← Book details Kutkale Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 55 OF 94

Sashe 55

Kutkale Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

yi masa wani kallo, kamar ba shi ne yanzu ya shige sun fahimci juna ba hakan ya kara sakawa Muhammad dar dinsa yana kallonsa ya fice a dakin ya nufi masalaci Wata irin zabura ya yi tsaye ya bi bayansa ya ga ya tafi bai labe masa a bayan kofa kamar yanda ya saba taka tsantsan ya dawo ya dauki wani wandon yana mai jan wani uban tsaki a fili ya ce" mu zuba ni da kai, zan koya maka aikinka banza kawai! Abdul na gama sallah sai da ya hantse tare da su BS Suna fitowa ya shiga shawagi tsakar gidan, inda BS ke biye da du wani takunsa hakama Hasanna dake jiran shigowarsu daga masalacin, Waje waje suka shiga bi a cikin gidan nasa kama daga lambu, wajen motsa jikinsa kai du wajajen da ya san yana zuwa ya zauna da Hafsat dan kawai ya tsokaneta ya bibi karshe ya tsaya a kasa shukar mangwaron dake shuke a tsakiyar gidan ya kurawa inda take yawan tsayuwa ido sai kuma ya saki murmushi ya girgiza kai dan kuwa har irin hararar da take binsa da shi idan ya yi wani abin yana hankalce da ita kawai yi yake tamkar bai ganta ba Yana murmushin sai kuma ya gimtse fuska yana satar kallon su BS, tabas BS na cikin muguwar damuwar rashinta, yana hankalce da shi sai dai bashi da damar nunawa ko zakewa a lamarin dan a karkashinsa yake a yanzun Kansa ya girgiza ya kai hannunsa na dama ya shafa uwar sumar da ya tara a kansa da sajen da ya tara tsabar damuwar da yake ciki sai kuma ya saki hannun nasa ya dantse lebensa na kasa yana kallon wajen dai bai kawar da idannuwansa ba yana mai ayanna ya Allah ya bayana masa wanda ya dauketa da ransa ido da ido! Muryar BS ne ta dawo da shi hayacinsa, sanyin safiya dalbeji sai kadawa suke da shuke shuken cikin gidan, A hankali ya kai dubansa wajen wada BS ya dakatar kar ta karaso wajen Abdul Ido ya tsura mata, Du ta fita hayacinta tamkar ba ita ce ta shigo da iya yi da kisisina da tarin iskanci a tare da ita ba, A yanzu haka fitowar da ta yi doguwar bakar riga ce jikinta, gaba daya jikin nata sai rawa yake, hannayenta ta dago ta maraoraice fuskarta ta budi baki da kyar ta ce" ka taimake ni, kashe ni zai yi Idannuwansa ya zaro, inda yana wulaga ido ya ga jan hasken abin harbi a jikin bishiyar dake kusa da shi, da sauri ya maida hankalinsa kanta sai dai me, BS da ya zabura da hanzari dan riketa ya yi wata irin juyowa da gudu yana ihun su tare Abdul su kare Abdul, Wata irin girgije Hasana da ta je da niyar jan sa da karfi ta kai shi maboya ya yi kafin ya karasa da gudu inda aka harbeta a baya daidai kahon zuciya wanda ya sakata take wani irin abu tana zubar da jini ta bakinta idannuwanta na yin sama sama tana hahakewa , Mikewa ya yi shima da gudun balaki ya rufawa BS baya dan zuwa inda suke tsamanin an yi harbin, sai dai abinda suka tarar mutun yashe da shigar masu harbin nesa da alama an shamace shi a lokacin da ya yi harbin shima an harbe shi kuma duka kaf haka ba tare da an ji karar harbin ba Lokaci guda kuma aanguwar ta kwashi kukan laluwa dan kuwa BS ya shaidawa polisai an kuma yin wani harbin, nan da nan maganar har ta hau sama wayoyi sun shiga kuka suna neman maganar Abdul, Abdul ya jinginar da bayansa jikin garun wajen yana mai kallon gawar nan, Dubansa ya maida tsakar gidansa inda aka yi harbin nan ya ga har an sakata cikin wata bakar jaka irin ta rufe gawa an dora gawarta saman gadon asibiti an shigar da ita cikin ambulance Yana nan tsaye sai ga baban sojoji wanda yake aboki a gare shi ya hayo da kansa inda suke tsaitsaye, Sai da ya dan ja ya kale shi kafin ya sara masa dan kuwa du girman sa girman aikin Abdul ya zarce nasa, Wajen BS ya je inda BS kuwa ya sara masa, ya karbi bindigar yana jujuyata sannan ya kali BS ya ce" shi kadai ka samu a tare da shi? BS ya gyada kansa yana kallonsa, Mikewa ya yi ya dawo wajen Abdul ya tsaya ya ce" kar ka tayar da hankalinka abokina, zamu je da gawarwakin nan asibiti likitoci su bincika dan gane shi wannan sabuwar gawa ce ko tsohuwa? Abdul dake bin bakinsa dake magana da kallo ya lumshe idannuwansa ya kuma bude yana kallon sa, A hankali ya daga kafarsa ya taka ya je inda gawar ke kwonce wace aka hayo itama da niyar a rufe ta a tafi da ita ya duka wajen gawar ya saka yatsarsa mai bin banar yatsar a dan ramin harbin inda ya dangwalo jinnin dake baki baki wanda bai yi tauri ba gayanan shar a hannunsa ya dago da yatsar ya nunawa Baban sojojin mai suna Ahmad ya ce" wannan sabon harbi ne, domin jinnin da duminsa sannan bai yi kauri ko ya dunkule ba, Ahmad ya kale shi da kyau kafin ya ce" aman, me hakan ke nufi? Abdul ya karasa bakin windows din da daga nan aka harbi matar ya tsaya a hankali ya ce" hakan na nufin *Makashina na kusa sosai da ni, hakan na nufin makashina na cikin wannan benen a wannan lokacin* Da sauri Ahmad ya matsa kusa da shi ya ce" ga polisai da sojoji du sun cika wajen sai bincike suke, gashi du mutane sai kaura suke daga anguwar babu wasu mutane da yawa bale har ya shige cikin mutane ya bace mana, ko cikin benen nan mutanen basu fi hudu ba du irin girman hotel din nan, kuwa, kar ka damu zamu same...... Kafin ya karasa muryar Muhamad ta karaso wajen, ya shigo da sauri hankalinsa a tashe ya nufo Abdul, Ba wanda ya dakatar da shi sai dai binsa da kallo da mugun tausayin irin yanda ya damu da lamarin aminin nasa Shi kansa Abdul ido ya kura mada har ya karaso ya rungume shi a jikinsa ( kun san ai larabawa saka mutun a jiki a wani abu bane, hakan gaisuwa ne ko nuna an damu da mutun), yana rungume shi ya ce" innalilahi wa.ina ilaihi raj.une, ya Abdellah, kana gannin bakin cikin rayuwa, irin haka sai ya saka mutun ya haukace ko zuciyarsa ta buga Abdul ya lumshe idannuwansa ya damki hannunsa sannan ya cire shi daga jikinsa ya kuma lumshe idannuwansa ya bude, sai kuma ya yi wani dan malalacin murmushi ya ce" Muhammad, ka daina tsawalawa kanka damuwar nan, ji yanda zuciyarka ke bugawa, yannayin numfashinka na sauka da sauri sauri tamkar wanda ka yi gudu, haka kuma jikinka ya dauki dumi, sannan bana so kana zuwa inda nake a irin lokacin da ake harin rayuwana, Muhammad idan wani abu ya same ka zuciyata zata tsaya, bana tunanin zan iya ci gaba da tafia a matsayin mai hankali Idannuwansa ya rintse da karfin gaske ya bude su inda suka kara rikidewa ya jimke hannayensa ya kaiwa garun wajen naushi da karfin murya ya ce""" *KUTKALE* *(PRISON)* NA *SAJIDA* Marubuciyar DUK KARYAR KADA YAR MAHAUKACIYA DAGA TAFIA DAUKAR SOJA NEMAN NA KAINA BANI DA ZABI IDAN KA RAINA INDA KAKE BAK'A CE INA KUKE MASOYAN NOVELS DINA, GANI NA DAWO DA SABON SALO, SABUWAR TAFIA, NA ZO MAKU DA SABON NVL DINA MAI TAKE *KUTKALE* WATO GIDAN PRISON, WANNAN NVL ZAI ZO MAKU DA LAMURA DA YAWA, KU BIYO NI KU SHA LABARI........ *WANNAN NOVEL NA SIYARWA NE, DU MAI SO ZAI IYA TURA KUDINSA TA wannan acct NAIRA DARI BIYU : Usman Muhammad 3072998062 First bank. Sai ya turo shaidar ya biya ta wannan number +22791466605....sannan a yi adding dinsa cikin grup, MUTANENA NA NIGER KUWA SANADIYAR RASHIN SAMUN ORANGE MONEY DA KUKE YI, KUNA IYA TURO HOTON KATIN SAHELCOM KO NA AIRTEL TA NUMBER KAMAR HAKA 91466605 SAI A SAKA KU A GRUP DIN, .....* taku ce, Sajida 4 Cikin yannayin rashin tsoro da kyama take duban keayar idannuwan Muhammad dake dan langi sakamakon kwayoyin da ya hadiya ta shiga mayar da zancen duka kaf da ta gano wajen bincikenta, da irin sato tan da suka yi shi da sojansa mai bashi goyon baya, da komai da komai Sai da ta ja numfashi ta kai dubanta wajen BS da har jikinda bari yake tsabar firgita da ikon Allahn nan, ya ga lamari da yawa, ya ga gaba da yawa, aman bai taba gannin ci amana irin wannan ba Idannuwanta cike da hawaye ta ce" wannan da kake gani, wanda ba zan iya kiransa da madaukakin sunna irin MUHAMMAD ba, domin ya kasance azalumi, mai izgili da rashin tsoron Allah, wannan aljanin mutumen wanda ban ga sunnan da ya dace da shi a musulunce ba! Ta kuma rinyse idannuwanta sannan ta ce" *shi ne mai kashe kashen nan baki daya ban cire maka ko daya ba, kuma yana yi ne dan vengeance* Sai da BS ya dafe gaban kirjinsa dan luguden kidan da yake masa, Dubansa ya kai wajen algungumin a daidai lokacin da ya daga hannunsa ya nuna Hafsat ya ce" karya ne! Gindin bindigarsa ya saka ya daki keyarsa hakan ya katse masa fitsarar da ya dauko a bakinsa ya silale wajen a sume Da kallo ya bi shi sannan ya bada umarnin a nufi asibiti da Abdul da Hafsat Shi kuwa ya dadaure Muhammad dauri irin na huhun goro sannan ya shiga bincike da harhada du abubuwan da zasu isa cikaken shaida haka kuma ya tabo ikon garin wa.inda bai isa ya aiwatarwa da Muhammad wani abu ba sai abinda aka yanke masa a kotu A lokacin da aka saka masa ankwa bayan sun dankara masa wata gigitaciyar allura mai taba kwakwaluwa aminin Abdul mai sunna Ahmad ya yi tsai yana kallon motar da aka shigar da shi baima san inda kansa yake ba, Tabas shima ya girgiza, sai dai da wuri ya kwabi kansa a lokacin da ya tuna cewa Muhammad fa mutun ne, dan adam ba, dukan abubuwan da ya
Chapter 55 · 0% Book details