← Book details Kutkale Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 79 OF 94

Sashe 79

Kutkale Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

ya raya shi idonsa biyu, ya raya shi yana begen fulawar dake gabansa kwonce, ya raya shi yana mai neman mafitar yanda zai yi da ita ta sha maganin da yake baiwa yar uwarta, yana son haihuwa fa, yana son samun yaya, da zai samu maza ......sai dai ya san ayya sai ta tabata a kansa, irin yanda ya yi wasa da yayan mutane yana tsoron hakan ta kasance a kansa! Sai bayan ya gama sallah ya tasheta, A hankali ta iya mikewa ta sauko daga saman bed din nasa Kanta na kallon kasa ta samu ta yayumi abin rufar tasa ta nemi hanyar ficewa dan zuwa dakinta Da sauri ya rike hannunta yana kallonta ya ce" ki zauna a nan Kauriyata plz Hafsat ta kale shi da kyau sannan ta ce" nan bangarenka ne Abdul, wanda ba ni daya nake da kai ba, matarka na iya shiga du lokacin da muradin hakan ya taso mata, inma tambayeka na taba kwana a nan ne? Ni dakina zan je Murmushi ya yi yana kallon bakin tsiwar nata, ita dai bata sasautawa kennan dai, du irin halin nan da take ciki na wahalar da ta sha a jiya da dare bai hanata buda dan bakinta ta dan juya shi ba Murmushi kawai ya yi sannan ya bita da kallo har ta fice a dakin Wani murmushin ya yi a ransa yana godewa Allah da ni.ima da ya yi masa, du irin abubuwan da ya ringa aikatawa sai Allah ua bashi matayen auren dake rufe ruf abinsa, shi dai haihuwa ne kawai ba zai yi na, ya hakura da haihuwa. Hafsat na komawa dakinta wayarta ta dauka ta yi kiran number auntynta Kuka ta fashe mata da shi kafin ta ce" aunty ciwo nake ji Shiru aunty ta yi, ta dan jima sannan ta ce" Hafsat, kina ina ne? Mijin ki ya zo ne?? Hafsat ta turo bakinta ta ce" eh ya zo, yama jima da dawowa ai, aunty ni ki zo dan Allah ba zan iya tafia ba, ki zo ki kaini wajen Malan! Aunty ta sauke ajiyar zuciya tana mamakin yaya aka yi Hafsat ke barambarama haka? Koda yake ba sai ta yi kawayen da zasu koya mata yanda zata yi ba sannan zata gane me yaren ke nufi Cikin hikima aunty ta kwatantawa Hafsat cewa hakan ba wani abu bane zai fice, sannan ta koya mata yanda zata kula da kanta Sai da ta kwadaita mata ladan hakan sosai sannan sukai salama Yanda Aunty ta koyar da ita haka ta yi, ta tatare zannin gadon ta kai mashine din wanki, Sallah ta gabatar a hankali ta samu ta yi shinfida sannan ta haye gadonta ta nade Can wajen karfe biyu na rana ya shigo dakin, kwonce take tana ta bacinta hankali kwonce Abincin da ya shigo da shi ya ajiye sannan ya karasa kusa da ita A hankali yake shafar gefen fuskarta har ta buda idannuwanta Murmushi ya sakar mata yana kallonta Mikewa Hafsat ta yi daga kwoncen tana kallon agogo Idannuwanta ta zaro tana kallon agogo Bata yi magana ba ta sauka daga saman gadon ta je ta yi brushing Tana fitowa ta karasa inda yake zaune Hannunsa ya mika ya janyoya jikinsa yana kallonta, yanda take sasada kanta abin na matukar birgeshi, ita kam komqi ta yi na jan ra.ayinsa sosai Abincin da ya shigo mata da shi ne ya miko mata , Zaunar da ita ya yi ya shiga kokarin ciyar da ita Sai da ta kusan rabi ta ji cikinta ya dan daure Dafe cikin ta yi kadan, sai kuma ta ji ya saki Ajiyar zuciya ta sauke sannan ta kai dubanta wajensa Gani ta yi madaukakiyar damuwa a tare da fuskarsa, gannin ta saki cikin nata har sai da ya sauke ajiyar zuciya Bata nuna komai ba sai ci da ta yi cikin nutsuwa har ta gama Tana gamawa ya fice da abincin, Sai da ya ajiye abincin a kicin ya jinginar da bayansa, ajiyar zuciya ya ringa saukewa domin irin rike cikin da ta yi gabansa ba karamin faduwa ya yi ba, me hakan ke nufi? Tsoro ya ji kar a je maganin da ya zuba mata a abincin dan dabara ya saka mata rikewar cikin Watsar da abin ya yi ya nemi walwalarsa, karshema fita ya yi ya tafi gidan malan cike da nishadi A kwanaki bakwai da Abdul ya yiwa Hafsat sun matukar shakuwa Shakuwa fiye da ta da, domin kwana daya rak ya saka mata ta huta kafin ya shiga horar da halitarta irin tasa A hankali ta ringa koyon al.amuransa, bata da sanya a abinda ya shafe shi, tana kafa kafa da komai nasa, sai dai abinda ke damunta mararta na yawan yi mata ciwo bayan ba al.adarta ke kusantota ba, sam al.adarta na nesa dan bata ana jibi kawota gidanta ta gama Bayan wata mu.alar aure da suka yi, Abdul ya kawo mata jus Hafsat na sha ba.a dauki lokaci mai tsayi ba cikinta ya kule Wata irin zabura ta yi jin mararta na kara rikice mata, Da sauri ta nemi sauka a gadon gannin abin na kara hawar mata Abdul da fitowarsa kennan daga bayi ya tarar da ita tsugune wajen bed din tana mitsitsiya Da sauri ya ajiye kum din hannunsa ya nufeta gabansa na wani irin mugun faduwa..........yana zuwa ya........ Ku gane, situation din rayuwa na saka mutun da yawa zama wasu iri, zaka ga mutun na rayuwa irin ta bayahude, wanin na canzawa, wani kuwa haka yake tafia har ya tsufa ya koma ga mahalicinsa Abdul na gudun haihuwa ne dan baya so ya sami mace ya wayi gari ya riski wani ya wulakanta masa ita, Bai san cewa Allah mai gafartawa bayinsa ne, sannan idan ayyar ce zata kqsance a kansa bai isa ya hana ba, ba.aiwa Allah wayo Dan haka zan so ku fahimci labarina....ku gane me ya kunsa.....godiya nake *KUTKALE* *(PRISON)* NA *SAJIDA* Marubuciyar DUK KARYAR KADA YAR MAHAUKACIYA DAGA TAFIA DAUKAR SOJA NEMAN NA KAINA BANI DA ZABI IDAN KA RAINA INDA KAKE BAK'A CE INA KUKE MASOYAN NOVELS DINA, GANI NA DAWO DA SABON SALO, SABUWAR TAFIA, NA ZO MAKU DA SABON NVL DINA MAI TAKE *KUTKALE* WATO GIDAN PRISON, WANNAN NVL ZAI ZO MAKU DA LAMURA DA YAWA, KU BIYO NI KU SHA LABARI........ *WANNAN NOVEL NA SIYARWA NE, DU MAI SO ZAI IYA TURA KUDINSA TA wannan acct NAIRA DARI BIYU : Usman Muhammad 3072998062 First bank. Sai ya turo shaidar ya biya ta wannan number +22791466605....sannan a yi adding dinsa cikin grup, MUTANENA NA NIGER KUWA SANADIYAR RASHIN SAMUN ORANGE MONEY DA KUKE YI, KUNA IYA TURO HOTON KATIN SAHELCOM KO NA AIRTEL TA NUMBER KAMAR HAKA 91466605 SAI A SAKA KU A GRUP DIN, .....* taku ce, Sajida 6 Da sauri Abdul ya nufeta, irin yanda take damkar cikinta sai da gabansa ya yanke ya fadi Da sauri ya cicibata ya dagata ya dorata saman bed din dakin Du ya bi ya rude, danna inda take rikewar kawai yake hankalinsa tashe Hafsat dake neman ficewa a hayacinta ta yi saurin damke hannunsa, muryarta na wani irin rawa ta ce" Abdul zan mutu Da sauri ya mike tsaye ba tare da ya yi wata wata ba ya wawureta daga saman bed din Sai da ya nufi hanyar bayi da ita sai kuma ya juyo da wani irin sauri sauri gudu gudu ya nufi kofar fita da ita, daidai lokacin tuni Hafsat ta sume, ta fita a hayacinta Gaba daya Abdul ya rikice, yana zuwa motar da ya bude ya sakata a nan ya lura da ta sume, Innalilahi wa.ina ilaihi raj.une...shi ne abinda ya fada da dan karfi yana kallon fuskarta da ta yi fayau da ita, Bai wani lura da bai dauko mata hijab ba, haka kuma bai lura da rigar jikin nata doguwar riga ce mai siririn hannu rigar da ta bi ta fitar mata da surar jikinta sosai Wata irin rufewa ya yi ya zagaya ya shiga mazaunin direva ya tayar da motar Tuki yake na garari, yana yi yana take dokokin tukin, A haka har ya karasa clinik Yana zuwa ya fita a sitin ya kuma daukanta ya nufi cikin dakin likitocin Tarbansa nourse din ta yi da sauri aka gurguro gadon mararsa lafia aka dorata Da sauri wata daga cikin nurse din ta danna number docter dan fada masa an kawo urgence Wani irin zama abdul ya yi kan kujerar dake wajen, Idannuwansa ya rintse da sauri sakamakon wani irin dokawa da zuciyarsa ke yi, Walahi rabonsa da ya ji irin haka tun lokacin da ya ga gawar kanwarsa, ya ga ta mahaifiyarsa, sai wanda ya ji a lokacin da ya gane amininsa ne bakin kumurcin da ya hana shi zaman lafiya Yana nan zaune mutumen da yake docter ya zo ya shige dakin Nurse din ce ta zo wajensa ta ce" asalamu alaikum Da sauri ya dago ya sauke dubansa a kanta Dan gyara tsayuwarta ta yi ta ce" docter ne ya ce a tambayo, shin wani abu ta ci? Sannan tana da ciki? Ta saba irin haka? Tamkar wanda ke karantar bakinta dan tsai kawai ya yi yana dubanta, Sai da ta ce" Malan are u ok? Da sauri ya kawar da dubansa daga kanta, fuskarsa a yannayin hadewa ya ce" ban sani ba Kara dubansa ta yi daga sama har kasa, yannayin shigarsa ya sakata yin gum da bakinta ta juya da sauri Tana shiga ta tarar ta farfado aman sai birkidadoniya take ana tareta Likitan ya gama sauraron abinda aka ce, Da yake mai hakuri ne sai ya matsa kusa da Hafsat din ya shiga yi mata tambaya a hankali Kanta kawai take juyawa idan eh ne ko aa ne Kina da aure? Hafsat ta gyada masa kanta Yaushe rabon ki da al.ada? Hafsar ta nuna masa hannunta wato yatsarta biyu Tambayarta ya kuma yi kwana? Ta girgiza kai, Sati? Ta gyada masa kai Shin kin ci wani abin da baki saba ci ba?? Hafsat ta juya masa kai Ya ce" dama kina irin haka?? Hafsar ta kuma juya masa kai alamar aa Wajen da ta fi rikewa ya kurawa ido, A hankali ya ce" kin sha wani magani ne??? Hafsat ta girgiza kanta tana ta mikewa tamkar
Chapter 79 · 0% Book details