← Book details Kutkale Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 45 OF 94

Sashe 45

Kutkale Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

saya mata sutura, yarinyar da a da hayowa zata yi, ba ruwanta da neman izini sai dai ta afka idan a gaban wa sai dai ta fadi muradinta na kudi ta karashe da fadin" kuma a bani ko na je saurayina ya bani! Sai gashi yanzu a gidan duniya Allah ya nuna masa ita tana godiya harma ta rasa bakin godiyar Hannunsa ya daga mata dan ya tabata tana iya yi masa kuka a gurin , shi kuwa baya so , dan haka ta mike har ta kusa fita ta tsinkayo muryarsa ya ce" su ABDALLAH zasu dawo gari da zama karshen satin nan, kwana biyu ina tsaye kan saukar alkur.ani a gidan da zai zauna , kulun muna zuwa a sauke a yi sadaka dan gudun fitinar zamani Sai da gabanta ya fadi, a ranta ta ayanna me kuma zai dawo da shi kasar Niger? Kafadunta ta daga a lokacin da ta tuna asalin dan niger din ne shima fa, haifafan garin ne, haka kuma dangin da suka rage masa yan nan ne wato matarsa da kanwar mamansa Bata baiwa Malan amsa ba sai karasawa da ta yi da murnarta suka dadaga kayan da mahaifiyarta kafin su shiga yi masu turaran wuta da adu.ar Allah ya sa a mora lafia Bayan kwana goma Kwonce take tsakar dakinta wajen karfe biyar na yama, juyi kawai take tana tunanin wai yau zata yi zance, zancen ma da BS, zuwansa biyu sai yau Malan ya bashi damar ya zi su gana Mikewa ta yi zaune tana kallon madubin dakinta mai tsayi, kanta ta girgiza ta koma ta kwonta gashi har karfe bakwai din ta kusa, Tana nan kwoncen har karfe shida ta buga, buda kofar da aka yi ne ya sakata mikewa zaune tana kallon yayarta da ta shigo da yaronta da ya fara rarafe yana yawonsa ko.ina Bayan sun gaisa ne yayar tata ta bita da kallo, Can ta ce" Maman malan, ni ba bako aka ce zaki yi yau ba? Hafsat ta dubeta ta ce " eh Yayarta ta ce" to ya haka baki shirya ba Hafsat ta kaleta da mamaki ta ce" shiryawar me kuma auntu ? BS ne fa?? Sai da ta rike habarta sannan ta yi dariya ta girgiza kai ta ce" dan BS ne shine ba zaki kimtsa jikinki ba? Oya tashi tashi malama Mikewa Hafsat ta yi tana kallonta kafin ta shige ciki ta dauko abaya daya daga cikin abayoyin Aba ta saka abinta a nan sannan ta shiga saka turarukan wutar da ta miko mata Tana kokarin yana mayafin dan kwalin ta tsayar da ita ta zauna ta dan gyara mata fuska da kwalinta sannan ta yana mata dan kwalin a kanta Tsaf hafsat ta fito tamkar ba ita ba, wani irin kyau ne ya bayanna a tare da ita wanda ita kanta sai da ta shafa gefen fuskarta sannan ta yi murmushi Ana fitowa sallar magariba aka suka zauna tsakar gida inda malan ya basu minti talatin su gana A zancen nan Hafsat banda tambayoyi a kan aiki ba abinda ta tsare BS da shi, shi kansa sai ya kasa wani yi mata zancen soyaya sai da ya tashi tafia ne ya ce da ita" Hafsat, ina son na turo a yi komai da wuri a gama, dan kin ga malan baya son dogon zance Sai da ta ji gabanta ya fadi, ta dan tsura masa ido aman sai ta kasa ce da shi komai, Murmushi ta sakar masa sannan ta shige ciki da dan gudu gudu hakan ya saka shi sauke ajiyar zuciya ya juya ya tafi ya shiga galeliyar motarsa yana tunanin sai dai a waya ya mata maganar aikinta da kuma dukiyarta Can wajen karfe biyun dare, dare ya tsala Hafsat na zaune tsakiyar gadonta daga ita sai dan gajeran wandonta da yar rigarta na barci ta yi zuru da wayarta a hannunta tana dannawa tana game Message ne ya shigo mata kamar haka " *KAURIYATA, NA KASA BACI* kurawa harufan ido ta yi tana kallo, bugun zuciyarta ne ya canza lokaci daya hannunta ya fara rawa, Du duniya ba wanda ke haye mata irinsa, shi ne, walahi shi ne Wayar ta ajiye tana kallon rubutun tamkar wanda ya yi da hannunsa idan hasken wayar zai dauke sai ta danna ta kara kallo A hankali ta rubuta " *ME YA HANA KA BACI?* mikewa ya yi zaune daga kwoncen da yake yana mai hararar wayar, kafin ya rubuto " *ke, gida kika je kika tara samari haka? Bakya dan jan aji daga yi maki magana har ki bani amsa ko kin sanma da wa kike magana ne?* A lokacin da ta karanta sai da ta saki murmushi, sannan ta rubuto" *na san ko kasuwa na yi a tsakiyar dare irin na barawo? Dole bazawara ta ringa damka da karfi karfinta mana* Wani uban tsaki ya ja a lokacin da ya karanta message din, Zama ya gyara ya shiga dandankara magana son ransa, har ya so saki sai kuma ya koma da baya ya zauna ya jinginar da kansa jikin bed din, ajiyar zuciya ya sauke yana kallon waje daya sai kuma ya rubuta message kamar haka" *Na yi missing din ki amaryar BS* Numfashinta ne ta fara ji yanai mata sama sama, lokaci daya kuma ta koma ta mike kafafuwanta saman bed din , sai da ta yi mika nitsatsiya sannan ta rubuta message kamar haka......... *KUTKALE* *(PRISON)* NA *SAJIDA* Marubuciyar DUK KARYAR KADA YAR MAHAUKACIYA DAGA TAFIA DAUKAR SOJA NEMAN NA KAINA BANI DA ZABI IDAN KA RAINA INDA KAKE BAK'A CE INA KUKE MASOYAN NOVELS DINA, GANI NA DAWO DA SABON SALO, SABUWAR TAFIA, NA ZO MAKU DA SABON NVL DINA MAI TAKE *KUTKALE* WATO GIDAN PRISON, WANNAN NVL ZAI ZO MAKU DA LAMURA DA YAWA, KU BIYO NI KU SHA LABARI........ *WANNAN NOVEL NA SIYARWA NE, DU MAI SO ZAI IYA TURA KUDINSA TA wannan acct NAIRA DARI BIYU : Usman Muhammad 3072998062 First bank. Sai ya turo shaidar ya biya ta wannan number +22791466605....sannan a yi adding dinsa cikin grup, MUTANENA NA NIGER KUWA SANADIYAR RASHIN SAMUN ORANGE MONEY DA KUKE YI, KUNA IYA TURO HOTON KATIN SAHELCOM KO NA AIRTEL TA NUMBER KAMAR HAKA 91466605 SAI A SAKA KU A GRUP DIN, .....* taku ce, Sajida 3 Sai da ya gama yi masa wani kallo sannan ya ce" kai, banma taba sannin irin girman rainin hankalin da ka yi min ba sai yau da na tabatar da abinda na dauki shekaru ina fada maka baka yarda ba! Muhammad ya nemi waje ya zauna yana dubansa, da irin duban da yake masa a kulun idan ya yi maganar cewa mahaifinsa na raye, ya tabata yau din ma maganar ne dan haka ya yi masa wani zuru yana kallonsa irin kai nake sauraron nan Abdul ya gyada kansa yana kallonsa, Girgiza kai ya yi ya Mike ya gyara rigarsa da ta yakune sanadiyar daukansa da aka yi har sau biyu, Tsaki ya ja a fili mai mugun karfi ya juya ya fita shima a dakin ya bar Muhamad zaune yana mai binsa da kallo Sai da ya tabatar da ya fita ya dauko wayarsa ya kara shiga dakin ya danna wata number ya shiga waya cikin rage murya sosai yanda idan ba kai ne yake yiwa maganar ba zaka yi ba, hakan ya saka ban fahimci abinda yake fada ba Abdul, yanda ya ga dare haka ya ga rana, zuciyarsa ciwo take masa, yana mai jin wani irin tsananin haushin Hafsat da ta tare masa gaba ta tsayar da shi wa aikata abinda ya fi buri a rayuwa, bai taba tunanin wata halita zata shiga gabansa , ta tare masa aiwatar da harbe Abdul basid, muten da ya yi sanadiyar mutuwar mahaifiyarsa, da kanwarsa, sannan yake neman rayuwarsa, sai gashi, yarinyar karama da zai yi kanwa ta biyar da ita, yarinyar da bai hada komai da ita ba ta zo ta shiga gaban mutumen da yake nema ruwa a jalo aman ya ji gabansa ya yanke ya fadi, hannunsa ya kwashi rawa? Saman bed din daya daga cikin sauran dakunnansa ya kwonta ya mike kafafuwansa ya lumshe idannuwansa, Tamkar an dake shi ya zabura ya zauna, dan kuwa hasko masa ita ne aka yi a lokacin da ta yi tsaye da bindigarta ta yi rantsuwar sai dai ya kasheta kafin ya kashe mutumen nan, Hannunsa ya saka ya mari gefen fuskarsa ya ce" ABDUL me ya hana ka harbeta kafin ta yi shiru a maganarta? Abdul me ke damunka har haka? Abdul kana ji kana gani ya kubuce maka bayan ka gansa a raye? Ba zaman jeji ba ko zaman cikin rami ko rijiya zaka koma sai na kara samo inda kake , kuma ba wai wannan yarinyar ba, ko wa ya shiga tsakanin bindigata da kwakwaluwarka sai na harbe shi kafin na harbe ka! Idannuwansa ya kuma lunshewa yana sakar zuci, shi dai a tambaya daya ya tsaya wace ya rasa amsarta gamsashiyar da zata saka shi kawar da kai ya manta komai hakan ya saka shi kwana zaune, yanda ya ga dare haka ya ga rana Washe gari wajen karfe tara na safe, hayaniyar da ya ringa jiyowa kasa kasa ce ta saka shi mikewa daga saman salayar da ya keana kaiwa Allah subahanahu wata.ala kukansa Labulen dakin ya dan ja ya leka kansa, Ikon Allah, shi ne kalmar da ta fara fitowa da bakinsa zubewa lebensa Ido ya kurawa yan mata biyun da yake hange daga dakinsa, Wannan matarsa ce Bahija, wace ta gudu ita da Mariam, kwarai wannan bahija ce, dayar da ta bayar da kanta gefe ce bai fahimta ba, Aa, yaya aka yi bakin fuska suka samu damar shigowa har tsakar gidansa? Yaya aka yi haka? Tsayuwa ya yi ya harde hannayensa yana kallo da kyau BS ne ya yi tsaye a gabansu ya ce" dan kina tsohuwar matarsa bai bamu damar dan kina haka ki zo kai tsaye ki shiga har inda yake ba, ki juya wanda ya baki damar shigowar da ya sanki ya shigo ya hau wajen Sire ya tambayo shi ya kuma sako ki ciki, aman daga inda nake tsayen nan ba zaki shiga ba Kallonta ta sauke saman kansa a yatsine, ta mayar da dubanta wajrn
Chapter 45 · 0% Book details