Sashe 52
Kutkale Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
gadonta dakinta ta kwonta saman lalausan bargonta kafin ta rufa mata lalausan bargonta ta kuna mata panka Ajiyar zuciya ta ringa saukewa tana hangen mahaifiyarta ta tsura mata ido, bata tambayeta daga ina take ba har yanzu, du dai wani takunta tana biye da shi , sai dai abu daya da maman nata ta yi mata shi ne a lokacin da ta fito a wanka ta dawo daki ta umarceta da ta kwonta zata dubata, Bata wani damu da hakan ba, hasalima bata san me hakan ke nufi ba dan kuwa ta jima tana mata irin haka ko can baya, irin idan ta cika daren nan da safe sai ta duba ta, A lokacin da ta gama dubanta kuwa sai ta ga murmushi kan leben mahaifiyar nata, tabas mama ta yi farin cikin abinda ta gani hakan ya sakata kwonciya itama a lokacin da ta fahimci Hafsat ta yi baci itama ta kwontar da hakarkarinta A washe gari ba ita ta farka ba sai wajen karfe tara dan kuwa tsakiyar dare al.adarta ne ya tasheta ta kimtsa kanta ta koma Wanka ta fito ta yi cikin nutsuwa sanann ta koma dakin mahaifiyarta Har kasa ta duka tana gaishe da mamanta hakan ya sakata tsayawa tsai cike da mamaki tana kallonta, Kasa rike tambayarta ta yi, dan haka ta ce" *ANMIH, INA KIKA JE? ME YA SAME KI? ME AKAI MAKI?* HAFSAT ta dago da dubanta, ko a yanzun doguwar rigarta ce cikin kayanta na da ta saka, rigar bata matseta ba dan bata kara jiki ba saima daidaituwar halitarta da ta yi sai dai rigar bayanta gaba daya a bude yake, ahigar sam batai mata dadi a ranta ba, Jiki a sanyaye, muryarma a sanyaye ta buda baki zata yi magana ta kasa, ta kara budawa zata yi sai kawai ta shiga inda indar da bata saba ba, haka kuma jikinta ya dauki rawa, muryarta ne take rawa sosai a lokaci daya ta ce" *MAMA* muryar mahaifinta da ya kasa hakurin jiran har su je gaishe shi ne ta katseta a lokacin da ya ce" *UWATA?* A tare suka juya , shi kuwa ya tako ya shiga cikin dakin a nitse, sai da ya kali Hafsat din sannan ya kalli mahaifiyarta , Da hannunsa ya yi mata nuni da ta zauna, Cikin nutsuwa ta zauna jikinta a sanyaye dan ta tsorata da abinda ya tsoratar da yarinyar nata har haka harma ta kasa magana, Sai da malan ya kara dakin sannan ya zauna cikin nutsuwa ya ce""" *KUTKALE* *(PRISON)* NA *SAJIDA* Marubuciyar DUK KARYAR KADA YAR MAHAUKACIYA DAGA TAFIA DAUKAR SOJA NEMAN NA KAINA BANI DA ZABI IDAN KA RAINA INDA KAKE BAK'A CE INA KUKE MASOYAN NOVELS DINA, GANI NA DAWO DA SABON SALO, SABUWAR TAFIA, NA ZO MAKU DA SABON NVL DINA MAI TAKE *KUTKALE* WATO GIDAN PRISON, WANNAN NVL ZAI ZO MAKU DA LAMURA DA YAWA, KU BIYO NI KU SHA LABARI........ *WANNAN NOVEL NA SIYARWA NE, DU MAI SO ZAI IYA TURA KUDINSA TA wannan acct NAIRA DARI BIYU : Usman Muhammad 3072998062 First bank. Sai ya turo shaidar ya biya ta wannan number +22791466605....sannan a yi adding dinsa cikin grup, MUTANENA NA NIGER KUWA SANADIYAR RASHIN SAMUN ORANGE MONEY DA KUKE YI, KUNA IYA TURO HOTON KATIN SAHELCOM KO NA AIRTEL TA NUMBER KAMAR HAKA 91466605 SAI A SAKA KU A GRUP DIN, .....* taku ce, Sajida 4 A hankali malan ya koma ya zauna , Sai da ya sauke ajiyar zuciya sannan ya ce" da baka yi magana irin haka ba, da na bar wajenka cike da tsoro da tunani dan kuwa idan ba mahaukaci ba sai mai kishirwar ramuwa zai hadiye irin wannan lamari lokaci daya Abdallah , imani da Allah da yarda cewa a cikin mutane akoy masu cuta akoy masu tsoron Allah, Imani, hakuri ne kawai zasu saka ka yarda da wani mahalukin a nan duniya Zan so ka kasance mai hakuri ka cinye jarabawar nan Abdallah Kansa ya sada yana mai jin yanda zuciyarsa take cinkushe bata da wani yannayi na wanda zai iya samun nutsuwa, Kansa ya kuma dagowa ya kalli malan ya ce" da idona, da kunnena na jiyo shawarar aminan mahaifina na zasu hada ni da bin mata, duda bata fadi komai ba idannuwanta sun karantar min komai Zan so a ce ba daga bakinta haka ya fito ba ko na samu damar musawa har na fuskanci dan uwana Malan ya kara matsa kujerarsa kusa da gadon yana kallonsa ya ce" ka rage zurfafa kauna , haka kuma ka rage zurfafa kiyaya Tsananin kaunar da kake masa da yardar da ka bashi dari bisa dari ne ya rufe maka ido ka kasa gannin ainahin wanene shi, sannan wacece ta fada maka? Kar ka yarda ka hau kan abu ba da kwakwaran shaida ba Idannuwansa ya dago yana kallon Malan, Sai da gabansa ya yanke ya fadi, a lokaci daya kuma irin yannayin da ya tarda ta ya fado a idannuwansa, Shikenan, ta dalilinsa rayuwarta ta bace ko me? Anfani ya ringa yi da ita? Shi kam me ya yiwa Muhammadu a duniyar nan? Me ya yi masa da zafi haka? Da sauri ya kali malan, tausayin malan da na Hafsat ne ya ji sun mamaye zuciyarsa, ta jure gwagwarmayar rayuwar nan, ta shiga Kutkale ta fito lafia, ta shiga gidan horon maza ta fito lafia, du bata rasa mutuncinta ba sai a dalilin bashi tsaro? Bashi tsaroma ya dace ya mayar da ita tun harbin da akai mata aman ya kasa hakan ya riketa a wajensa gashi ya jaza mata wannan balaki? Muryar malan ce ta dawo da shi daga dogon tunanin da ya saka shi mayar da ido ya rintse dan jin wani irin kyankyamin Aminin nasa, Bai taba jin kyankyamin zina, kallon matan wasu ba irin na yau....sai a wannan lokacin ya ringa hasko dubunnan matan da ya ganni tsirara dan kawai ya samu biyan bukatarsa, Sai a lokacin ya yi tunanin wa.innan mutanen fa y'ayan wasu ne, iyayen wasu ne, yayun wasu ne, kuma kannun wasu ne, duda su suka kawo masa kansu aman shi dan rashin tsoron Allah da rashin kunya ya mike ya mika masu abinda ya fi sirri a jikinsa suka lumda suka bashi nutsuwa ta hanyoyi daban daban....sai gashi shi ya ki ya haihu dan kar a yiwa abinda ya haifan aman cikin ikon Allah, Allah ya saka masa muguwar shakuwa da yarinyar da basu hada komai ba, shekarunsu ba daya ba , fatarsu ba daya ba, shakuwa irin ta yan uwantaka wace yake jinta har cikin jinninsa, yake yi mata so daya da ba hadi... an yi mata abinda yake gudun a yiwa yayan nasa? Dama ba.a isa a zagaye ikon Allah ko a yiwa Allah dabara ba ko? Dama lokaci Allah ya ara masa na ya gama zagaye zagayensa kafin ya rike shi? Kai, ya san ba zai iya ja da amininsa kan maganar kisan kan da ya ringa yi....wannan Allah zai saka masa! Cin amanar aminta da ya yi ..shima ba zai wani hukunta shi ba, Aman baya jin zuciyarsa zata iya amince masa ya hadu da mutumen da ya tsaga jikin Hafsansa ba tare da igiyar aure ba dan kawai cin mutunci da wulakanci ba tare da ya gile shegiyar da ta kai shi aikata hakan ba, tabas sai ya yi masa kaciya da faratunansa zai tsinke abinda ya kasa rikewa a wandonsa sai da ya ketawa Hafsat hadi! Shiru Malan ya yi gannin wasu guntayen hawaye na biyowa gefen fuskarsa , carbinsa ya ci gaba da ja yana mai dubansa a kasan zuciyarsa kuwa yana nema masa sauki a wajen ubangiji A haka BS ya shiga dakin ya ja ya tsaya, Ya jima a yannayin da yake na sarawa Abdul na kallonsa kafin ya iya daga masa hannu ya sauke hannunsa Yana saukewa a hankali ya ce" takarda ce daga saudiya, suna bukatar a mika masu mai laifi dan an karanta masu komai an kuma tura masu dukan hujoji ta hanyar computer shine suka turo da sakon a mika masu shi can Kafarsa dake ajiye yana karkadawa a hankali ya ce" idan aka basu shi me zasu iya yi masa? BS ya yi shiru domin ya tabata tambayar ba ta neman amsa bace Abdul ya dago jajayen idannuwansa ya ce" zasu saka masq fararan tufafi ne, su dauko shi su shigo tsakiyar gari da shi, su saka masa bakin yadi su rufe masa fuskarsa su dauki doguwar takarda su karanto laifinsa sannan su saka doguwar wuka sun gile kansa..... Sai da ya tsaida idannuwansa cikin na BS ya ce" an bashi mutuwa mai sauki, bai ga duniya ba an tafi da shi lahira..... Malan dake kallonsa sai da ya ji dar din Abdul din, dan kuwa gaba dayansa ya mike zaune ya kara kallonsa da kyau ya ce" ka bani wayoyina Da sauri ya juya ya yafito su Hafsat dake tsatsaye Suna shigowa ya karbi wayoyin Abdul din dake hannun su Hafsat ya mika masa su kuwa du suka juya suka layu daga kan Bs Har su Hafsat din kusan garu inda malan ya bi Hafsat da kallo dan kuwa yanzu ba hijab din a jikinta cikin damararta na aiki da ta saba Abdul kam mikewa ya yi tsaye kan kafafuwansa da kayan asibiti a jikinsa ya danna kira, Ana dagawa ya canza harshe ya shiga magana cikin yannayin zafi zafi , yana yaran larabawa wanda Hafsat da Malan suna fahimtar duka kaf abinda yake fada Cikin yannayin tsoronsa ta kafe shi da dara daran idannuwanta, dan kuwa ya fito sak a baban mutun ma.aikaci mai zaman kansa mai iko da kansa wanda ya san hakokinsa da wa.inda ba.a isa a take masa ba Maganar da ya karasa da uta shi ne" *in dai ba za.a sake shi a saki amininsa a fili a basu damar kashe kansu ba, to fa ba.a isa a tura shi saudiya ba, a barshi a Minna su yanke masa hukunci....a kai shi Niger a saka shi a cikin gidan kason KUTKALE* Yana gama fada ya ajiye wayar ya daga manyan damatsunansa ya cusa hannayen nasa a cikin gashin kansa Ya jima a haka ba wanda ya ce komai a cikinsu har ya yi niya da kansa kuma ya juyo