Sashe 43
Kutkale Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
irin shake gashin kanta dake baje ne ya yi, hakan ya sakata buda idannuwanta ba shiri sai kuma ta mayar ta rintse, Walahi da za.a tona zuciyarta da an ga rubutacen abu cewa taba fatar jikinta da ya yi a yanzu ya fi mata ciwo fiye da azabar dukan da yake gana mata, Murya na shake mata ta ce" Ta yaya zaka yi tunanin muna soyaya da shi bayan ba wani abu makamancin haka da ya taba hada ni da shi? Kara matsa fuskarsa kusa da tata ya yi sosai sannan ya ce" irin alwashin da ya ci a kan du wanda ya dauke ki na shi ne ajalinsa da hannunsa kadai ya isa ya shaida cewa kina zuciyarsa, A kan ya ci alwashin kake son halakani? Yana shirin bata amsa wayarsa ta dauki ruri, Da sauri ya rarumo abin rufe bakin ya rufe bakinta sannan ya saita kansa ya daga wayar Yana dagawa ya ce" Abdul, ina ka je kuma? Ina ka je? Kana ina ne? Shin yaushe zaka daina tayar min da hankali idan kana fita? Yaushe zaka san ciwon abubuwan dake faruwa ka daina fitar nan da kake har sai wani abu ya same ka? Sai da na tashi na neme ka ban same ka ba shin yaya kake so hankalina ya kwonta? Abdul ya yi murmushi ya ce" Muhammad, gani fa na dawo kai ne nake nema ban gani ba, ka yi hakuri nima kana raina, na je wani uzuri ne Muhammad ya yi gagawar kashe wayar ya koma wajen Hafsat dake binsa da kallo , da yatsarsa ya yi mata nuni da zasu sake haduwa ne, sannan ya juya da sauri ya fice ya bar mata dakin, wanda yana fita mai tsaron nata ya dawo ya rufe mata idon ya ci gaba da gadinta A lokacin da Muhammad ya koma ya tarar da Abdul zaune a falonsa, Sai da ya kimtsa yannayinsa sannan ya karasa wajen Abdul fuskarsa na nuna tsantsar damuwar halin da yake ciki, Yana zama ya kura masa ido kafin ya ce" yaushe zaka cire damuwar yarinyar nan a ranka ne? Kana abu cikin yannayin da kai kanka baka sani ba, nace da kai kaunarta kake ka kamu da son macen dake baka tsaro, wace aka bata horo irin na gardawa aman ka musa min? Abdul ya girgiza kansa ya mika masa hannu ya ce" kai kuwa yaushe zaka daina dirowa wajen mutun ka rufe shi da fada da accusation ne? Asalamu alaika Muhammad ya mika masa hannun da ya shaki gashin kan Hafsat sukai musabaha kafin su ci gaba da tataunawa suna musun da suka saba a haka har ya mike ya ce da shi zai je ya watsa ruwa Da ido Muhammad ya raka shi har ya shige kafin ya bi masu bashi tsaro sai shawagi suke a wajen, Murmushi ya yi kasa kasa sannan ya mike shima ya nufi dakinsa A lokacin da Abdul ya shiga dakinsa tubewa ya yi ya dauki tawul ya nufi bayi da niyar yin wanka Tsayuwa ya yi kasan shower rufa na sauka jikinsa ba tare da ya goga sabulu a jikin nasa ba, A hankali ya kawo hannun da sukai musabaha da Muhammad da shi ya saka wajen fuskarsa yana share ruwan dake rubar masa a fuskar Tsai ya yi da hannun, inda gabansa ya wani irin bugawa, A hankali ya maida hannun wajen hancinsa da kyau dan kara shakar kanshin turaran gashin matan da ya shaka wanda ya tabata da turaran gashin mata ne dan kuwa a da mamansa ke anfani da shi sai kuma da ya ji shi wajen Hafsat dan kuwa irin yanda ake zama na matsewa junna waje dole a ji iskar kamshi ko warin da jikin mutun ke iya fitarwa, dan shinema ya saka GN basu kulawa dan kiyaye fitar da warin jiki Tsai ya kurawa pampon ido kafin ya mika hannunsa ya dauko sabulu ya shiga gogawa, Wankan ya yi ya gama ya dauro tawul ya fito ya tsaya gaban gadonsa yana kallo, A fili ya furta" aa, Ni.ima da na shiga dakinta bata kanshinnan, hasalima ban taba jin kanta na kanshi ba sai dai abin ruwa ko kanshi kanshin man gashi hade da warin ruwa, Tawul din ya yar ya mika hannunsa ya dauko jalabiyarsa zai saka ya kuma juyowa ya ce" aman, malan kawai na yi musabaha da shi a fitan da na yi, me zai hada hannun malan da kanshin turaran ruwa na gashin mata? Yarfe hannunsa ya yi kafin ya kara kai hannun wajen hancinsa ya sinsina, wankan da ya yi da sabulu ya saka babu kanshin, Dan tsaki ya ja ya shinfida salaya ya tsaftace tunaninsa ya gabatar da sallah Yana gamawa ya shiga jan carbi yana mai kallon waje daya, ya jima yana adu.a kafin ya shafa ya mike ya cire rigar daga shi sai wandon cikin ya kwonta saman bed dinsa Shiru ya yi yana mai jin tunanin turaran nan na dawo masa, Mikewa ya yi ya zauna, a ransa yake ayanna bayan malan sai Muhammad da muka yi musabaha da shi, Muhammad? Ya Salam, me ya hada Muhammad da turaran gashin mace wanda hakan na nunin ya taba gashin ne? Shin Muhammad ya saka kansa a harkar bin mata ko meye? Saurin rintse idannuwansa ya yi, dan ba zai yarda yana ji yana gani ya kyale Muhammad ya saka kansa a muguwa kuma lalataciyar rayuwa irin ta bin mata ba, rayuwar da idan kana yi baka da mutunci a idannun al.uma? Ita kanta abokiyar watsewar naka ba mutuncinka take gani ba, a wajen Allah baka da rabo, haka a duniyar du abinda ka taba sai dai ya ringa yin baya? Ina ba zai bari amininsa ya saka kansa a wulakantaciyar rayuwa irin wannan ba Waje ya samu ya kwonta aman fir baci ya ki zo masa, haka ya yi ta juyi yana tunane tunane ga tarin gajiya, karshe dai ya mike ya kara dangana kansa da darduma dan kara fadawa Allah ya kare mutuniyarsa a samu yar mutane lafia ya shige gaba kan matsalarta na kaso a wanketa tsaf ya mayar da ita wajen iyayenta lafia idan ya so ya daga ya yi tafiarsa shima saudiya tare da amininsa! A lokacin da ya gama shafa fatiya wayarsa message ya shigo, Hannunsa ya saka ya shiga message din dan kuwa yanzu baya sake da du wani abinda zai shigo masa dan gudun ya taka kaya ya bar abinda zai kai shi ga Hafsat Yana dubawa message ne kamar haka" *Ba.a gane mahinmancin abu sai yana nesa da kai, yanda kake ji, haka nake ji ba dare ba rana tun daga bakin lokacin da na shiga jirgi da niyar yiwa yarona daya kwal da matata karyar na mutu, Abdallah damuwa ta hana ka baci ne? Rabona da baci tun lokacin da aka kashe min yarinya,.........BA NI BANE* Tsaki ya ja ya jefa wayar saman bed dinsa ya mike ya fice a dakin a lokacin karfe hudu ne na dare dan kuwa ko kiran sallar farko ba.a yi ba Ky din wajen sa ya saka ya buda dakin ya shiga, yana shiga ya zarce inda yake kwonce ya saka hannunsa ya dada masa wani duka mai karfi wanda ya saka shi mikewa tsaye a firgice yana kallon Abdul Abdul ya kura masa ido kafin ya nuna shi da yatsa ya ce" kai, wace irin rayuwa kake son shiga? Daga ina kake dazu? Ina ka hadu da ita? Ina ka kai ta? Wani irin faduwar gaba da ta ziyarci zuciyar Muhammad, lokaci guda kafafuwansa suka kwashi rawa , wata irin zufa ta shiga zubo masa a fuskarsa, Da sauri ya kalli bayan Abdul ya ga shi daya ya shigo a wannan lokacin, gaba dayansa a hargitse, yannayin Abdul ya mugun tsorata shi dan kuwa a lokaci daya abinda ya fado masa a rai shi ne asirinsa ya tonu, lokaci daya ya fara jin wani abu na bi masa kafa kamar wanda fitsari ya kufce masa fan ya sani, ya fi uban kowa sani in dai har asirinsa ya tonu ne walahi sai dai a banbare gawarsa ko yace abinda ya yi saura a gangar jikinsa daga hannunsa, Hannayensa ya hade yana son yin magana, lokaci daya kuma yake son amayar wa da abdul cewa eh shi ya yi, shima dan ya raba shi da budurwarsa (Allah kennan, wato shi mugun abu , ita mugunta idan kana aikata ta du dadin da kake ji bai kai fargabarka da tashin hankalinka ba, dan kuwa kai kulun jininka a akaifa yake, baka da nutsuwa a komai! Cin amana? Du mai yi bashi da nutsuwar zuciya, haka kuma ka mace ka je ka tarar da Allah) Kafin ya yi magana Abdul ya sasauta muryarsa ya ce " Haba, Haba , Haba Muhammad, me ya yi zafi da zaka saka rayuwarka a kazamar rayuwa irin wannan , kar ka manta fa, kai ke min fada kan rayuwar zina, kar ka manta tashin hankalinka ka ganni ina rabawa mata ruwan jikina, ka fi kowa sannin ba shigar mace nake ba aman a wancen din ma adu.arka Allah ya shirye ni, sai yanzu da na shiryu na canza na daina kai zaka afka? A inama ka ga yarinyar da har ka yi kusancin da ya hada hannunka da gashin kanta? Wata wawuyar ajiyar Zuciya Muhammad ya sauke yana mai matse kafafuwansa tare da neman zama saman bed din dan kar Abdul ya fahinci abinda ya aikata a jikinsa, Sai da ya zauna sosai sannan ya saka hannun nasa cikin gashin kansa yana shafawa a hankali kafin a ransa ya ayanna' tabas zan yi gagawar kawar da ke a doron kasa kafin sanadiyarki asirina ya tonu, idan na mutu a yanzu yanzu ban ga anfanin rayukan da na yi ta dauka ba, dan kuwa du irin mutuwar da akai masa kala daban daban bai saka shi ya rasa imaninsa ba, haka kuma bai zauce ba! Burina na ga Abdul na sakin magangannun haukacewa, kafin na kai shi gidan mahaukata a ringa tsira masa alurar mahaukata mai karfi tana cinsa a hankali tana azabtar da shi har lumfashinsa ya bar gangar jikinsa, daga nan na tabata na ci galaba a kansa! Abdul ma ya zauna irin zaman fa ya yi ya ce"