Sashe 73
Kutkale Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
mai girma a ransa, yana rokon Allah ya sa rashin jin maganarta shi ne iya jarabawar da zai yi masa da ita, Allah ya sa mijinta ya zauna lafia da ita, kar ya wulakanta masa mamansa Duban da mama ta yi masa ya bashi kwarin gwuiwa, dan haka ya rintse ido ya ci gaba da yi mata mata nasiha mai ratsa dukan gabai har ya saka ka yi sanyi tamkar ruwan sama ya dake ka Tun tana kuka muryarta na fita har ta kwontar da kanta a cinyar mamanta take gurnani gaba daya muryarta ta disashe ta daina fita Sai da aka fara kiraye kirayen salar farko ya saka shi mikewa bayan ya yi mata wata irin doguwar adu.a, ya yafe mata dukan abinda ta yi masa wanda ya sani da wanda bai sani ba, mahaifiyarta ma haka, sannan ya umarta da a kaita kowani daki ta nemi gafara, ya mike yana mai shaida masu Abdallahnma zai shigo nan da sati domin yana saudiya har yanzu bai gama ba Kamar a lokacin za.a tafi da ita gidanta, gaba daya mama ta kasa mikar da ita, a hankali muryarta na wata irin magana take furta" Abanna, ni ba zan je ko.ina ba, ni a barni a wajen Abanna, wayo Abanna Mama kam ta san za.a rina, shi kansa ta san fama ne yake ya gudu ya zubar da hawayen zai rabu da mamansa, murmushi ta yi ta cicibata da kyar ta kamata a jikinta ta fito daga dakin malan din ta nufi dakinta da ita, Suna shiga ta cire mata hijabin jikinta ta zaunar da ita, Wata dilkar ta zo ta shiga cude jikinta da ita, ba abinda ya dameta da irin kukan da take ta san za.a rina kuma dole ta yi hakuri ta je domin kowama da haka ya saba Sai da ta gama filketa ta shiga ta dauro alwallah Tana gama sallah har sai da rana ta fito ta tashi ta kamata daga saman salayar da take zaune ta kasa tashi ta dauketa ta kaita can kurya Ba.a jima ba aunty mariama ta zo Tana zuwa ta tube hijabin ta kawo garwashi ta mikar da Hafsat ta saka turare a cikin bokicin karfe ta sakata zama bisa Hafsat na zama ta ji yanda hayakin ke ratsa jikinta, a hankali ta lumshe idannuwanta sai wasu hawayen ke zubo mata, karo na biyu kennan, karo na biyu zata bar gidan mahaifinta ta je gidan wani ba da son ranta ba, eh lale ba da son ranta ba domin bata son sa kuma baya son ta Aunty ce ta kaleta ta ce" Maman malan, menene?? Idannuwanta da ta ci kuka da su har sukai mata hadari hadari bata iya daga su da kyau ta dago ta zuba mata, A hankali ta ce" Aunty *Ni BANA SON SA, KU SHIMA YA TSANE NI!* ido Auntyn ta tsura mata tana kallonta kafin ta mike ta bude humurar da ta zo da ita katuwar kwalba guda ta bude ta debo mai yawa ta zo kusa da ita a hankali ta ja zip din rigarta ta yi kasa da ita sosai ta shiga murza mata shi a hankali a wuyanta sannan ta daga hannayenta ta ce" du saurin ki, ki kasance cikin kanshi Maman malan, Ki ringa shafa turare a gurbi gurbi na jikin ki, kin ga daga kasan wuyan ki, bayan kunnen ki, hamatar ki, kasan maman ki, tsakakanin cinyoyin ki, cibiyar ki, du inda ya dace wannan humura ta zamo ita ce ta sirrin jikin ki kafin turaran wuta, Idan kina haka zaki kasance daban, bata da daci bale hakan ya damu abokin zaman ki, bata da karfi bale ta dame ki ko ta dame shi, Hannunta Hafsat ta rike ta shagwabe fuska sai ga hawaye ta ce" yanzu aunty kai ni zaku yi? Aunty yaya ina magana bama zaki kula ni ba?????? Comment zafafa ke saka ni rubutu bilahi *KUTKALE* *(PRISON)* NA *SAJIDA* Marubuciyar DUK KARYAR KADA YAR MAHAUKACIYA DAGA TAFIA DAUKAR SOJA NEMAN NA KAINA BANI DA ZABI IDAN KA RAINA INDA KAKE BAK'A CE INA KUKE MASOYAN NOVELS DINA, GANI NA DAWO DA SABON SALO, SABUWAR TAFIA, NA ZO MAKU DA SABON NVL DINA MAI TAKE *KUTKALE* WATO GIDAN PRISON, WANNAN NVL ZAI ZO MAKU DA LAMURA DA YAWA, KU BIYO NI KU SHA LABARI........ *WANNAN NOVEL NA SIYARWA NE, DU MAI SO ZAI IYA TURA KUDINSA TA wannan acct NAIRA DARI BIYU : Usman Muhammad 3072998062 First bank. Sai ya turo shaidar ya biya ta wannan number +22791466605....sannan a yi adding dinsa cikin grup, MUTANENA NA NIGER KUWA SANADIYAR RASHIN SAMUN ORANGE MONEY DA KUKE YI, KUNA IYA TURO HOTON KATIN SAHELCOM KO NA AIRTEL TA NUMBER KAMAR HAKA 91466605 SAI A SAKA KU A GRUP DIN, .....* taku ce, Sajida 5 Tsayar da abinda aunty take ta yi, sannan ta duka gaban Hafsat domin so take su yi ido cikin ido da ita Ai kuwa suka hada idon, hakan ya saka Hafsat dan kawar da dubanta a hankali Aunty ta yi murmushi tana girgiza kanta ta ce" kar ki damu maman malan, zaki so shin ne Hafsat ta zumburi bakinta gaba, ita kai ji take da ta je gidan Abdul a yau gwarama ta yi ta zama a gwauruwarta a yi ta yi mata gorin in dai zatana gannin mamanta da malan sai me? Daina kulata suka yi, kowa yake hidindimunsa na shirye shiryen kaurar da ita gidanta, domin yan uwanta mata baki daya kulewa suka yi a dakin mama suna ta kimtsa dukan abin kimtsawa Sai da magariba ta yi sannan aka samu fitowa da Amarya Abin mamaki ga kowa mama da kanta ke janye da Hafsat, wace ke cikin lulubi cikin farin abin rufa ba.a gannin komai nata, yan uwanta sun zagayeta kamshi kam sai rabawa take A hankali aka shiga dakin Hajia mama da ita, Suka da ita mama ta yi, cikin nutsuwa ta kalli hajia mama ta ce" mamanta, ta zo yin salama da neman gafara, a yafe mata zaman yau da kulun Hajia mama dake zaune da sauran matan a dakinta ana ta cicira maganar irin motocin da suka zo daukar Hafsat motar ba wasu masu yawa ba aman hameur biyar ce cif dukansu bakake wulik sai haska wajen suke, suna tsaka da tautaunawar aka shigo da hafsat din hakan ya saka suka bi su mama da kallo da mamaki Hajia mama ce ta tabe baki ta ce" a yafe Murmushi mama ta yi ta kama Hafsat ta mikar da ita daga tsugunnin da akai mata Kama hannunta ta yi suka juya har sun kusa fita amarya kasa kasa ta ce" ba girin girin din ba, ta yi mai, ai shi matsalar irin haka ba ridi ba daraja sai dai a je a dawo Aunty nana mariam ce ta ja ta tsaya, sai dai kallon da mama ta yi mata ya sakata juyawa suka fice a dakin Sai da suka zo kusan kofar gidan mama ta ja ta tsaya ta damka hannun Hafsat a cikin hannun Aunty , Da sauri ta juya domin raf Hafsat ta rike hannun taki saki sai da mama ta janye da karfi ta yi ciki tana jiyo irin yanda Hafsat ke kuka , ita kanta sai da ta labe ta yi hawaye kafin ta saku ta shiga sha.aninta tanaiwa yarta fatan alkhairi Su Aunty kansu sun yi adu.a da fatan alkhairi a irin gidan da Hafsat ta samu, sun yi fatan Allah ya sa mai hakuri da datako ne mijin , hakan zai sa su jima zaman nasu ya yi karko Tamkar zata suma a lokacin da zasu tafi su barta Sai dai aure ne, daga shi sai mutuwa su ke rabaka da iyayenka, da danginka , su canza maka muhali, yannayin rayuwa, Haka suka rabu da yar uwarsu bayan dogon jawabi da rarashi, Sun yi mamakin gannin ba wanda ya leko su ko ya aiko masu da sakon su ci kansu, sun kuwa lura da gidan akoy mutun domin fitila a kunne take kuma da dan hayaniya Suna tafiya ta nemi waje ta zauna kasa saman kafet dinta ta saka hannayenta bibiyu ta yi tagumi tana bin dakin da kallo Jin abin da gannin abin take a wai, wai ita ce matar Abdul? Mutumen da ta hadu da shi dan kawai ta zama bodyguard dinsa sai gata yau ta zo gidansa a matsayin katarsa? Rabonsa da ya yi mata wata maganar arziki tun da suka fita zuwa gidan dinki, Gaba dayansa ya canza mata tamkar ba shi ba, ba wata magana bale kulawa, wai yau ake kawota gidan miji ba danginsa ba wani nasa shi kansa baya nan bare har ta ji kanta tamkar amarya ko ta rufe fuskarta anai mata oyoyo ana zolayarta ana jan rufarta, Gata dai zaune a dakin da mahaifinta ya wani irin kashe kudi ya zuba mata kaya, kayan alatu, kayayaki masu kyau da gayu, an tafi an barta daga ita sai halinta! Rufar da ta aka lulubo mata ta yaye baki daya, Mikewa ta yi tana jin kanta har yanzu da zafi irin kitson nan da aka yaryara mata kananu har haka, kitson tamkar da alura aka yi su, sun yi cas sun cika sun yi tsayo sun kuma zanu Hannayenta ta bi da kallo, Ita kanta kunshin jan lalen hannunta na birgeta sosai Cire rufar ta yi baki daya ta nufi wajen kular abincin da aka kawota da shi Budawa ta yi hankali kwonce ta zauna ta ci abincinta, Kanta ta baiwa hakuri cewar zamanta da abdul ba wani zama bane dan ba zai iya da halayanta ba itama ba zata iya da wulakancinsa ba, dan haka kar ta wani saka damuwa a ranta ta tsamure ta lalace a wofi, zata koma kusa da iyayenta soon Sosai Hafsat ta saki jikinta ta saki ranta a tankamemen bangarenta , bata rasa ci, sha , sutura, kayan kwalam da makulashe, bata rasa abin kallo ba, ga Ac da take sha kowani lokaci, Sangartarta take zubawa da barna kala kala, Takan hada fruits ta markade ta juye peak da kananfari da dabino ta zauna ta yi ta sha abinta Karshema da yawa ta yi ta saka a frij ya zama ruwanta, koda yaushe zata didika ta je ta mike abinta Karshen neman magana