Sashe 32
Kutkale Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
ya aka yi kika tsori yafa dan kwali kamar wace akai maki aure? Ko a summar da na yi kafin na dawo akai maki aure? Du abinda yake fada tana jinsa, tana kuma biye da dukan kalmominsa, aman yannayin da ta nuna sai ka rantse da Allah da ba da ita ake ba, koma bata jin yaren da ake yi, Kansa ya gyada ya ci gaba da fadin" kin san rayuwa ashe abu ce mai mahinmanci? Hafsat Malan ina son na rayu mai dan tsayi, kin ga na yi aure aure du na masu ciki abina! Ikon Allah, shi ne abinda ta fada a ranta, ashe dai bai yi sauki ba? Ta kara fada aman kuma bata nuna da ta san yanai ba koda kuwa ta gane ya kama sunnanta da na malan ne dan ta kula magangannunsa Abdul dake lure da ita ya ci gaba da fadin" ashe dai kauriyata banda zama kauriya harda magannin karya sihiri ta samu? To dan kwatanta min sak fuskar macecin nawa mana? Sai a lokacin Hafsat ta juyo da dubanta ta dube shi da kyau, sak fuskar tata tamkar ta balarabiyar dan kwalin da ta yane kanta da shi yay mata das masha Allah Yaren da bata taba yi ya ji ba, wace sai da ya mike zaune da ta fara dan walahi shi baima yarda da ba yarenta bane wai koya ta yi, wato larabci wace ta saka hasana juyowa itama da mamaki tana kallonta harda sakin baki, inda hafsat ta gyara tsayuwarta da harshen larabci ta ce" *Rayuwa, lumfashi, shakar iska zan iya ce maka mun fi jin dadinsu da komai, to ai dole ne Abdul, mutun ba zai san darajarsu ba sai a lokacin da ciwo ko wani abin ya tunkaro shi, yah Abdul* Bata damu da irin kallon da suke mata ba ta juyar da kanta, gefe ta kara rage muryarta ta ce " *Abdullah* Hannayensa ya dora gaba daya ya rungume a kirjinsa yana dubanta yana kuma sauraronta, Hafsat ta numfasa ta juyo wannan karron ta saka idannuwanta cikin nasa ta dan rage tsayinta tamkar zata afka saman kujerar da yake zaune ta ce" *Abdel* Idannuwansa ya lumshe daga kallon cikin idannuwanta yana tunanin me take son fada da mahinmanci haka? Sai sunnayen da ta kiraye shi da su, wato Abdullah, da kuma Abdel Katse shi ta yi da fadin" *bayan tafiarta bayan korar ta da kakanin ka suka yi, ta yaya ka samu labarin ta haihu? Menene tabacinka na namiji ta haifa? Wanda yake yayanka ko yayarka, shin zumunci kake yi da su ko taimaka masu kake da wani abin? Ka san inda suke a duniya? Ko baka taba nemansu ba? Suna da bukata ko sun fi karfin hakan? Abdel........ina suke?* Sai da Abdul ya zauna da kyau saman kujerar da a da kwonce yake yana dubanta, Idan ya gane tana son sannin wani abu dangance da labarin da ya bata na rayuwarsa cewar yana da dan uwa ko? Aman me ya sa? Menene dalilinta? Ya jima da zama, tamkarma ba zai amsata ba, ya kai dubanda wajen su BS dake shawahi sunna aikinsu, ya kuma duban bakuwar Bodyguard dinsa mai nacin kallo wato Hasana da ta yi kuri so take dole sai ta gane me suke fada ko meye? Kafin ya maida dubansa wajen Hafsat da ta yi shiru tana kallonsa, kallon fuskarsa sak take tana sauraronsa dan ta san a yanda ya kasance mutun mai taka tsan tsan ba zai yarda kamar sakarai ba a yi masa tambaya irin wannan ta fice ba tare da ya bada amsa ko ya ji dalili ba, Fuskarsa ya hade kafin ya ce"""" Comment , comment, comment *KUTKALE* *(PRISON)* NA *SAJIDA* Marubuciyar DUK KARYAR KADA YAR MAHAUKACIYA DAGA TAFIA DAUKAR SOJA NEMAN NA KAINA BANI DA ZABI IDAN KA RAINA INDA KAKE BAK'A CE INA KUKE MASOYAN NOVELS DINA, GANI NA DAWO DA SABON SALO, SABUWAR TAFIA, NA ZO MAKU DA SABON NVL DINA MAI TAKE *KUTKALE* WATO GIDAN PRISON, WANNAN NVL ZAI ZO MAKU DA LAMURA DA YAWA, KU BIYO NI KU SHA LABARI........ *WANNAN NOVEL NA SIYARWA NE, DU MAI SO ZAI IYA TURA KUDINSA TA wannan acct NAIRA DARI BIYU : Usman Muhammad 3072998062 First bank. Sai ya turo shaidar ya biya ta wannan number +22791466605....sannan a yi adding dinsa cikin grup, MUTANENA NA NIGER KUWA SANADIYAR RASHIN SAMUN ORANGE MONEY DA KUKE YI, KUNA IYA TURO HOTON KATIN SAHELCOM KO NA AIRTEL TA NUMBER KAMAR HAKA 91466605 SAI A SAKA KU A GRUP DIN, .....* taku ce, Sajida 1 Nufar gadon da Ni.ima ke zaune tana zarar ido ta yi, Irin yanda kirjinta ke dokawa da a lokacin ya yi gigin cewa da ita kekek...ba abinda zai hanata yin dayan biyu, au ta zura da gudu , au ta kwala ihu, domin wannan lamari ba jarumta ya aro mata ba , sai tarin tsoro da fargaba, ko a abubuwan da aka koya mata ba.a koya mata irin wannan ba. Tsaye ta yi gaban gadon tamkar an dasata , ta tsurawa Ni.ima ido tanai mata kallon da ita kanta bata san na menene ba, Can kamar an tsikareta ta dan farfado ta karasa da kyau wajen bed din , Sai da ta saka hannun mai dauke da abin aikinta na caje abubuwa ta caje gadon nan har kasan sa, Sannan ta dawo tsaye gaban Ni.ima, wace da ba aikinta ne ya kama da hakan ba, ba zata taba gigin cajeta ba, domin yannayinta bai nuna alamar muguwa ce ba, sai dai a aikinsu babu innocent face da ake ignored, kowama damka ake a bashi kyakyawan kulawan da ya dace.... Hannunta na dan rawa ta shiga bin du wani yaken da ake iya adana abin cutarwa a jikin Ni.ima har ta gama, ita kanta Ni.imar ta cika da mamakinta ta zura mata ido ne tana kallonta, Haka ta gama ta kuma bi dakin da bincikenta sannan ta juya kanta a kasa ta lalubu hanyar fita tana mai jin zuciyarta na gudun da bata taba yi ba,....namiji? Duk abinda take yana tsaye ne a wajen da ta barshi yana kallonta, Shi gaba daya ta zame masa wani abin nishadi, ikon Allah..wai ita nan caje matar da zai yi mu.amala da ita ta yi kennan? Kar ta kashe shi, Kafadunsa ya daga, kafin ya juyo da dubansa wajen Ni.ima, Yannayin da ya ga ta nuna ya jara bashi nishadi, Gadin ya tunkara kai tsaye, wanda hakan da ta gani ya sakata kara gyara zama tana kara sada kanta kasa tamkar ta zo gaban sarki, Tsayuwa ya yi yana mai bin ko.ina na jikinta da kallo, Zama ya yi bakin bed din, wanda ya bashi damar dora gaba daya kafafuwansa saman bed din aman kuma ya tankwashe su yana kallonta ya ce" aman ai kin san zaki yi wani abu dan birge ni ba wai kawai ki zauna min da wadinnan manyan kayan tamkar kin zo gaban liman ba ko? Gabanta ya yanke ya fadi, abinda zata birge shi? Shi ne abinda ta ayanna a ranta, to aman amarya ai daraja gareta ko bazawara ana shigo mata da fuskar kamala ana ririta ta, duk kuwa da ta san romonta za.a sha ...aman ana mai nuna mata da tafiar ba ta hakan bace, Sai gata, ita Ni.ima, ya Dadynta da momynta, ya daya kwal a wajensu, mai kananun shekaru domin bata fi ashirin da biyar ba , ta tare gaban namiji ingarma da zuciyarta ta rayu da soyayarsa, darensu na farko, tana hasashen tarairaya ko dan ramin da yake yiwa....sai gata ita zata tarairaye shi?, Kokarin mikewar da ta fahimci yana yi ya sakata saka hannunta na fama dake rawa ta rike hannunsa na hagu, Ba zata yi gangancin nan ba, ba zata yarda tana kallo ya fice a wajen nan ba, ba zata manta waye shi ba, dan haka mace ce ita ba zata yi wasa da damarta ba.... Hafsat na fita bata tsaya wajen bodyguards din Ni.ima ba kamar yanda ya dace har ya fito daga dakin..takim takim takim ta nufi tsakar gidan, Tana fita bata lura da BS dake tsaye yana gadin wajen ba ta yi gagawar dukewa wajen tana mai dafe wajen zuciyarta dan ta tsayar da bugawar da take mata, Riko damatsunan hannayenta da ya yi ya sakata firgita ta mike da sauri da kuma karfi da nihar kaiwa bugo, Tarewar da ya yi sannan ya bude bakinsa ya ce " hei Bab, menene haka ? Lafia? Tsai ta yi da yannayinta ta tsurawa fuskarsa ido, A *KUTKALE* an sha kokarin haye mata, Sai dai bata taba gannin ainahin abin, tudunsa ko yannayinsa ba, domin za.a shigo mata tsakiyar dare ne su sha dambe da mai tsautsayin, Aman yau, dan tudunsa ne ta gani ba wani abu ba, ta tsorata, Dan me maza fitsararu ne? Ba sai ya nunawa duniya shi din dan duniya bane za.a yarda, ya bar abinsa a shi kadai mana, ki Allah ya yi hani ga bawa tonon asiri idan ya rufa maka, Da sauri ta janye kafadunta da ya rike yana son ta dawo hayacinta, Sai da ta janye ya tuna cewar a duniya ta tsani lamari irinnan a taba mata kafadarta, Koda wasa bata son hakan, A hankali ya dan ja baya ya bata spac, hakan ya saka ta sauke ajiyar zuciya ta tsurawa waje daya ido tana mai sauraron yanda BS ke faman kwontar mata da hankali duda bai san abinda ya firgitata ba, Sun dauki lokacin mai tsayi, domin har duhu ya shigo sosai, Ita kam tana cikin halin rashin sallah hakan ya saka bata nemi zuwa sallar magariba ba, BS kuwa bai je ya yin bane, Suna hira tana dan kai dubanta wajen windows din dakin, zuciyarta na cike da tambayoyin da ta san ba zata taba samun amsar su ba.......... Kanta ta kuma dagawa ta kai dubanta wajen windows din, idannuwanta ne suka sauka a kan irin jar fitilar nan da ake daidaitawa jikin garu, wace ke hade da bindigar seti, ana daidaita wajen windows din dakin Ni.ima, Da idannuwanta ta yi masa nuni, wanda hakan na cikin aikinsa, Da wani irin matsiyacin gudu ya juya ya fita waje inda ita kuwa ta juya da mugun gudu ta afka cikin dakin ba tare da damuwar wani