← Book details Kutkale Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 16 OF 94

Sashe 16

Kutkale Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

maki haka har kika rasa ranki a lokacin da ni sauna nake kofa tsaye dan zama mai kare lafiyarki.......... Gaba daya wajen, su su uku ne dama, domin Boy bai fito ba tukunnan yana daki, wajen gaba daya tsit ya yi kafin cikin matsanancin faduwar gaba madame bilkissu ta saki cokalin tana dubanta ta mike tsaye ta ce" ke, me kike nufi haka? Me menene wannan din kuma? Hafsat ta yi murmushin da har cikin ranta yannayin da ta nuna ya bata dariya, bata son mutuwa wai ita wannan? Ikon Allah, yanzu ita bata so ta mutu, so take ta yi ta rayuwa cikin jin dadin nan har yaushe? Har a busa kaho ko me? Murmushi ta kuma yi ta ce" aa, bafa mutuwar bace Madame, Wai yanda aka tsara lamarin karshenki ne na baki a takaice, Wata irin tsawa ce ta daki kunnayensu daka wajen matatakala, ashe Boy ya sauko yana sauraro, Jikinsa na rawa ya karaso yana dubanta ya ce" kashe mini uwa zaki yi? Wannan wani irin banzan zance ne? Tunda kika zo gidannan dai abincin oder ake ci dan kin kori yan aiki na odernma ke ke kawowa dan baki yarda da kowa ba, idan kika fadi haka, wannanma na yau ke kika kawo shi, kennan kece zaki kashe min uwa ko me? A nitse ta ce" aa dan jaririn mamansa, ba.a kai ga wanda na kawo din ba kennan, Ni ne jaririn? Ni ne jaririn? Ya fada da hargowa yana dubanta yana matsowa da niyar kai mata duka Da sauri madame bilkissu ta tare shi ta riko hannunsa ta maido shi kusa da ita tana duban yannayin Hafsat ta ce" ki bani haske kan maganarki , a kan aikinki kike kar ki manta, Hafsat dake sauraron maganar su BS da suka karaso da police ta kai dubanta wajen Joli dake tsaye itama gaba dayanta, du wani alama na rashin gaskiya ya bayana a tatare da ita ta ce" bomb da aka saka a motarki, ta sayeta ne da makudan kudin da kike sakar masu a acct, ta hanyar kawarta dake da yaya dan fashin boye, wanda yake harkar miyagun makamai a boye , Bata cinma burinta ba na kashe ki ta hanyar bomb, ta siyi dan sholisho kan ya soka maki wuka, wanda mun fito daga alimentation ya shigo mu da gudu da wuka na karbe, wannan ma bai mata ba, ta so ta buga zuciyarki ta hanyar kiranki tsakiyar dare ta fasa maki kuka dan ta san kinada mugun hawan jinnnin da tabas damuwarta na iya tada maki ita....... Wannanma ba.a samu galaba ba, shi ne aka gwada ta jus jus, shima du na canza su, yau aka gwada ta hanyar yin Fride rice, abincin da kika fi so, Wai wai wa kike nufi? Ya zaki ringa magana kina duban Joli? Me kike nufi? Karan laluwar da ya karade anguwar harma dake nuni da cikin gidan yake nufowa ya saka Joli sakin marfin glass na kwannon cin abinci ta juya da gudu ta nufi waje da niyar neman inda ta tsere, Wata irin juwa ce ke neman kayar da ita, nan da nan boy ya tareta a jikinsa, jikinsa na rawa da mamakin wai da da gaske da take cewa zai zama nata niyarta ta kashe matar da ta dauketa ta mayar da ita mutun? Magani ta balo wanda dama ta san a rina ta mika masa ya saka mata a baki , aka bata ruwa sannan aka jinginar da ita inda gidan ya rikice da hayaniyar kama Joli, Idannuwanta da sukai mata nauyi ta daga ta dubi boy, muryarta na rawa ta ce" Boy, kace min karya ne ka ji? Kace min ba haka bane, me me ya sa ? Me yayi zafi Boy? Ashe dama makashina na tare da ni? Me na yi da zafi haka boy? Boy ya sada kansa yana kuka kamar yaro gannin yanda mam dinsu abu ke cinta har zuciyarta, Wani abu Hafsat ta ji a ranta, tausayin matar, tabas ita fa a matsayin yayanta na cikinta ta dauke su, idan kuwa har haka ne dole ta ji mugun mikin da zai yi barazana wa numfashinta, A hankali ta matso kusa da ita ta tsaya ta ce" ke fa lauya ce hajia, kin yi shara.ar da ta fi haka gigita, dan yau ya zo a kanki idan har kika yi hakuri zaki bada exampl wa duniya, Ke kika bani kalmar dan adam mugun ice ne, Ni kuwa zan kara maki kalmar Allah na jarabtar bawa da abubuwa da yawa, ciki kuwa harda raba bawa da abu mafi soyuwa a ransa, yaya ne, iyaye ne, kudi ne, mata ce, ko miji ne...da dai sauran su, Da ciwo, aman kar hakan ya zama sanadiyar rugugewar tsayayiyar lauya mai kare yancin matan garina Kallonta kawai suke gaba dayansu, har BS ya shigo falon, Nan ta mike ta sara masa tana dubansa har ya bata izinin tana iya sauke hannunta, Likitan da aka zo da shi ne ya karaso aka kama Madame bilikiss aka dora gado na turawa aka fita da ita,.a takaice dai kafin su bar gidan sai da suka daidaita komai, suka kwashe komai na dakin joli dan karin bincike suka bar gidan tare da Hafsat Sai da ta yi wanka ta mike saman gadon dakinta da aka maida su masu gadaje ta lumshe idannuwanta, Maganar BS ke dawo mata, ashe zasu shirya da shi? Lale duniya, ......... Ummih, bafa zan zauna kato na take min baya a dukan motsina ba, haba ummih ba zaki bar maganar nan bane? Zama ta yi kusa da shi tana dubansa ta ce" kana so na mutu? Da sauri ya dago da dubansa kanta shima yana dubanta , murmushi ya sakar mata, sak yanda take masa yana yaro idan ya ki yarda abu, tsoron hakan ke saka shi amincewa da koma menene, shine yanzuma zata yi masa, Hannayenta ya riko yana dubanta , ya ce" idan kin amince da abu daya, zamu je tare da ke, a bani na zaba, aman fa mace, a bisa sharadin zamu baro wajen da sunnan matata take, dan kin ga zata zame min karfen kafa, du inda na shiga zata ce sai ta shige itama, zamu ringa kwana gida guda....... Ni ban ce zan yi wani rayuwar aure da gardi irina ba, dan kuwa du macen da ta san ciwon kanta ba zata dauki kafa wai ita ta je ta yi gudu ta shiga duniyar mazajen daga tace itama yar dagan ce na iya kallonta ba, aman saboda irin rayuwar da ake a nan, da irin yanda aka cakulu ake cakuda abubuwa, ga auren nan da kika saka a yi na yarinyar nan, kin ga zan so ta bata tsaron, aman wai ba ni ba, aman kuma a matsayin wace zata fito a Bodyguard kuma matata *Wannan cakwakiyar fa? Mai yiwuwa ce? Yan matan Bodyguard, damar au yi auren ana nufin irin wannan ko me? Idan irin wannan ne daman ana iya aure haka? Aure dai ai aure ne, ana iya rayuwar aure da su normal ko yaya? Irin matarka ce idan ta raya maka matarka ce?..............mu je zuwa karatun Kutkale* *KUTKALE* *(PRISON)* NA *SAJIDA* Marubuciyar DUK KARYAR KADA YAR MAHAUKACIYA DAGA TAFIA DAUKAR SOJA NEMAN NA KAINA BANI DA ZABI IDAN KA RAINA INDA KAKE BAK'A CE INA KUKE MASOYAN NOVELS DINA, GANI NA DAWO DA SABON SALO, SABUWAR TAFIA, NA ZO MAKU DA SABON NVL DINA MAI TAKE *KUTKALE* WATO GIDAN PRISON, WANNAN NVL ZAI ZO MAKU DA LAMURA DA YAWA, KU BIYO NI KU SHA LABARI........ *WANNAN NOVEL NA SIYARWA NE, DU MAI SO ZAI IYA TURA KUDINSA TA wannan acct NAIRA DARI BIYU : Usman Muhammad 3072998062 First bank. Sai ya turo shaidar ya biya ta wannan number +22791466605....sannan a yi adding dinsa cikin grup, MUTANENA NA NIGER KUWA, ZAKU YI MIN ENVOI NA DALA DARI BISA NUMERO KAMAR HAKA 92777744 AMAN FA TA ORANGE MONEY.....* taku ce, Sajida 4 *Free page* Ana mayar da ita cikin kurkukun dakinsu ta ja ta tsaya sanadiyar ganninsu da ta yi fada suke mata kowace na rantsuwar a barya da ita ta koya mata hankali, Ganninta ya saka suka fara nufota da yannayin izgilanci suna rantsuwar yau sai dai gawarta, bale masu zaune a wajen da nufin daurin rai da rai, Da gudu ta warci tabaryar da ake dakan da ita, daidai saratu ta karaso wace ta fi kowa rawar kafa dan samun gidin zama wajen Eliz, sai dai me, batai wata wata ba ta daga tabaryar nan ta sheka mata ita a goshi, sannan ta aniya tarban wa.inda basu rigai sun karaso din ba, ja suka fara yi suna tsayawa, kai danma zaman balaki ne zaman kurkuku? Da me zai saka ka tarban gabanta? Mai zai kaika yin wannan kasadar? Bata ji bata gani, idan ta rufe ido kawai a fado a mutu ne, Cikin hargagi da iface iface suka shiga dankarawa da gudu, wasu na zagayawa suna nufar wajen sojojin gidan, Sojojin du mikewa suka yi tsakaninsu suna magana, ba wani abu ba suke cewa sai canko cewa da Aljanar prison ne ake fada, harda masu saka kudi, sannan bakin zuwa sun cika da mamakin wai ita haka take? Da gudu suka shigo da shirin ko ta kwana, gaba daya suka rufta masu suka shiga dukansu, ba ji ba gani, duka kawai suke sha, sai da suka yi laushi sannan aka barsu, aka tiso keyarsu dan dora garin da suka surfa ba wankewa sai fecewa da suka yo suka kuma daka shi ya zama gari suka dora tuwonsa, inda masu tuka tuwon du suka tafi wanke helunan da zasu tuka tuwon da shi, Can gefe kuwa Eliz ta hasa wuta da itacen mainan da mazan ke yowa a wajen su hura wutar ta dora tankamemiyar tukunya ta kawo tunjumemen ruwa ta maka ta zuba yan kayan miyan da suka samu, ta afka gishiri, sai dakakiyar miyar da suka dakata da kansu bayan miyar ta tashi sosai ta kawo ta kada da katuwar sanda ba ruwanta da wani burkakewa ta kawo dan mai kadan ta afka abinta ta juya ta zauna tana jira ta yi dan kauri a shiga rabo, yau ta yi niya dan ubanta ba zata samu tuwo ba! Zata nuna mata wanda ke
Chapter 16 · 0% Book details