, Gilashin idonta ta cire, ta wara kafafuwanta, ta dora hannayenta saman gwuiwoyin kafafuwanta ta tsura masa idon itama tare da cuno bakinta da kuro idannuwant a irin kale ni da kyau din nan Murmushi ya saki shima ya yi exactly yanda ta yi , hannunsa ya dago ya ka8 wajen hancinta da nufin shafawa, sai dai ta kauce tana hada fuska, Sai da ya kara sakar mata murmushi ya ce" idan ba Allah ba, ba wanda ya isa ya zana mutun ya fito das da shi, ke wollah kina da kyau, wa kika biyo? Maman ki ko baban ki? Da mamaki ta dawo da dubanta wajensa, sai dai bata gama mamakin hakan ba ya ci gaba da magana hankali kwonce, wanda du abinda yake fadi kowa na jin sa, ya ce" kin ga, kyakyawar halita da ke, yar caras, ga kugu... Ya saki murmushi , ya ci gaba da fadin...ga gashi, ga ido, ga dogon hanci, ga dan baki mai dadin tsotsa ..... Murmushi ya kuma yi, ya ce" ke karantar jikinki da kasancewarki gardi kawai ya bata, kin ga jikin ki karami ne sosai, haba namiji na son ya ringa damka, ba wai ya ringa tsakura ba, kuma yana son ya ji lema ba wai kamas ba, Kin ga yawo jiki a bude, na busar da mace, ruwan jikinki yanzu haka ba komai , du ya tafi, haka kuma Shut up! Ta fada ranta bace, fuskarta har ta yi ja dan masifa.... Sai fai kafin ta yi shiru da hakan muryarsa ta daukaki tata, ta fi tata nuna masifa ta hanyar fadin" *u shurrrp!* Karya na maki ne? Uban me ya kawo ki harkar aikin da maza ke yi kuma ki ce sai an kiyaye harshe wajen yi maki maganar da ake
Chapter 22 · 0% Book details