Sashe 44
Kutkale Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
mazinaci, mazinaci, bashi da wata daraja da ta rage masa a duniya, karshensa ya mutu babu ido, ba abin hannu, ba iyalin da zasu talafe shi, ba mutunci a idannun kowa, dan kuwa yaro karamima zai taka shi ya fice idan bai tuba ba wa Allah ba.......wannan shi ne nasiharka gare ni Muhammad ya gala masa harara ya ce" yanzu saboda wannan abin ne ka biyo bayana kai jarababe da tsakiyar daren nan Abdul kake kokarin sakawa jinina ya hau? Ni ba tsoro na ji ba kar a je mugayen anamiman masu biyar bayan naka ne suka kuma kawo mana farmaki da tsakar dare haka? Gaba daya ka saka na firgice na fita a hayacina bayan ni na sayi abin gashin dan ya birge ni? Sai a lokacin Abdul ya yi tsai yana mai karewa yannayinsa kallo, Dariya ce ke son kubuce masa dan kuwa walahi ya bashi dariya du ya yi tsuru tsuru da shi, Hannunsa ya matso kusan sa ya ce" Muhammad, wai tsoron mutuwa kake? Muhammad ya tsura masa ido bai bashi amsa ba, ya nuna yannayin irin ya kufilan nan Abdul ya yi murmushi ya dan daki kafadarsa ya ce" to dan me ba zaka juya saudiya abinka ba Muhammad? Ka koma gida ka huta zan biyo bayanka in sha Allah Muhammad ya sauke hannun Abdul a kafadarsa ya ce" kana tunanin zan iya barinka kai daya tsakanin masu harin rayuwarka? Rana tsaka fa wata aljanar yarinya ta zo wai yayarka ce, kai kuwa ka bata wajen zama , idan fa ita ke harin rayuwarka? Abdul bana samun isashen baci dan yawan tunani, a ina tare da kai idan na koma yaya kake so na samu nutsuwa? Abdul ya koma ya zauna a hankali yana kallon sa ya ce" *MUHAMMAD, MAKASHIN MAZA AI MAZA KE KASHE SHI* Na yi imanin ko irin yanda mai bibiyar rayuwana ke hana aminina sukuni Allah ba zai barshi ba, Muhammad, hakurin da nake yi, ahi zan ci gaba da yi, na tabata Adu.a bata faduwa kas, Ban san tsayin lokacin da zan kara dauka ina cikin wannan rayuwar ba, aman na san lokacin da Allah ya diban mata zai zo zata kare, Muhammad....mai bibiyar rayuwana na kusa da ni, tunda Allah ya saka hijabi tsakanina da shi na kasa gane shi du irin yanda na kware a harkar bincike, nasa ya zame min a cikin duhu ..... to kawai na barama Allahn, na tabata ya bashi dama ne ya gama rawarsa kafin ya daga shi sama ya kuma dada shi da kasa, *MUHAMMAD, IN SHA ALLAH, ALLAH SAI YA SAKA MIN KAFIN YA BAYANA SHI KOMA WANENE* Muhammad dake binsa da wani irin kallon da ba zan iya gane ko na meye ba, cikin wata irin murya mai rawa rawa ya ce"...... *KUTKALE* *(PRISON)* NA *SAJIDA* Marubuciyar DUK KARYAR KADA YAR MAHAUKACIYA DAGA TAFIA DAUKAR SOJA NEMAN NA KAINA BANI DA ZABI IDAN KA RAINA INDA KAKE BAK'A CE INA KUKE MASOYAN NOVELS DINA, GANI NA DAWO DA SABON SALO, SABUWAR TAFIA, NA ZO MAKU DA SABON NVL DINA MAI TAKE *KUTKALE* WATO GIDAN PRISON, WANNAN NVL ZAI ZO MAKU DA LAMURA DA YAWA, KU BIYO NI KU SHA LABARI........ *WANNAN NOVEL NA SIYARWA NE, DU MAI SO ZAI IYA TURA KUDINSA TA wannan acct NAIRA DARI BIYU : Usman Muhammad 3072998062 First bank. Sai ya turo shaidar ya biya ta wannan number +22791466605....sannan a yi adding dinsa cikin grup, MUTANENA NA NIGER KUWA SANADIYAR RASHIN SAMUN ORANGE MONEY DA KUKE YI, KUNA IYA TURO HOTON KATIN SAHELCOM KO NA AIRTEL TA NUMBER KAMAR HAKA 91466605 SAI A SAKA KU A GRUP DIN, .....* taku ce, Sajida 2 Cikin nutsuwa malan ya yi gyaran murya ya shiga labartawa mama duka kaf abubuwan da Abdul ya fada masa, da kuma gannin idonsa da ya yi, harma ya tina mata lokacin da ya zo ya fada mata a yau mamansa ta ziyarce shi, mamansa na raye dan kuwa a masalaci ya ji a jikinsa ita din ce Idannuwanta cike da hawaye ta kai dubanta wajen da Hafsat ke zaune a saman cafet ta sada kanta sai zubar da hawaye take, A hankali ta ce" Allah ya kara shiryar da ke, ya maki albarka, ya baki miji na gari Hafsat ta dago kanta da sauri ta saka idannuwanta cikin na mahaifiyarta, gaba daya maman nata ta yi wani irin sanyi bata zaci zata zama haka ba, tana shashekar kuka ta ce" mama, uncle din Abdul aziz ne, shi ne ya kai ni gidan kason gagan yan daba dan kawai na mari matarsa, mama ba zan taba yafe masa ba, ya wulakanta ni, ya tozarta ni, ya kai ni gidan halaka wanda Allah kawai ya fitar da ni Mama ce ta gala mata harara ta ce" ko komawa zaki yi ki kara daukan fansa? *UNMIH* ba zan so ki koma irin rayuwarki ta da can baya ba, kin ga taurin kai, jayaya, masifa, raina maganar manya sun bada gudunmuwa wajen saka ki a wannan jarabawa, shiga gidan kaso na abin kunya bane dan kuwa kadarar bawa ne baka isa ka kauce masa ba, sai dai abin lura me kika koyo a can? Yaya kike son tafiar da rayuwarki a yanzu? Mace kike, rayuwarki kadan ce, kar ki yi tsamanin kyan nan naki zai yi ta karuwa ne, daidai da gashin kankin nan zai ringa ja baya a hankali a hankali ne har ya dawo kadan, fatar jikinki zata janye, idannuwanki zasu jeme, furfura zata yi maki salama idan har kin dace! Ki rufa bakin ki, babu rufin asirin da ya kai na kariyar da Allah ya baki, Allah ya baki kariya Unmih ke kin sani...nima na sani...nan gaba kowa zai sani, kar ki yi garajen da Allah zai barki ya ga yanda zaki yin! Tashi malama ki fice min a daki ga kys din dakinki an gyara , je ki zan neme ki! Jiki a sabule ta mike ta karbi kys din dakin a hankali ta shiga takawa tana kuma waiwayen malan aman ga mamakinta bai daka tsawar kar a yi mata fada ba, saima kawar da kai da ya yi tamkar baya wajen Bakinta ta zumburo ta daga kafa ta fice a dakin tana fadin lale malan ya daina son ta Tana fita malan ya kurawa mama ido yana kallonta, Kanta ta sada kafin take kamo dan yatsarta ta shiga dan ja, Malan ya ce" to a huce a kaina mana da za.a saka min uwa gaba daga dawowarta a fara yi mata ihu ana fitar mata da ido? Ni madame me ya sa karfinki kike nuna shi a kan UWATA NE? murmushi ta saki a hankali, ta dago da idannuwanta da sukai jajajir, Sai da ta sauke ajiyar zuciya sai kuma ta fashe masa da kuka marar sauti Murmushi malan ya yi yana kallonta ya ce" menene na kukan kuma? Sai da mama ta yi dan kukanta wanda tamkar na shagwaba kafin ta sasauta tana kallonsa ta ce" tsoro nake ji, du wannan rayuwar da Anmih ta gani bai saka ta daina fada ba, ji fa ita nan har tana gannin ramuwar da zata yi ta huce? Ramuwa ta fi ta barwa Allah ya saka mata? Sai da ya lakaci hancinta yana kallonta ya ce" shekarun ki arba.in da bakwai da wata hudu da kuma kwana ashirin da biyar yau maman Uwata, aman har yanzu akoy rigima......... Ki kwontar da hankalin ki, adu.ar nan dai da muke yi in sha Allah ba zata kuma ba, ai yanzunma Allah ya dawo mana da ita lafia ba karfinmu ko dabararmu ba ko? Kanta ta gyara a hankali sai kuma ta shiga sauke ajiyar zuciya A kadan dai sai da Malan ya jima dakin mama yana ta yi mata nasiha sai da hankalinta ya idasa kwontawa sosai sannan ya mike ya kalli agogon hannunsa ya ce" yau ban ga ana shirin zuwa turakata ba Murmushi ta yi tana rufe idannuwanta irin ta ji kunyar nan, hakan ya saka malan kara sakar mata murmushi ya juya ya fice a dakin, har tsakiyar ransa yana so ya je ya ga kar a je fadan da mamanta ta yi mata tana can tana kuka, kai a duniya da ake cewa ko cikin yaya Allah na saka maka kaunar wani ta fi ta wani, haka yake jin kaunar mai sunnan mamansa har baya iya boyewa, dalilin wannan ne ya saka shi daukan damarar boyewa ko a gaban mahaifiyarta ne bale a cikin yan uwanta da sauran matansa ko za.a shafa mata lafia Bayan kwana hudu..... Hafsat a kilace take cikin gidansu, an yi gumurzun an kare an yi rigimar da tashin hankalin an kare, an yi yawan maganar da tsegumin du an lafa, masu jiran su ga ta tsiro da dabanci kala daban daban sun ga shiru, Abdul aziz ya yi sau ya fi a kirga bai ga ko kalar mai kama da ita ba bale ya ganta, kai hasalima ta zama kawar mamanta da kuma yayarta A yanzu du zama da tashinta tana lure da kyawawan dabi.un mahaifiyarta, idan aikin mamanta ne takan shiga ta zabga masu girki na ji na gani mai dadin dandano a zuba kowa ya ci da sabon taste wa.inda ta koya a wajen Formation na zama bodyguard Bata da waya, bata damu da rikewa ba , ita ta kanta take sai a yamacin yau mahaifiyarta ta mika mata wayarta ta da wace masoyinta na da wanda sanadiyarsa ta afka tashin hankalin rayuwa Ta jima tana juya wayar kafin ta kai ta saka a caji ta ci gaba da sha.aninta A rana ta shida mai dinki wato hajia Farida ta kawo dinkunnan da mama ta bata , Ai kuwa dinkuna ne masu shegen kyau rufafu tsararu sannan na gayu masu tsadar gaske, Ba karamin farin cikin kayan nan ta yi ba, haka ta hau sama wajen mahaifinta dan yin godiya, tana zuwa ya kara mata abayoyi kala biyar masu shegen kyau na yayi dukansu masu botira da mayafansu bakake masu tsari Kanta kawai ta sada ta rasa bakin magana, a hankali ta dago da idannuwanta sai ta ga mahaifin nata na kallonta yanai mata murmushi, ba komai yake jin dadinsa ba sai yannayinta na yanzu, wai mamansa ce ke nuna farin ciki dan an