Sashe 58
Kutkale Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
sannan ta juya ta je wajen biyan ta ciro kudin a pos dinta ta mika ta tsaya tana jira mai gidan nasu ya bata canjinya ta juya abinta Canjin ya taso sa kansa ya miko mata yana kallonta, da yannayin gimshewa ya miko mata makekiyar wayarsa ba tare da ya yi wani dogon magana ba ya ce" No Wayar ta kala, sannan ta bi hannayen nasa da kallo masu dauke da gashin jiki sosai kalar fatarsa dan ba bakake bane gashin a haka har ta kai fuskarsa dake dauke da dan karanmin saje dan siriri Sai da ta wana idannuwanta tana kallon yanda yake wani tsarewa yana wani kamewa abinsa A hankali ta yarfe shi da idannuwan nata da suka dauki bakin kwali suka kara fitowa radau da su sannan ta buda labanta cikin wani yannayi na shegantakar da ta koya wajen Abdul a wani irin hankali ta ce" *Baka da saje da gemu* Tana gama fada ta karbi jakar kayan ta juta da canjinta tana sakawa cikin pos dinta Idannuwansa ya firfitar da matsanancin mamaki sannan ya kali madubin wajen da ya zagaye ko.ina, Na farko a rayuwarsa an fizga shi, wai bashi da saje, saje kuma a me? Ina ba zai barta ta tafi haka ba bayan ta zama ta farko da ta ki shi fan saje Juyawa ya yi wajen yaran nasa ya ga du sun kawar da dubansu a kansa wato suna kallon du abinda ya faru? Juyawa ya yi ya shiga bin bayanta a hankali jar suka fito bakin inda zata dauki taxi Shi dai bai gane taxi ne zata dauka ba sai da ya ga ta tsayar da daya yace ba can ya nufa ba mamaki ya kara kashe shi, Bama ta da motar kanta? Aman ta iya dizga namiji kamarsa? Ko dai dan ya biyota ne? Aa, ko dai tana da aure? Ko kuma mata take so? Shi daya ya yiwa kansa tambayoyin da sun kai biyar aman ba amsa dan haka yake tsaye yana magana ko zata saurare shi har ta amsa kiran wayar da ajau ta yi mata inda ta fadi sunnan Boutik din fa take sannan ta ci gaba da neman taxi domin lokacin saukar aikin yama ya yi taxi na wahala sosai bare anguwar yan gayu taxi na wahala sosai....... *KUTKALE* *(PRISON)* NA *SAJIDA* Marubuciyar DUK KARYAR KADA YAR MAHAUKACIYA DAGA TAFIA DAUKAR SOJA NEMAN NA KAINA BANI DA ZABI IDAN KA RAINA INDA KAKE BAK'A CE INA KUKE MASOYAN NOVELS DINA, GANI NA DAWO DA SABON SALO, SABUWAR TAFIA, NA ZO MAKU DA SABON NVL DINA MAI TAKE *KUTKALE* WATO GIDAN PRISON, WANNAN NVL ZAI ZO MAKU DA LAMURA DA YAWA, KU BIYO NI KU SHA LABARI........ *WANNAN NOVEL NA SIYARWA NE, DU MAI SO ZAI IYA TURA KUDINSA TA wannan acct NAIRA DARI BIYU : Usman Muhammad 3072998062 First bank. Sai ya turo shaidar ya biya ta wannan number +22791466605....sannan a yi adding dinsa cikin grup, MUTANENA NA NIGER KUWA SANADIYAR RASHIN SAMUN ORANGE MONEY DA KUKE YI, KUNA IYA TURO HOTON KATIN SAHELCOM KO NA AIRTEL TA NUMBER KAMAR HAKA 91466605 SAI A SAKA KU A GRUP DIN, .....* taku ce, Sajida 4 Cikin yannayin rashin tsoro da kyama take duban keayar idannuwan Muhammad dake dan langi sakamakon kwayoyin da ya hadiya ta shiga mayar da zancen duka kaf da ta gano wajen bincikenta, da irin sato tan da suka yi shi da sojansa mai bashi goyon baya, da komai da komai Sai da ta ja numfashi ta kai dubanta wajen BS da har jikinda bari yake tsabar firgita da ikon Allahn nan, ya ga lamari da yawa, ya ga gaba da yawa, aman bai taba gannin ci amana irin wannan ba Idannuwanta cike da hawaye ta ce" wannan da kake gani, wanda ba zan iya kiransa da madaukakin sunna irin MUHAMMAD ba, domin ya kasance azalumi, mai izgili da rashin tsoron Allah, wannan aljanin mutumen wanda ban ga sunnan da ya dace da shi a musulunce ba! Ta kuma rinyse idannuwanta sannan ta ce" *shi ne mai kashe kashen nan baki daya ban cire maka ko daya ba, kuma yana yi ne dan vengeance* Sai da BS ya dafe gaban kirjinsa dan luguden kidan da yake masa, Dubansa ya kai wajen algungumin a daidai lokacin da ya daga hannunsa ya nuna Hafsat ya ce" karya ne! Gindin bindigarsa ya saka ya daki keyarsa hakan ya katse masa fitsarar da ya dauko a bakinsa ya silale wajen a sume Da kallo ya bi shi sannan ya bada umarnin a nufi asibiti da Abdul da Hafsat Shi kuwa ya dadaure Muhammad dauri irin na huhun goro sannan ya shiga bincike da harhada du abubuwan da zasu isa cikaken shaida haka kuma ya tabo ikon garin wa.inda bai isa ya aiwatarwa da Muhammad wani abu ba sai abinda aka yanke masa a kotu A lokacin da aka saka masa ankwa bayan sun dankara masa wata gigitaciyar allura mai taba kwakwaluwa aminin Abdul mai sunna Ahmad ya yi tsai yana kallon motar da aka shigar da shi baima san inda kansa yake ba, Tabas shima ya girgiza, sai dai da wuri ya kwabi kansa a lokacin da ya tuna cewa Muhammad fa mutun ne, dan adam ba, dukan abubuwan da ya ringa yi ke dawo masa a idannuwansa, Sai da ya kalli BS dake kokarin tayar da mota dan bin bayan su Abdul sannan shima ya buda motar da shiga wace ke dauke da gagan sojoji wa.inda ba alamar sun taba sannin wani abu mai sunna dariya a rayuwarsu sannan ya gyada kai a ransa ya ayyana........shara.ar Muhammad ya dace a barwa Allah, bai ga hukuncin da za.a yiwa wannan bawa a nan cikin duniya ba, bai ga irin abinda za.a iya yiwa wannan bawa ba a huce ko a rama irin abubuwan da ya shuka, tabas zasu tura shi kasarsa a hukuntashi a can, ya tabata kisa ne ta hanya mafi muni ya je can kuma ya fuskanci wanda ya halice shi! A asibiti kuwa tun a hanya BS ya samu ya kirayi number Malan, domin tun ranar da Abdul ya je BS ya gane akoy fahimta tsakanin datijon da Abdul, a irin yanda Abdul ya zame kasa ya duka ya gaishe shi wanda hakan shi ne gannin farko da ya yi ya mutunta mutun Bayanin da ya yiwa malan ya saka shi jin zufa ta keto masa, cikin nutsuwa ya nuna masa cewa da zai samu jirgi a lokacin tabas da ya zo da kansa domin kuwa dole Abdul na bukatar mutun a kusa da shi BS na jin haka ya ce da shi ya kasance cikin shiri koda yaushe ana iya zuwa daukansa in sha Allah za.a kawo shi BS ma karasawa ya tarar likitoci na kan Abdul , famansu shi ne su dawo da numfashinsa da bugawar zuciyarsa daidai, Hafsat kuwa na zaune saman kujera an saka mata magana a fuskarta an gyara mata an yi an yi ta kwonta ta huta aman ta kasa tana zaune ta saka wata riga baka mai dogon hannu aman bata canza wandon jikinta ba ta faure kanta da dan kwali baki ta yi zuru da ita tana kallon waje daya, a kasan zuciyarta kuwa sai adu.a take kan Allah ya sa ya yi hakuri ya dauki komai da sauki Sun dauki kusan awa kafin a fitar da shi a kai shi dakin hutu sai a lokacin ta mike ta koma dakin da ya dace a kwontar da ita ta shiga bayi ta yi wani irin wanka sannan ta fito ta dauki wani wandon da rigar baka da hijab da Hasana ta kawo mata ta saka ta kabarta sallah a nitse Ta jima tana ramuwar salolin dake kanta, ta dauki lokaci tana sallah kafin ta salamce ta shiga adu.a da godiya ga Allah Jaka kawai ta tsinci kanta da yi masa adu.a mai nauyin gaske, ta jima tana rokon Allah ya taimaketa ya ji kanta duda baya barin wani dan wani ya ji dadi ita kam bata tunanin zata ci gaba da walwala idan bai mike ya samu kansa ba Tana ta jero adu.o.in ta ji wata kamilaliyar murya, nitsatsiyar murya, muryar da ta kasance mai yi mata nasiha da lalaba ta, muryar dake tsananin girmamata ta hanyar kiranta *UWATA* muryar da ta kasance daya daga cikin adu.o.inta na Allah ya nuna mata ranar da zata kara jin muryar a duniya Kasa kunne ta yi tana mai jin zuciyarya na bugawa a lokacin da ta ji BS ya yi magana sai kuma ta ji muryar ta ce" Allahu ya tashi kafadar bawan Allah, ya bashi lada da juriyar wannan jarabawa, domin Abdallah mutumen kirki ne Wata irin mikewa ta yi ta doshi kofar, sai dai me, Hasana ce ta riko hannunta da karfin gaske ta ce" ki koma ki zauna H, kar ki jazawa kanki kin san kina cikin mission ne Wani kallo ta yiwa hannunta da ta riketa da shi sannan ta ce" ki cika ni Hasana ta saketa ta ce" zaki lalata aikin ne Hafsat bata ce da ita komai ba ta buda dakin da saurin gaske ta fita Tsayuwa ta yi ta shaki kamshin turaransa, bai canza shi ba shi dai ne har yanzu, Da sauri ta shiga raraba ido tana neman inda zata gan shi, ina zata ga hasken idanniyarta, Kyalkyalin tazbaha da ta gani a daidai kofar dakin da aka saka Abdul ya sakata nufar wajen har tana hardewa , muryarta ta buda ta ce" *ABANA* Da sauri ya saki kofar da ya buda da jiyar shiga domin likita ya ce ana iya shiga Abdul ya farka ya juyo inda ya ji muryar Ita ce tsaye gabansa A hankali ya furta" Alhamdulilah.... *UWATA* AI kuwa Hafsat ta fashe da kuka sannan ta arta a guje , tana zuwa ba wata wata ta fada jikin mahaifinta ta kankame hannunsa tana wani irin kuka , bata wani damu da tunawa ya hana su fadawa jikinsa ba, ko jikin wani namijin haka kawai ba, shi kansa sai da ya ji kwala ta cika idannuwansa sannan ya yi mamakin yanda mamansa ta girma a dan lokacin nan fuskarta ta nuna alamun ta nutsu. A hankali ya cirata a jikinsa yana kallonta ya ce" ya isa haka ko Uwata?