Sashe 27
Kutkale Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
zafi sannan ta yi tsaye a gabansa wanda yannayin kyakyawar fuskarta da ya nuna hadewa sam ba alamar annuri ya saka shi jin gabansa ya fadi, Abdul dake zaune a hankali ya bi hannun Hafsat da ta saka ta mayar da Murtala zaune da kallo, Wandon dake jikinta ne ya kuma bi da kallo , ya dameta sai dai na roba ne hakan ya saka take motsawa son ranta aman du wata halita mai rawa ko mai motsi a wajen tana iya mitsawa in dai Hafsat din ta motsa, Sannan rigar dake jikinta mai siririn hannaye ce, dan kuwa tun harbin da akai mata ta daina saka mai dogon hannu ko fita zasu yi dan hannun ya warke kar ya danyace Rigar ta yi mata caras a jikinta, kanta da dan karamin dan kwali baki sidik wanda ta yane kan da shi, fuskarta ba ko digon kwali aman lebenta haka yake jan idon wanda ya kale shi dan tamkar ta goga masa jan baki ne Lebensa ya hade gaba daya sannan ya tabe bakinsa yana kallonta, irin tsayuwar da ta yi a kan Murtala, Kansa ya girgiza sannan ya mike tsaye, Hannunsa ya saka ya mayar da ita gefe hakan ya saka ta zama yar tsuwat a gefensa tana huci dan neman fadan dama take Abdul sai da ya daura agogon hannunsa da kyau sannan ba zato ba zamani ya saka hannunsa na dama ya dago wuyan Murtala ya ja shi ta wajen kujerar hakan ya saka wandon dake rige da kugunsa janyewa dan kuwa arzunzumi ne harka da yan gayu bai wani daure shi da kyau ba, Kiiii ya ja shi sai da ya dangana shi da bangon dakin sannan ya saka dayan hannun nasa ya daga shi gaba daya ya raba shi da dandar kasa ya rike masa wuya sosai yana dubanda ido cikin ido ya ce" yaushe na zama bolar da har zaka daga muryarka a kan tawa? Bayan karya da cin amanar har raini zai shiga tsakanina da kai? Ka manta a gidan iskancin da na hadu da kai a irin halin da kuka hadu? Ko dan kana tunanin kai lauya ne sannan ka girme ni zaka raina ni? Murtala dake harhaba kafafuwansa dan neman a sake shi, du idannuwansa sun ruruko yana ta kokarin yin magana a hakan ko zai sake shi sai rike hannayensa yake aman Abdul ya kasa sakinsa sai kara matsar masa wuya yake Da sauri Hafsat ta matso ta tsaya ta ce" Abdul, ka sake shi, kar ka kashe shi Abdul Idan ya kulata to lale dakin ya amsata, Gannin yana neman yin kisa ya sakata dan kokari matsawa ta saka hannayenta dan kwaljwace wuyan Murtalan a hannun Abdul Hannayen nata ya yarfe da hannunsa na hagu, bai saki murtalan ba ya hankadata da hannun nasa hakan ya saka ta yi tagal tagal ta hadu da kujerar wajen ta ja ta tsaya tana sauke ajiyar zuciya kafin ta tsinci muryarsa a kausashe ya ce" *Ke, bilahilazi kika yarda kika kara taba wannan jemagen sai na karya maki wuya!* Yana gama fadi ya sake shi nan ya fadi yana kakarin tari , shi kuwa ya duka ya lalubi wayoyinsa ya juya da su ya fice ya nufi dakinsa ya rarumi computernsa ya zauna ya jona wayar ya shiga aiki yana mai jin shi bashi da abinda zai iya yiwa wannan mutumen ya huce sai dai idan zai kwakule masa idannu ne ya soye ya huta! Hafsat kam sai da ta sha jinnin jikinta a lokacin da ta ga ya nufo kamar ita zai damka , sai kuma ta ga ya fice a dakin, Ajiyar zuciya ta sauke a fili ta zabgawa hanyar harara a ranta kuwa ta ce" dama na bari ya hayeka a mikewar da ya yi dazun, ni na ga jaraba! Malan ana kare ka kana hana mutun aikinsa! Juyawa ta yi ta fice a dakin ba tare da ta kuma bi ta kan Murtala dake yashe a nan ba ta fice gaba dayanta ta zagaya wajen sojojin dake gadin bayan gidan ta samu daya ta amshi aron mashin dinsa ta haye ta harba titi Gudu take tamkar ba zata karasa inda ta nufa ba, A haka man mashin dinta ya kare ta tsaya ta zuba harma ta yi guzurin wani, sannan ta dauki wayar da ta gama bincike ta kare a sunnan wani gagarumin malamin islamiya dake raye a kauyen garin Minna din, wanda ke rayuwa daga shi sai almajiransa, aman kuma mutumen har ya iya hawa social media, ba komai ya ja hanlalinta yau tsayun kwana biyar a kansa ba sai sunnansa, Sunnansa *Muhammad bine Abdul Basid Abdallah* Ta zama wata irin mutun ce mai kurmuwa dukan wani abinda zai bata damar samun gaskiyar abinda ke boye a tatare da Abdul, ba ruwanta da me zata tarar? Waye shi mutumen? Burinta ya kasance shi ne! A lokacin da ta shiga cikin jejin, a bakin wata rijiya ta ga mutun zaune yana rubutun allo, Babur din ta tsayar tana son saka jak ta ajiye mashin din mutumen ya dago da kansa daga saman allon karfen da yake rubutu samansa A tare gabansu ya yanke ya fadi, a wannan lokacin a wannan wajen ya mike ya durfafa cikin jejin wanda kafin hafsat ta sauka a mashin din tuni ya bace mata bat ta nema ta laluba kamar ta yi hauka ba shi ba alamarsa Wajen allon ta je ta tsugunna ta dauki allon da tawadar, Yatsarta ta saka ta lashi tadawar, ta daga idannuwanta ta kai wajen rijiyar, Ba komai ake rubutawa a jikin allon ba sai astagafari, Mutumen ba wani yaro ba aman irin yanda lokaci daya ya bace mata ya tsoratar da ita *Wannan mutumen shi ne ya damki hannunta a wajen daurin auren dan minister da yar Elhaj,* Ta shiga rudu, waye shi? Ko shi ne mai wannan sunna? Me ya sa a page din da yake yawan rubutu baya saka komai sai jawabi da gargadi a kan zina? gashi dare na kokarin yi mata a jejin da ta daina gannin ko wulgawar tsuntsu ne bare na mutun. Zuciyarta na son gaskata mata hasashenta, runguntsumin tashin hankalin Abdul na ture komai, Idan haka ta kasance ina zai shiga da ransa? *Wai wa ke neman ranka Ya Abdel?* hafsat ta mike ta kuga haka wanda gaba daya sai da wajen ya amsa da amon muryarta ...... Allon nan ta dauke ta juya wajen mashin din tana kokarin hawa ta tayar ta hang........... *KUTKALE* *(PRISON)* NA *SAJIDA* Marubuciyar DUK KARYAR KADA YAR MAHAUKACIYA DAGA TAFIA DAUKAR SOJA NEMAN NA KAINA BANI DA ZABI IDAN KA RAINA INDA KAKE BAK'A CE INA KUKE MASOYAN NOVELS DINA, GANI NA DAWO DA SABON SALO, SABUWAR TAFIA, NA ZO MAKU DA SABON NVL DINA MAI TAKE *KUTKALE* WATO GIDAN PRISON, WANNAN NVL ZAI ZO MAKU DA LAMURA DA YAWA, KU BIYO NI KU SHA LABARI........ *WANNAN NOVEL NA SIYARWA NE, DU MAI SO ZAI IYA TURA KUDINSA TA wannan acct NAIRA DARI BIYU : Usman Muhammad 3072998062 First bank. Sai ya turo shaidar ya biya ta wannan number +22791466605....sannan a yi adding dinsa cikin grup, MUTANENA NA NIGER KUWA SANADIYAR RASHIN SAMUN ORANGE MONEY DA KUKE YI, KUNA IYA TURO HOTON KATIN SAHELCOM KO NA AIRTEL TA NUMBER KAMAR HAKA 91466605 SAI A SAKA KU A GRUP DIN, .....* taku ce, Sajida 2 Tana kokarin tayar da mashin din ta hango wani irin mutun, Mutun ne zabaya namiji kuma wada , Kai ba dan ba dan ba sai tace ko ta yi gamo ne? Dan kuwa mutumen tsayawa ya yi yana kallonta kamar ya ga bakuwar halita Adu.a ta yi sosai ta tofa masa yana kallonta tana kallonsa, Gannin ya ki motsawa ya kuma kin yi mata magana ya sakata saukowa a hankali ta nufe shi inda gabanta ke luguden kida Tsayawa ta yi dan nesa da shi ta yi salama, Ga mamakinta sai ta ga ya matso kusa da ita sosai Sai da ya daga kansa ya kaleta domin ya matso kusa da ita kafin cikin muryarsa dake nuni da manyantakarsa ya ce" ke kuwa, kin ari musulunci ne ko musulmar ce ke? Kanta ta sada dan kallonsa da kyau itama kafin ta ce" kama gare su ne musulmai ko salamana ne bai cika ba? Kansa ya gyada kafin ya juya da niyar tafiyarsa , Gane hakan da ta yi ya sakata matsawa da sauri ta ce" dan Allah, ka taimake ni, ina son sannin waye Muhammad bine Abdul Basid Abdallah? Ko zaka iya kai ni inda yake? Sai da ya kare mata kallo sannan ya ce" ki je dare ya yi, ki dawo zan kai ki wajensa, aman yanzu akoy nisa ga kuma dare Ta so ta yi magiya ko zai saurareta, sai dai gannin bashi da niyar hakan ya saka ta juyawa ta hau mashin din ta tayar ta dauki hanya wanda a lokacin tuni isha ta kawo kai, a kadan zata iya kaiwa awa uku ko zata isa Gudu kawai take yi, gashi a lokacin da zata bar gidan Abdul sai da ta ajiye du wani abin aikinta da zai bada damar a san inda ta nufa, ta tabata yanzu an farga da bata nan, fatanta kar ta kai BS bango ya dauki mataki a kanta ya kawar da wani gudun bacin ranta ya saba mata! Ta jima, ba karamar wahala ta sha a hanyar ba kafin ta karasa anguwar, a haka har ta karasa kofar gidan Tun daga irin kallon da sojojin ke binta da shi ta dan sha Jinnin jikinta, sai dai bata saka komai a ranta ba ta samu ta shigar da mashin din ta karamar kofar sannan ta sauka ta shiga tura shi ta ci uwar tafia kafin ta karasa farfajiyar gidan Dare ne, aman ko.ina ya dauka da hasken fitila , hakan ya saka du wani mai motsi ana iya ganninsa da dukan abinda ke tare da shi Tun da ta shigo gabanta ya yanke ya fadi, dan kuwa du wani bodyguard da ya kwana ya tashi a gidan yana tsaye cirko cirko , BS sai doka waya yake haka kuma sai duba agogo yake, gefe kuwa Abdul ne tsaye hannayensa cikin aljihun wandonsa ya zubawa hanyar da ta fito ido Turus ta yi