Sashe 53
Kutkale Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
a hankali Yana juyowa ya kurawa Hafsat dake kusa da BS ido, A hankali ya kai dubansa wajen BS din, da kuma Hasana.... Haka kawai ya tsinci zuciyarsa na cewa" ba abinda basu gani ba Rigar asibitin ya shiga cirewa hakan ya saka Hafsat saurin sada kanta daga dubansa da take, ba ita daya ba du wanda ke wajenma sai ya kawar da dubansa a kansa , wasu na mamakin shi bashi da kunyar cire kaya ne? Wa.inda suka san ko shi waye kuwa basu wani yi mamaki ba Wando da riga ya saka bakake lut, sannan ya saka gilas a fuskar tasa ya juyo wajen Malan dake tsaye, Zuwa ya yi sosai kusa da shi sannan ya duka har kasa, a hankali ya ce" na gode da mutuntani, da adu.o.i da nasihohi, in sha Allah zaka juya da Hafsat a yau yau.....zan zo nima domin zaman kasar nan ya fice min a rai Malan kam kansa kawai yake gyadawa yana kallonsa, haka ya mike ya fice inda suka mara masa baya gaba dayansu Suna fita daga asibitin ya mikawa BS waya, BS na gama sauraron maganar ya kalli Hafsat da sauri, sannan ya kali Abdul, Ganni ya yi Abdul din ba wani alamar fara.a a tare da shi, dan haka ya mika masa wayar ya je kusa da Hafsat ya yi mata bayanin abinda aka ce Ji ta yi kamar tsokanarta yake, dan haka da wani irin gudu ta karasa inda Abdul yake tsaye, Haki ne ya hanata magana sai nuni da take masa, Abdul ya lumshe idannuwansa yana mai jin nauyinta har cikin ransa ya ce" ki je Hawayen idannuwanta ne suka bale, cikin yannayin kuka ta ce" kana nufin..shikenan? Kana nufin na zama mai cikeken yanci? A yanzu ta waya ka saka aka sake ni daga kason da na shiga? Kana nufin zan ga mahaifiyata Dariyar da take ua saka shi tsurawa fuskarta ido, Hannunsa ya dago a hankali, hakan ya saka hannun nasa dake bari bari ya dora yar yatsarsa a gurbin kumcinta da ya lotsa sosai , sannan ya kama dan mayafin nata da ya fadi a kafadunta ya dora saman gashin kanta sosai ya rufe, Idannuwansa ne ya sauke saman kirjinta, lokaci daya gabansa ya buga da mugun karfi, lokaci daya kuma ya rintse idannuwansa a hankali ya ce" *zan waiwaye ki* Suna tsaye suna kallo ya shige wata mahaukaciyar bakar mota ya tayar ya harba bakin titi inda su hasana suka mara masa baya Gaba daya jikinta ne ya mace mata, bata son tafia ta barshi du irin zumudin gannin wannan ranar, Gata dai ga mahaifinta, sannan an tabatar mata da ta bi mahaifinta ta je gida ta huta ba tare da an tsara mata tsarin rayuwarta ba, Sai dai kash, yau ta tabata sabo tirken wawa ne, ita kuwa ta yaya zata iya sabawa da rashinsa bayan ya saba mata da shi a ko wani motsi nata? Dubanta ta kai wajen BD dake tsaye yana yi mata murmushi, sai a lokacin ta waiwaya sai ta ga mahaifinta baya nan, Da sauri ta ce" ina Abih? BS ya saki murmushi yana kallonta ya ce" sun tafi da Abdul, daga can za.a kai shi aeroport ne, akoy abinda zasu yi, mu je a can zamu hadu Ajiyar zuciya ta sauke ta daga kafarta ta shiga motar da ya nuna mata ya tayar suka kama hanya Ko a hanya hira ne BS ya cikata da shi, wanda dadaya take tsinta sai dai ta yi masa murmushi Cikin nutsuwa ya ce" kin taka sa.a, babar sa.ar rayuwa, wace ba kowa ke samun irinta ba, A yau na ga abubuwa da yawa, na ga ribar zuciya daya da girman adu.a, tabas a baya na yi sake da na ringa wasa da Sallah, ashe dai wanda ya rike Allah ba zai ji kunya ko ya wualakanta ba? Hafsat ta sakar masa murmushi tana mai kallon gari, itafa walahi har wata iska mai sanyi ce take ji tana ratsa gabanta..... Muryar BS ce ta tsinke tunaninta a lokacin da ya ce" *me zai hana ki cika min nawa burin nima? 1ki karbi tayin soyayata ki so ni tamkar yanda nake son ki Uman Malan?* Tsurawa fuskarsa ido ta yi tana kallonsa, Menene aibunsa? Dama sallah ce, a yanzu yana yin sallah tun karfinsa, Idan ta kai warhaka da karfinta a sha.anin kutakale tabas harda taimakon BS Yana biye da ita ne dan yana matsanancin son ta, Ita kuwa isan bata so shi wa zata so? Mutun ne shi mai daraja da daukaka, ya kasance mai kaunarta tun bata zama Bodyguard ba, ya kasance mai kawar da kai a irin halayanta na yau da kulun, ya jure iskancinta kala kala, baya hukunta ta, baya sakata kwana cikin maza.......yana kishinta, to ita kuwa wa zata samu ya yi mata irin wannan son? Kanta ta sada cikin yannayin kunya, abinda bata taba nuna masa ba a hankali ta budi bakinta ta ce"........ *KUTKALE* *(PRISON)* NA *SAJIDA* Marubuciyar DUK KARYAR KADA YAR MAHAUKACIYA DAGA TAFIA DAUKAR SOJA NEMAN NA KAINA BANI DA ZABI IDAN KA RAINA INDA KAKE BAK'A CE INA KUKE MASOYAN NOVELS DINA, GANI NA DAWO DA SABON SALO, SABUWAR TAFIA, NA ZO MAKU DA SABON NVL DINA MAI TAKE *KUTKALE* WATO GIDAN PRISON, WANNAN NVL ZAI ZO MAKU DA LAMURA DA YAWA, KU BIYO NI KU SHA LABARI........ *WANNAN NOVEL NA SIYARWA NE, DU MAI SO ZAI IYA TURA KUDINSA TA wannan acct NAIRA DARI BIYU : Usman Muhammad 3072998062 First bank. Sai ya turo shaidar ya biya ta wannan number +22791466605....sannan a yi adding dinsa cikin grup, MUTANENA NA NIGER KUWA SANADIYAR RASHIN SAMUN ORANGE MONEY DA KUKE YI, KUNA IYA TURO HOTON KATIN SAHELCOM KO NA AIRTEL TA NUMBER KAMAR HAKA 91466605 SAI A SAKA KU A GRUP DIN, .....* taku ce, Sajida 4 Cikin karfin murya ya ce" *INNALILAHI WA INA ILAIHI RAJ.UNE, ALLAHUMA AJURNI FI MASIBATI, WA KHALIFUNI KHAIRAN MINE HA!* Muhammad da sauri ya karasa inda yake tsayen ya riko hannun nasa da ya daki garun da shi yana kallo da yannayin mugun tausayawa ya ce" ka bari mana, dan Allah ka bari Abdul ya rike hannun nasa shima ya ce" me ake so da ni? So ake a taba imanina ne? Muhammad za.a saka ni na fara zance a titi, zan iya fita da gudu a kowani lokaci Muhammad ya kara shiga kirjinsa irin ya hana shi maganar nan, aman a kasan zuciyarsa murna yake na lale lale bukatarsa ta kusa biya, burinsa zai cika na gannin Abdul ua wulalance kafin ya aika shi lahira, A haka shima aka nade shi aka fita da shi, inda su BS ne, sojoji da polisai ne, sai kwaya dayan sojan Muhammad da ya bari dan kuwa ya salami sauran dayan nan kwal shi ke biye da shi Sai da kowa ya watse sannan suka fito tare suna tafia du da yannayin rashin karfin jiki da rashin laka, Muhammad ya kale shi ya ce" ka yi hakuri, na san da ciwo Abdul a kashe maka lanwarka, a kashe maka mahaifinka, a kashe maka mahaifiyarka, a zo a kashe maka kuma yar uwarka daya da ta rage maka? Abdul ya ja ya tsaya , sai da ya dan dafe kansa sannan ya ce" ba yar uwata bace Muhammad ya tsura masa ido yana kallon sa ya ce kamar yaya? Abdul ya daga kafadunsa ya ce" ba yar Abdul Basid ba ce, Aman ya aka yi ka gane haka? Muhammad ya fada cike da mamaki Abdul ya waiwayo shi sai kuma ya saki murmushi ya ce" tana zaman kanta a saudiya kusan shekara goma sha bakwai, ita din haifafiyar maradi ce, iyayenta du sun mutu, ta fita neman na kanta da kanta ne, Muhammad ya yi saurin cewa" to me ya kawota nan, me ya hadata da tsohuwar matarka? Abdul ya shafa sajen fuskarsa sannan ya daga kafadunsa , Muhammad ya kasa sammun nutsuwa suka ci gaba da tafia da Abdul har suka shiga baban falonsa, Muhammad ya ce" Abdul, sai nake gannin hankalinka a kwonce, wannan matar ta zo da niyar cutarka fa, domin ta zo a matsayin wai yayarka, hakan kuma harda tsohuwar katarka, ta zo dan dukiyarka ko dan rayuwarka? Abdul ya ce" eh, aman ai ka ga Allah ya tsayar da lamarin da kansa Muhammad ya kura masa ido ya ce" to aman ita matar taka ina take? Ina ta shiga? Sai da Abdul ya fara tafia dan kuwa jirri yake ji sosai dan hankalinsa ba a karamin tashe yake ba , gaba daya ya sare , tsoro ya lulube masa zuciya na tunanin a wani hali Hafsat take ciki? Ko har an kashe ta ne? Da kyar ya iya tsayawa ya juyo ya ce" tana boye , ni kaina ban san inda suke bata soin ba! Haka Muhammad ya yi shiru yana kallon sa har ya shige dakinsa na baci, Yana shiga nan ya fadi ya rintse idannuwansa yana jin yanda kansa ke sarawa, ya Allah, ya Allah shi ya fi maimaitawa yana mai neman hawaye su zubo masa aman shiru basu zubo ba Wayarsa ce ta dauki kuka dan haka ya mika hannu ya lalubo ba tare da ya duba mai kiransa ba ya kara a kunnensa yana sauraro A takaice aka ce" *jarumi ne kai, cikin da ta fita da shi barinsa ta yi bata haife shi ba, zubar da shi ta yi Abdellah, tashi kar a cin maka a lokacin da kake halin kaka naka yi* Ihu ya yi da haushi ya nausa wayar a kasa A cikin wannan rayuwar kunci aka ci gaba da tafia da Abdul da Muhammad da mutanen dake tare da shi, Wa.adin da malan ya dauka na sati daya cir suna wata nafila tsakiyar dare daga shi har Abdul dan neman haske da bayanar Hafsat a wajen Allah ya zo ya cika aman shiru Hankalin Abdul ya kara tashi, shi dai du ya daburce abinsa aman yana yin bakin kokarinsa yana boyewa dan gudun hargitsa lamarin Muhammad dake tare da shi ba dare ba rana A rana ta tara , ya tashi da matsananciyar faduwar gaba, Tazbaharsa ya lalubo ya shiga lazumi zaune saman salayarsa, har lokacin komawarsa baci ya yi na wajen karfe goma aman shiru