Sashe 56
Kutkale Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
ringa yi ke dawo masa a idannuwansa, Sai da ya kalli BS dake kokarin tayar da mota dan bin bayan su Abdul sannan shima ya buda motar da shiga wace ke dauke da gagan sojoji wa.inda ba alamar sun taba sannin wani abu mai sunna dariya a rayuwarsu sannan ya gyada kai a ransa ya ayyana........shara.ar Muhammad ya dace a barwa Allah, bai ga hukuncin da za.a yiwa wannan bawa a nan cikin duniya ba, bai ga irin abinda za.a iya yiwa wannan bawa ba a huce ko a rama irin abubuwan da ya shuka, tabas zasu tura shi kasarsa a hukuntashi a can, ya tabata kisa ne ta hanya mafi muni ya je can kuma ya fuskanci wanda ya halice shi! A asibiti kuwa tun a hanya BS ya samu ya kirayi number Malan, domin tun ranar da Abdul ya je BS ya gane akoy fahimta tsakanin datijon da Abdul, a irin yanda Abdul ya zame kasa ya duka ya gaishe shi wanda hakan shi ne gannin farko da ya yi ya mutunta mutun Bayanin da ya yiwa malan ya saka shi jin zufa ta keto masa, cikin nutsuwa ya nuna masa cewa da zai samu jirgi a lokacin tabas da ya zo da kansa domin kuwa dole Abdul na bukatar mutun a kusa da shi BS na jin haka ya ce da shi ya kasance cikin shiri koda yaushe ana iya zuwa daukansa in sha Allah za.a kawo shi BS ma karasawa ya tarar likitoci na kan Abdul , famansu shi ne su dawo da numfashinsa da bugawar zuciyarsa daidai, Hafsat kuwa na zaune saman kujera an saka mata magana a fuskarta an gyara mata an yi an yi ta kwonta ta huta aman ta kasa tana zaune ta saka wata riga baka mai dogon hannu aman bata canza wandon jikinta ba ta faure kanta da dan kwali baki ta yi zuru da ita tana kallon waje daya, a kasan zuciyarta kuwa sai adu.a take kan Allah ya sa ya yi hakuri ya dauki komai da sauki Sun dauki kusan awa kafin a fitar da shi a kai shi dakin hutu sai a lokacin ta mike ta koma dakin da ya dace a kwontar da ita ta shiga bayi ta yi wani irin wanka sannan ta fito ta dauki wani wandon da rigar baka da hijab da Hasana ta kawo mata ta saka ta kabarta sallah a nitse Ta jima tana ramuwar salolin dake kanta, ta dauki lokaci tana sallah kafin ta salamce ta shiga adu.a da godiya ga Allah Jaka kawai ta tsinci kanta da yi masa adu.a mai nauyin gaske, ta jima tana rokon Allah ya taimaketa ya ji kanta duda baya barin wani dan wani ya ji dadi ita kam bata tunanin zata ci gaba da walwala idan bai mike ya samu kansa ba Tana ta jero adu.o.in ta ji wata kamilaliyar murya, nitsatsiyar murya, muryar da ta kasance mai yi mata nasiha da lalaba ta, muryar dake tsananin girmamata ta hanyar kiranta *UWATA* muryar da ta kasance daya daga cikin adu.o.inta na Allah ya nuna mata ranar da zata kara jin muryar a duniya Kasa kunne ta yi tana mai jin zuciyarya na bugawa a lokacin da ta ji BS ya yi magana sai kuma ta ji muryar ta ce" Allahu ya tashi kafadar bawan Allah, ya bashi lada da juriyar wannan jarabawa, domin Abdallah mutumen kirki ne Wata irin mikewa ta yi ta doshi kofar, sai dai me, Hasana ce ta riko hannunta da karfin gaske ta ce" ki koma ki zauna H, kar ki jazawa kanki kin san kina cikin mission ne Wani kallo ta yiwa hannunta da ta riketa da shi sannan ta ce" ki cika ni Hasana ta saketa ta ce" zaki lalata aikin ne Hafsat bata ce da ita komai ba ta buda dakin da saurin gaske ta fita Tsayuwa ta yi ta shaki kamshin turaransa, bai canza shi ba shi dai ne har yanzu, Da sauri ta shiga raraba ido tana neman inda zata gan shi, ina zata ga hasken idanniyarta, Kyalkyalin tazbaha da ta gani a daidai kofar dakin da aka saka Abdul ya sakata nufar wajen har tana hardewa , muryarta ta buda ta ce" *ABANA* Da sauri ya saki kofar da ya buda da jiyar shiga domin likita ya ce ana iya shiga Abdul ya farka ya juyo inda ya ji muryar Ita ce tsaye gabansa A hankali ya furta" Alhamdulilah.... *UWATA* AI kuwa Hafsat ta fashe da kuka sannan ta arta a guje , tana zuwa ba wata wata ta fada jikin mahaifinta ta kankame hannunsa tana wani irin kuka , bata wani damu da tunawa ya hana su fadawa jikinsa ba, ko jikin wani namijin haka kawai ba, shi kansa sai da ya ji kwala ta cika idannuwansa sannan ya yi mamakin yanda mamansa ta girma a dan lokacin nan fuskarta ta nuna alamun ta nutsu. A hankali ya cirata a jikinsa yana kallonta ya ce" ya isa haka ko Uwata? Tana haki da komai ta ce" Aba, ba guduwa na yi ba Abana, Abana ka min auren da du wanda ka zaba min na maka alkawarin da zauna da shi koda kuwa yankan naman jikina yake, Abana ka yafe min, ina mamana? Abana ka san inda aka kai ni? Ka san me aka min? Abana gidan yarin *KUTKALE* aka kai ni a matsayin wace ta yi laifi na zama budurwar dan ta.ada, Abana daga nan aka kai ni ..... *UWATA* ya fada cikin nutsuwa yana kallonta, nunsa ya saka ya share hawayenta sannan ya ce" Abdallah ya je ya fada min, Shiru ta yi tana kallonsa, sai a lokacin mamaki ya kamata na jin wai Abdallah ya je wajen mahaifinya ya fada masa wannan maganar, Ikon Allah, sai yanzu tunanin me ya zo yi asibitin ya dirar mata, Dubanta ta kai cikin dakin marar lafiar nan ta hango Abdul kuri su yake kallo Gabanta ne ta ji ya yanke ya fadi lokaci daya kuma ta damki hannun mahaifinta a hankali ta ce" Abana, ya farka Malan ya kai dubansa wajen Abdul din, ya ga gaba daya hankalinsa a kansu dan haka ya ja hannunta da niyar shiga da ita, sai dai ga mamakinsa hannun ne ya fara rawa ta kasa motsawa harma ta iya furta cewa" Aba Tsayawa ya kuma yi da mamaki ya kalli yannayinta, a hankali ya cika hannun nata sannan ya juya ya shiga dakin , sai dai ya kasa rufe kofar dan du ji yake idan ya rufe ba zai bude ya kuma ganninta a wajen ba BS ne ya zo ya yi mata magana fuskarsa a tamke hakan ya sakata bin bayansa suka je suka tsaya nesa da dakin, bai ce da ita komai ba sai dai shirun da ya yi shima yana kallon waje daya kamar yanda ya ga hankalinta ya raja.a dakin da mahaifinta da kuma Abdul ke ciki Tun da malan ya shiga ya nemi waje ya zauna, ba abinda yake karantawa Abdul sai girman hakuri mahinmancinsa da sakamakon da ake samu mai kyau idan an yi shi, Jarabawar da ya shiga mai girma da duhu ya ringa bashi baki da musalai da kuma ribar da zai samu idan ya yi hakuri da ita a hakan, Shiru ya yi yana kallon yanda Abdul ke kallon kasa bai ce da shi komai ba Ci gaba ya yi da bashi baki, da nuna masa kar ya dauki maganar cewa zai dauki fansa shima, hakan ba zai kai shi ga ci ba, ba zai samu wata nasara ba Abdul ya dago idannuwansa da suka yi jajajir da mugun nauyin da sukai masa ya sauke a kan malan Sai da ya hadiyi yawu mai daci da kuma yauki a hankali ya ce" ba komai *ABA, ALLAH YA JIKAN DU WA.INDA SUKA MUTU* Sai da ya ji zuciyarsa ta girgiza, ba komai fa yace? Tabas yana iya karbar abin aman ba komai din na lokaci daya ya bashi mamaki, ko dan yana cikin hali na rashin dadin yannayi shi sai ya ce kamar yau baya cikin yan magana ma, Ajiyar zuciya ya sauke ya mike da niyar fita, sai dai muryar Abdul ta dawo da shi cewa" Aba, Dama amini na zama makiyi? Aba dama alkhairi na jazawa mutun kiyaya? Aba, shin a gabanan zan iya yarda da wani dan adam komai kusancina da shi kuwa? Aba ashe aminina ya kashe min kanwata? Ya kashe min mahaifiyata? Ya kashe mutanen dake tare da ni? Du dan ya kai ni ga ciwon hauka kafin na bar duniya? Aba........zuciyata sai nake jin tamkar ba zata kuma gannin haske ba, ji nake tamkar na gama da farin ciki, idannuwana na gannin kowa da fuska biyu, *ABA, shin me zai saka na yarda da kai kanka?* Halin rudani na rudar da zukatanmu a likacin da wani lamari ya dake mu , sauki na Allah ne *KUTKALE* *(PRISON)* NA *SAJIDA* Marubuciyar DUK KARYAR KADA YAR MAHAUKACIYA DAGA TAFIA DAUKAR SOJA NEMAN NA KAINA BANI DA ZABI IDAN KA RAINA INDA KAKE BAK'A CE INA KUKE MASOYAN NOVELS DINA, GANI NA DAWO DA SABON SALO, SABUWAR TAFIA, NA ZO MAKU DA SABON NVL DINA MAI TAKE *KUTKALE* WATO GIDAN PRISON, WANNAN NVL ZAI ZO MAKU DA LAMURA DA YAWA, KU BIYO NI KU SHA LABARI........ *WANNAN NOVEL NA SIYARWA NE, DU MAI SO ZAI IYA TURA KUDINSA TA wannan acct NAIRA DARI BIYU : Usman Muhammad 3072998062 First bank. Sai ya turo shaidar ya biya ta wannan number +22791466605....sannan a yi adding dinsa cikin grup, MUTANENA NA NIGER KUWA SANADIYAR RASHIN SAMUN ORANGE MONEY DA KUKE YI, KUNA IYA TURO HOTON KATIN SAHELCOM KO NA AIRTEL TA NUMBER KAMAR HAKA 91466605 SAI A SAKA KU A GRUP DIN, .....* taku ce, Sajida 4 Sai da ta yiwa kanta fada kan irin rikicewar da ta yi dan kawai ya rubuto mata haka sannan ta rubuta" *NI KUWA, BANA JIN KEWAR KA* murmushi ya saki , sannan ya ki bata amsa ya dai kurawa magangannun su ido yana kallo haka kuma Na.ima dake gefensa tana kallonsa bata dai san me yake yi a waya ba, aman kuma ta ga ya bada hankalinsa sosai hasalima bai san ta farka daga bacin gajiyar da ya tara mata ba Hafsat