← Book details Kutkale Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 63 OF 94

Sashe 63

Kutkale Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

SIYARWA NE, DU MAI SO ZAI IYA TURA KUDINSA TA wannan acct NAIRA DARI BIYU : Usman Muhammad 3072998062 First bank. Sai ya turo shaidar ya biya ta wannan number +22791466605....sannan a yi adding dinsa cikin grup, MUTANENA NA NIGER KUWA SANADIYAR RASHIN SAMUN ORANGE MONEY DA KUKE YI, KUNA IYA TURO HOTON KATIN SAHELCOM KO NA AIRTEL TA NUMBER KAMAR HAKA 91466605 SAI A SAKA KU A GRUP DIN, .....* taku ce, Sajida 4 Jiki a sanyaye ta ce" idan zaka iya aurena a yanda nake, ka zauna da ni a haka, ni me zai hana na amince da soyayarka? Daidai sun karaso aeroprt kennan ya ja ya tsaya yana kallonta, Wani murmushi ya sakar mata kafin ya ce" da Sire ya salame mu, zaki gan ni, zan zo neman aurenki, zan koya maki so na domin kuwa a yanzu ba sai an fada min ba, ba soyayata a tare da ke, bana son ki amince min dan kina tunanin na cancanci haka, ina so ki so ni dan na cika namiji Shanyayun idannuwanta ta lumshe sannan ta bude motar ta fita Nan wajen motar suka zauna har aka kawo malan cikin wata motar harda masu yi masa rakiya Suna sauka basu jima sosai ba jirgi ya sauka , man ya kara kwasar yan Niger suka daga Malan da Hafsat sai dai su sakarwa junna murmushi lokaci zuwa lokaci A lokacin da jirgi ya sauka motoci ne suka zo daukan su wa.inda ta yi mamakin hakan, Sai dai a lokacin da suka zo shiga ta gane daga abdul ne domin mai jagorar motocin ya shaidawa Malan daga wajen Oga Abdul Jabar ne Shiru sukai cikin motar mai sanyi ga kamshi su duka, A lokacin da aka shigo anguwarsu sai ta ringa jin gabanta na matsananciyar faduwa, Du masu zazaune da ido suka ringa bin motoci ukun dake shigewa da matsiyacin gudu har suka ja suka tsaya kofar gidan malan Dubansa ya kai kan Hafsat da ta yi tsuru da ita, gashi wando dogo ne a jikinta sai dan kwalin da ta yane kanta da riga mai dan dogon hannu aman kuma bata da wani tsayin a zo a gani A hankali ya ce" bakya murna ne??? Da sauri ta kai dubanta kansa, sai kuma ta sada kanta, Tunaninta idan ta fita a irin wannan shigar da wannan yannayin me mutanen anguwar nan zasu kaleta da shi? Ta tabata koda za ta bi layin da ihun rantsuwar ba daga yawon bariki take ba, ba wanda zai yarda sai dai ma a kara tsanarta A hankali malan ya ce" menene mamana? Idannuwanta da suka cika da kwallah ta dago ta kali mahaifinta, Sai da ta ja hanci sannan ta ce" Abana, idan na fita a haka, zan kara jaza maku zagi ne da kai da mamana Murmushi ya saki wanda daga zuciyarsa ya fito, a cikin ransa ya furta alhamdulilah, ko ba komai duniya ta ladaftar masa da yarinyarsa, yo da da ne ko shigar da ta fi haka muni zata saka kafa ta fice abinta ba abinda ya dame ta da wai kar a zageta ko ta ji kunyar wani ba, a haka kuma idan mai tsautsayi ya yarda ya yi mata wani kallo su cashi junna Hannayenta malan ya riko yana kallon yanda du ta takure kanta, cikin nutsuwa ya ce" ki ji tsoron Allah Uwata ba wani ba, kin ji? Mu tafi Ajiyar zuciya ta sauke tana kallon yanda Almajirai suka tataru suna masu nuna murnar gannin malan ne ya dawo harda yan rakiya a yau tsal , da yake yama ta yi sosai mutane du sun dadawo daga nema Malan ya fara fitowa , nan ya shiga mikawa jama.ar hannu suna gaisawa cikin harda baban dansa A hankali ta sako kafarta mai sanye da takalmi sau ciki mai dan tudu baki kirin na aiki Gaba daya hankalin mutanen ne ya fara yowa wajen, a haka har ta fito gaba dayanta Ai kuwa magangannu ne kasa kasa suka fara tashi, ba dan ba.a saba ganninta da shigar wando da riga ba, ba dan ba.a saba ganninta da takalmi , kai kanta ko fan kwali bata sakawa a da aman a yanzu da dan kwalinta a rufe a kan hakan bai hana mutane mamakin ganninta harda fadin ta dawo daga yawon kennan Wasu kuwa kasa kasa su ce ita kuwa ba zata shiryu ba jiya i yau? Duniya ta horata kennan? Kiri kiri wajen ya nemi hautsinewa da dan hayaniya dan kuwa har matan anguwar sun fara lekowa ganewa idannuwansu wai da gaske UWAR malan ce ta dawo? A hankali ta zagaya mazan nan da suka tare hanya ta shiga cikin gidansu Tana shiga ta tarar da wata bakuwa bakin baban fanfon tsakar gidan ta tara abin wanke shinkafa tana tarar ruwa da alama girki take yi Tsayuwa ta yi tana bin gidan da kallo, dan kwata kwata ta shagala da shaukin ganninta a gidan ko salamar ma ta kasa yi Matar ce ta tsura mata ido tana kallonta dan bata santa ba, batama taba ganninta ba kanwa take a wajen daya daga cikin matan malan ta zo hutun makaranta ne A dan kiririce ta ce" ke, ke kuwa wacece malama zaki shigo gidan mutane da irin wannan shigar tamkar arniya ko an fada maki gidan nan yana daukan arnawa ne?? Da sauri ta kai dubanta kan matar, dai dai nan matan gifan suka fara fitowa jin hayaniyar nan, haka kuma daidai lokacin malan ya shigo cikin gidan Gannin Hafsat tsaye ya ce" aa, Uwata me kike tsaye nan sai kace baki san waje ba? A daidai lokacin da ta juyo dan kallon malan kunnayenta suka jiyo murya a hankali cikin zazakar muryar nan irin nata an ce" *ANMIH* Da sauri ta juyo haka kuma lokaci daya ta damko hannun mahaifinta Shima tsayuwa ya yi suna kallon mahaifiyarta dake sanye da wani zumbulelen hijab mai ruwan milk wanda ya rufe mata ilahirin jikinta sai hannunta da fuskarta dake waje, Tsaf tsaf da ita sai yar ramar da ta yi aman fatar jikinta lufluf daga fuskar da kuma hannayen Sai da ta lumshe idannuwanta, hawayen dake ciki suka fito sannan ta dago mata hannayenta irin ta zo din nan Hannayen malan ta saki ta daga kafarta da mugun gudu ta je ta fada jikin mahaifiyarta lokaci daya kuma ta fashe da kuka..... Tana kukan ta ce" baki yi fushi da ni ba? Ashe ba zaki juya min baya ba? Du laifin nan da na yi maki Ummana? Bayanta take taping a hankali, sai a lokacin ta tuna a tsakar gida suke kuma ta tabata abokanan zamanta na wajen, A hankali ta zame jikinta a nata dan a duniya irin mugun kawaicinta da kunyarta? Tana zamewa ta sada kanta bata kuma kallon kowa ba ta shige ciki tana share hawayen kukan farin cikin da ta yi, Tana shiga Malan ya saki murmushi, yana matsayin girmama lamarin matar nan tasa a nan gidan duniya, sam bai bata labarin inda mamansa take ba, rana tsaka ta shigo gidan da shiga irin ta wada ba.a so, aman bata mike ta shiga jaye jayen jafa.i da mugayen magangannu ba sai nuna tsantsar farin cikinta da ta yi har ta kasa boyewa, bata yi mumunar magana kamar cewa daga yawon duniyarta take ko makamancin hakan ba, sai riketa da ta yi ta nuna mata ta yi missing dinta haka kuma halayanta ba zasu saka ta gujeta ba, Yana kallo Hafsat ta gaisar da sauran matayen nasa da suka yi cirko cirko wasu na tsoron jarababiya ta dawo, wasu na mamakin wani abin sai a gidan malan yarinya ta je ta yi yawon duniya ta dawo gida anai mata oyoyo Basu iya amsata ba, sai saurin kauce mata suka bata waje ta shige wajen mahaifiyarta Juyawa ya yi ya fice a gidan bai ko amsa gaisuwar da suke yi masa na sannu da zuwa ba, dan ba zai iya rufe ido a irin lamarinsu ba Babar dake cikin matansu ce ta kama habarta ta ce " to fa, uwar masu gidan ta dawo mun shiga uku da ranmu kowace ta yi ta kanta domin a kanta malan sai ya saki mace ko ya tsinewa d'a Nan fa suka shiga cicira maganar wanda hakan ke iske har inda su Hafsat suke , tana zaune mahaifiyarya sai kwararo adu.o.i take tana godewa Allah A wannan rana mahaifiyarta ta kai mata ruwan wanka masu dumin gaske, ta tsaya ta yi wanka sun dawo daki, ta bata man zafi ta shafe jikinta haka kuma ta saka abin gasa jiki ta ringa gasa mata gefen fuskarta, ta bata madara hade da maltina ta shanye sannan ta yi mata shinfida saman gadonta dakinta ta kwonta saman lalausan bargonta kafin ta rufa mata lalausan bargonta ta kuna mata panka Ajiyar zuciya ta ringa saukewa tana hangen mahaifiyarta ta tsura mata ido, bata tambayeta daga ina take ba har yanzu, du dai wani takunta tana biye da shi , sai dai abu daya da maman nata ta yi mata shi ne a lokacin da ta fito a wanka ta dawo daki ta umarceta da ta kwonta zata dubata, Bata wani damu da hakan ba, hasalima bata san me hakan ke nufi ba dan kuwa ta jima tana mata irin haka ko can baya, irin idan ta cika daren nan da safe sai ta duba ta, A lokacin da ta gama dubanta kuwa sai ta ga murmushi kan leben mahaifiyar nata, tabas mama ta yi farin cikin abinda ta gani hakan ya sakata kwonciya itama a lokacin da ta fahimci Hafsat ta yi baci itama ta kwontar da hakarkarinta A washe gari ba ita ta farka ba sai wajen karfe tara dan kuwa tsakiyar dare al.adarta ne ya tasheta ta kimtsa kanta ta koma Wanka ta fito ta yi cikin nutsuwa sanann ta koma dakin mahaifiyarta Har kasa ta duka tana gaishe da mamanta hakan ya sakata tsayawa tsai cike da mamaki tana kallonta, Kasa rike tambayarta ta yi, dan haka ta ce" *ANMIH, INA KIKA JE? ME YA SAME KI? ME AKAI MAKI?* HAFSAT ta dago da dubanta, ko a yanzun doguwar rigarta ce cikin kayanta na da ta saka, rigar bata matseta ba dan bata kara jiki ba saima daidaituwar halitarta da ta yi
Chapter 63 · 0% Book details