Sashe 36
Kutkale Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
bai so haka lokaci daya ta tarwatsa komai ba, dan kuwa a lokacin da aka yi shari.arta yana wajen, yana zaune a wajen, shi da shi aka kama dan ta.adar, ya san waye shi, sannan a lokacin da aka bata damar ta yi magana a kotu magangannun da ta jefowa lauyan suka kara saka shi shakun abinda ake tuhumarta da shi du kuwa da irin yanda lauyan ya tafi da imanin du wanda ke wajen, A haka ya ringa bibiyar zamanta a gidan yarin, a hankali ya ringa samun amsoshin wasi wasin da ya ringa yi kanta, sai dai baban tashin hankali maganar dake dakatar da shi wace kaf anguwar su yarinyar ba wanda ke mata shaidar arziki, wani idan ya buda baki ceqa yake wa wai Khadija? Ai sunnayenta da yawa muguwar yar daba ce.... Su sunai haka fasara daban ta irin mugun rashin jin maganarta, da mugunta wajen fadanta, Iko kuwa zai yiwa maganar fasara daban duba da irin halin da aka kamata aka ce itace da hakan, Suturar da aka kamata da ita, ba wani dan kwali, ba hijabma sun taimaka wajen bada gudunmuwar rashin samun tudun dafawa, Hakan ya saka shi jin tausayin irin hidimar da mahaifinta ke yi, da irin hirarsa dadaya da ya tsinta a masalaci da aminansa kan yarinyar, ya saka masa tausayi da son yin ceto, Shi ya saka shi ya kasa zaune ya kasa tsaye, ya hana kansa baci sai da ya samu ya yi convaincre (ya ci galaba) din wanda ya yanke mata hukunci aka yarda da zata iya wannan aiki, aka bata dama dan karancin shekarunta da tarin iliminta ana hasashen zata kawowa kasa ci gaba, aka kawota sai gashi du ta shanye wahalhalun da jarabawar da yawa sai yanzu da za.a fita da ita take faman farke komai a gaban wannan lauyar da tana iya ja da kowa bata da dar, wanda hakan na iya ja, a yau a yanzu a mayar da ita gidan kason da bata taka ba, bata karya ba! Hakan ya saka shi tafka mata tsawa ta hanyar fadin" *LA FERME SOLDAT* (CHUTUP SOLDIER) Shiru ta yi da maganarta sannan ta kame ta sara masa, A hankali matar ta karasa shigowa tana dubanta da kyau, sai da ta gama karantarta ta ce" menene dalilinki na son shiga hurumin shari.ar bayan ke kariya kawai aka ce ki bani? Shiru ta yi kanta a sade, jikinta kam ya mutu dan karara ya fada mata cewar ta maida hankali, wannan aikin shi ne tikitin fitarta daga *KUTKALE*, Hankalinsa ya maida wajen lauyan ya ce" MADAME BILKISSU, ki yi hakuri, zamu maida ita baya mu bata horo, Kanta tsaye ta ce " ina son na ji amsar tambayata, Kallonta ya yi da yannayin takaici ya ce" ki bada amsa! A hankali ta dago da dubanta ta saka dara daran idannuwanta cikin na matar ta ce" na yi wannan tambayar ne dan ina son na yi bincike a tsanake kan wanda ya dace na fi saka idona a kansa a harkar aikina, Shin wa.inda kuke shari.a da su ne? Abokin shari.arki da su ne? Ko kuwa a cikin gidan da kike rayuwa ne? Ki yi hakuri aman an koya mana cewa mu kasance komai ba jikinmu ya zama idannuwa, kwakwaluwarmu ta kasance tana aiki kowani lokaci, aman kuma mu tabatar da muna da abinda zamu fi sakawa ido, Ba nan na nufa ba, ta yiwu wa.inda kuke shari.a da su, kaurin sunansu ya sa aka kalubalance su cewar menace din da kike samu na za.a kashe ki su ne, mai yiwuwa wani ya fake da haka ne dan ya cinma wani burinsa, Makashi, baya bada damar a gyara ko ya yi kisa, makashi na yin kisa ne sai dai kowace wace, an kwana da sannin cewa ba zaki ja da baya kan ra.ayinki na shari.ar da ta tunkaroki ba, kokonto ne ya darsun mani na cewa, wanda kike shari.a da shi....anya kuwa mai laifi ne kamar yanda ake hasashen yana iya bi ta kasa ya tsorataki dan ki bar shari.ar da kike? Ko dai kaurin sunnansa ne ya jaza masa jafa.i????? Ta karashe tana mai duban GN wanda ta yi maganar kaurin sunna ya jazawa mutun balaki da biyu..... Gaba dayansu ita suke kallo, Lokaci guda Madame Bilkissu ta kara shigowa face to face da Hafsat ta ce....... *KUTKALE* *(PRISON)* NA *SAJIDA* Marubuciyar DUK KARYAR KADA YAR MAHAUKACIYA DAGA TAFIA DAUKAR SOJA NEMAN NA KAINA BANI DA ZABI IDAN KA RAINA INDA KAKE BAK'A CE INA KUKE MASOYAN NOVELS DINA, GANI NA DAWO DA SABON SALO, SABUWAR TAFIA, NA ZO MAKU DA SABON NVL DINA MAI TAKE *KUTKALE* WATO GIDAN PRISON, WANNAN NVL ZAI ZO MAKU DA LAMURA DA YAWA, KU BIYO NI KU SHA LABARI........ *WANNAN NOVEL NA SIYARWA NE, DU MAI SO ZAI IYA TURA KUDINSA TA wannan acct NAIRA DARI BIYU : Usman Muhammad 3072998062 First bank. Sai ya turo shaidar ya biya ta wannan number +22791466605....sannan a yi adding dinsa cikin grup, MUTANENA NA NIGER KUWA SANADIYAR RASHIN SAMUN ORANGE MONEY DA KUKE YI, KUNA IYA TURO HOTON KATIN SAHELCOM KO NA AIRTEL TA NUMBER KAMAR HAKA 91466605 SAI A SAKA KU A GRUP DIN, .....* taku ce, Sajida 3 Cikin murmushi, da yannayin raini Abdul ya dora yatsarsa saman lebensa ya ce" shiiiiiiit, Sai da ya kikifta ido sannan ya ci gaba da fadin" Huraira? Not Furaira, u.r wlcm yar uwa, ku ware mata daki, wannan da kuke ganni an sameta ne ta hanyar kauna, ita din yar kauna ce Wani dan murmushi ta saki , a hankali ta janye hannunta ta ce" thanx Kafadunsa ya daga yana tsaye ya ga soja biyu sun nufi dayan bangaren dan ware mata dakin da zara zauna Juyawa suka yi ita da Bahija dan zuwa wajen, yana kallon su Sai da ya ga Bahija ta kusa shiga ya kalli gefen da Hafsat ke ciki, cikin yannayin basarwa ya ce" kirawota Nunatan da ya yi ya saka ta gane wace yake nufi, juyawa ta yi ta nufi wajen su ta kirawotan saannan ta dawo ta tsaya inda take tana mai satar kallonsa S lokacin da ta zo daf da shi, hannunsa ya mika mata yana kallonta Hannunta na rawa ta saka cikin nasa, da yannayin nunin soyaya ya janyota a hankali jikinsa yana mai daga kansa ya hangi window din Ni.ima dake tsaye tana kallon du abinda ke faruwa, ya kuma maida dubansa wajen masu tsaron ba tare da wani dar ba ya dan saki wani dan karamin murmushi ya sakata cikin jikinsa ya bata kyakyawar runguma Ajiyar zuciya ta sauke ta yi luf a kirjinsa tana shakar kanshin turaransa mai dadin gaske, Bakinsa ya kai daidai kunnenta, wanda du bawan da ya ga haka zai dauka wani kalaman soyaya ne yake shirin rataba mata dan har dan rausayawa kadan yake da ita a cikin kirjinsa A hankali ya ce" me kika zo yi gidana ne Bahija? Bahija da ta lumshe ido tana jin wani irin mugun kaunarsa a ranta a hankali ta amsa shi da" na yi missing dinka ne, ka yi hakuri Abdul ya dan saki murmushi ya ce" kin min laifi ne? Kanta take gyadawa a hankali a jikinsa sannan ta ce" ban gujeka da son raina ba, na gudu ne dan tsoro Abdul Jabar Abdul ya lumshe idannuwansa irin kalamanta sun masa dadin nan, sannan ya ce" ba laifi, *Bahija, ni Abdul Jabar mijinki, na tsinke igiyoyin auren da aka daura min da ke saki uku bisa dalilina na bin maza da kike, daga yanzu idan kika samu miji zaki iya aure, ban lamunce maki zaman minti daya a gidana ba, sannan idan na sake ki abu daya zai hana ni damun rayuwarki, ina nufin bin rayuwarki na tagayara ki shi ne ki mana min kiss a kuncina ki juya da niyar kin tafi ki dawo, idan kika kuskure da nu kike magana!* Gaba daya jikinta ne ya kwashi rawa, tana so ta dago da mugun firgicin da ya daketa sai dai ta kasa hakan ya sakata yin wani irin lakwas tana limshe idannuwanta da suka cicika da kwallah, A hankali ta ce" Abdul, Abdul ya ce" shuiiiiiiiiiiiiiiit Idannuwanta ta lumshe ta kuma budewa ta ce" *ABDUL, MAKASHINKA NA TA...* ABDUL ya kuma wani irin matseta a jikinsa ya kara cewa" i said .....Shuittttttttttttttt A hankali ya sasauta rikon da ya yi mata ya saketa baki daya yana sakar mata murmushi, sannan ya saka hannayensa ya share hawayenta a fili murya a dan dage ya ce" to meye na kukan? Ba gashi kin dawo ba? Ki je gidan zan zo Ya karashe yana kashe mata ido daya Murmushi ta kakaro itama ta matso jikinsa sosai ta yi dadage saman dogon takalmin dake kafarta ta mana masa kisss a kuncinsa kamar yanda ya umarta mata ta juya ta nufi motar da suka zo da ita cike da faduwar gaba da fatan Allah ya fidata lafia daga gidan Hafsat dake tsaye a hankali ta jinginar da bayanta jikin garun wajen ta lumshe idannuwanta tana mai jin zuciyarta na wani irin dokawa tamkar zata ballo kirjinta ta fito Abdul dake tsaye ya kuma mayar da dubansa dakin da aka kai yarinyar wace ta yi ikirarin ita yayarsa ce wato yar Abdul Basid, a hankali ya kara satar saitin tagar dakin Ni.ima, nan ya ga bata wajen, dubansa ya dan saci kallon dakin Muhammad, Tsai ya tsayar da idannuwansa wajen, kallon wajen yake sosai inda kansa ya sara, Dubansa ya kara maidawa dakin Huraira, Juyawa ya yi ya koma cikin dakin inda su Hafsat suka bi bayansa gaba dayansu Sai da ya kama kofar zai shiga ya juyo ya yafito Hafsat da hannunsa guda sannan ya juya ya shiga dakin Hafsat sai da gabanta ya yanke ya wani irin faduwa kafin ta daga kafarta da kyar ta kawar da dubanta daga hararan da Hasana ta gala mata ta juya ta shiga dakin itama A lokacin da ta shiga dakin yana zaune saman kujera ya janye jalabiyar nan sosai ta yi sama hakan ya bayanar da cinyoyinsa fili cike da gargasar gashi kwonce lufluf a jikinsa, hannunsa dauke da waya da kuma irin abin sauraron nan dake bada damar a ji inda mutun yake din nan Takunta ta kara