← Book details Kutkale Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 2 OF 94

Sashe 2

Kutkale Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

yanzun kam, Ta birge ta, irin yanda ta tuka motar dake faman juyewa da su, irin yanda yarinya karama da ita ta warci babur ta yi masa irin tukinnan, kai da zata samu wannan aikin, ta zama irin wannan baiwar Allah da ta so, ta gama tafia da ita, A lokacin da ta mayar da Abayarta ta fito cikin nutsuwa tana goge jinnin dake zuba a hannunta wanda ta ji a lokacin da ta daki gilas din motar, ta dubi yarinyar da ta gama baiwa tsaro, Murmushi ta sakar mata, ta mika mata hannu kan su yi salama Itama cikin murmushin ta bata hannun suka yi musabaha, Murya kasa kasa Hafsat ta ce" bawa na tsintar kansa a rayuwa kala kala, idan yana da dabara zai dauketa yanda ta zo, Babar dabarar da bawa zai yiwa rayuwarsa shi ne, ya iya rike opportunity.....bata fiya zuwa sau biyu ba, *FREIND* Da haka ta saki hannunta ta juya cikin tafia ta yanga irin ta yar budurwar da ta cika ta batse take takama da sura mai kyau, Hafsat ta gama hardace abubuwan d aka koya mata hakan ya sa ba zaka taba tunanin tana iya juyewa ta daki fada na mamaki Tunda ta taho ya shagalta da kallonta, yannayin yanda take shawagi, ga sansanyar iskar safiya na kadata, Murmushin da bai shirya ba ya saki yana kara kallonta, kafin ya waiga inda aka saka mutanen da aka kama da direban cikin motarsu, Tana zuwa ta zagaya ta shiga motar ta zauna mazaunin direba, Idannuwanta ta lumshe tana mai jin yanda mitar ta dauki shiru, A hankali ta mika hannunta wajen kuna redion motar ta kuna, sai waka ta shiga tashi ta hayaniya irin wannan, Hannunsa ya kai ya kashe, da hannu ya yi mata nuni da GN na sauraronsu fa, Dan karamin lebenta ta tabe sannan ta shiga bin garin da kallo, tana mai tunanin abinda zai kara fitar da ita, wata mission din? Ko da suka karasa computernta ta dauka ta shiga yanar gizo tana bincijen abinda ya shafi aikinta hankali kwonce, idan ta motsa daga inda take dan ta gabatar da ibadarta ne, A cikin wannan daren suka tashi da tashin hankali, daya dake cikinsu da ta tafi kasar Span dan baiwa wani atajirin saurayi tsaro, an cin mata, an zo harbe shi rana kusa aka hada da ita, inda shi bai mutu ba, aman ita a lokacin ta amsa kiran Allah, Wannan lamari ya girgiza su, domin yarinyar bata da damuwa, bata da dagin kai, duda yar wani ce bata da wata damuwa da hakan, Haka suna ji suna gani aka shirya gawarta cikin sanduki hayan an yi mata likafani aka kuma nadeta da drapo din niger ana sakata a sanduki aka tafi da ita inda za.a yi mata sutura tare da iyayenta wa.inda sai dai su ga sandukin, ba zasu ga gawarta ba, A wannan ranar wajen mutun uku suka ce sun fasa aikin, inda wajen ya rikice da rigima da koke kokensu, sun tsorata, harbi a kai? Ta tafi shikenan? Sun matukar girgiza, kowace so take ta samu mahaifinta , bata so, ta fasa wannan aikin mai cike da gadari.....su sun dauki hakan a matsayin gayu da nunawa duniya su din jarumai ne, aman haka kawai sai a kawo gawar daya? Aa...... ...................................................... Bayan kwana arba.in Du wani na nesa da na kusa, qminan arziki dama yan uwan yan uwa du sun tatara sun koma daga gaisuwar rasuwar mahaifiyarsa, Kanwar mahaifiyarsa da Muhammad kawai suka rage, shima Muhammad ya yi zuwa uku kasarsa ya dawo ne, Abdul Jabar ya zana wani silent man Askin nan da yake yi kwalkwal ya aske kai, rabonsa da shi tun kafin rasuwar mahaifiyarsa hakan ya saka suma ta fito sosai kansa, suma mai yawa mai kuma tauri tauri hakan ya saka kan ya cika da gashi irin yanda samari ke tarawa , Sajensa da a da yake askewa baya barin ko kadan, yanzu ya fito sosai ko.ina ya zagaye fuskarsa, Gemunsa ya kara cika, lebensa suna da dan girma, dan ba zaka taba kiransa da mai kananun lebe ba, aman kuma ba dambatsa dambatsa bane, Idannuwansa sun fi komai girma a fuskar tasa idan ka cire karan hancinsa mai tsini, idannuwansa jajajir suke, rabonsu da su yi haske tun a lokacin da yake tataunawa da mahaifiyarsa yana mata murmushi itama haka, Zaune suke su su uku, Su biyun suna dan taba hira, ba ta komai ba sai ta zaman duniya da jimamin yau da gobe wanda bai bar talaka ko mai kudi ba, Tunda suke magangannun shi dai kansa a kasa yana sauraron su, bai ce da su komai ba, haka kuma bai hana su maganarsu ba, A hankali ya bude bakinsa, muryarsa da ta zama wata iri mai amon irin muryar nan ta kakarfan maza ko wa.inda giya ta kashe masu zakin murya ya ce" aure nake so. Muhammad dake magana da aunty Firdausi ya juyo da sauri yana kallon Abduk Jabar, Itama auntyn hankalinta ta maido kansa, Dago da idannuwansa da a yanzu in dai ba dole ba , mutun ba zai so su kurewa juna kallo ba, ya sauke saman kansu, Lebensa na kasa ya kamo da harshensa ya shiga dan tsotsa yana kallonsu bai ce da su komai ba, Kai aunty ta kawar daga dubansa ta ce" Aure? A hankali ya saki bakin nasa ya ce" eh, aunty na san kin san na yi rayuwar rashin jin magana, To bana so na sake , dan ba zan so a tayar da mahaifiyata a nuna mata abinda nake daga kabarinta ba, kuma gashi ina son mace a kusa da ni, dan haka zan yi aure..... Muhammad ya shiga jinjina kai yana mamakin jaraba irinta abokinsa, Aman kuma ba laifi tunda yanzu ya nemi ya kara wani auren.....aman kuma wani abu ya tsaye masa a rai, ba irin maganar da ba.a fada masa kan ya daina harkar mata ko dan mahaifinsa idan baya tsoron sauran abubuwan, ya ji kunyar Allah, ya kuma kaucewa mahaifinsa shiga halaka ta dalilin sabon Allahn da yake, Yakan ci gaba da shagalinsa , aman yanzu ya nuna zai fasa dan mahaifiyarsa? Me abansa ya yi masa haka? Ko dai da wata a kasa? Irin rayuwar rashin sannin ciwon kan da ya ringa tafkawa? Dubanta ta kawo saman kansa bayan ta yi dogon nazarin maganarsa, a hankali, a nitse, da yannayi na rarashi, da neman cin galaba kan maganarta ta ce" aure ba laifi, za.a nema maka auren ko yar gidan wa kake so, Sai dai da sharadi Abdul,.... Maganar *BODYGUARD* da mahaifiyarka har ta rasu tana fama yana nan daram bai canza ba, Za.a je a dauko kwararun bodyguard biyar, Daya zata baiwa matar da zaka aura tsaro..... Hudu zasu kasance da kai idan maza kake so ko mata, a dukan motsinka, Abdul kar ka yi min gardamar haka, dan na rantse maka da Allah Ku yi hakuri, i.m sick ne, , na gode da adu.o.inku, Allah ya saka da mafificin alkhairi *KUTKALE* *(PRISON)* NA *SAJIDA* Marubuciyar DUK KARYAR KADA YAR MAHAUKACIYA DAGA TAFIA DAUKAR SOJA NEMAN NA KAINA BANI DA ZABI IDAN KA RAINA INDA KAKE BAK'A CE INA KUKE MASOYAN NOVELS DINA, GANI NA DAWO DA SABON SALO, SABUWAR TAFIA, NA ZO MAKU DA SABON NVL DINA MAI TAKE *KUTKALE* WATO GIDAN PRISON, WANNAN NVL ZAI ZO MAKU DA LAMURA DA YAWA, KU BIYO NI KU SHA LABARI........ *WANNAN NOVEL NA SIYARWA NE, DU MAI SO ZAI IYA TURA KUDINSA TA wannan acct NAIRA DARI BIYU : Usman Muhammad 3072998062 First bank. Sai ya turo shaidar ya biya ta wannan number +22791466605....sannan a yi adding dinsa cikin grup, MUTANENA NA NIGER KUWA, ZAKU YI MIN ENVOI NA DALA DARI BISA NUMERO KAMAR HAKA 92777744 AMAN FA TA ORANGE MONEY.....* taku ce, Sajida 8 *Free page* Gaba dayansu ita suke kallo, Lokaci guda Madame Bilkissu ta kara shigowa face to face da hafsat ta ce" wani diplom gare ki kafin ki shigo nan? Zata bada amsa GN ya yi gagawar matsowa ya ce" Confidential ne Madame, Dubansa ta yi da kyau kafin ta dubi Hafsat , Agogon hannunta ta kalla ta ce" ta mini, na fasa cinikin farashin daukan nata, a bani ita a kudin da aka yanke min, Ba karamin mamaki hakan ya basu ba, sai dai ba mamaki kadai ba, harda tsoron kar aje da biyu ta yi haka? Ya kama GN, shi kuwa SB shiga kimtsata yayi yana fadin Allah ya sa kar ta je ta tafka iya yin nata ta hanyar bada labari har ta tona asirin gidannan! Haka aka hada mata abubuwan da ya dace, sannan aka bata wani dan abu dan karami aka ce ya kasance koda yaushe cikin kunnenta, banda wanda da shi dan baya son ruwa, ta kiyaye ruwa ya shige shi, Karba ta yi ta saka a kunnen nata, wanda zai ringa basu damar jinta da kuma yi mata magana ne, sannan zai basu damar gyara mata abin gyarawa har dai lokacin da za.a magance menace din dake tunkaro wace zata kare lafiyarta, Haka ta je suka shiga mota, nan su duka aka rufe idannunsu suka dauki hanya, Sai da suka jima sunna tafia sannan aka tsaya, Cire mata abin idon, hasken ranar da ya tandi idonta da fatar jikinta ya sakata saurin rintse ido sannan ta kare da hannunta, A hankali take jin ranar a jikin fatar jikinta har ra iya supportg dinta, yaushe rabonta da rana haka? Yaushe rabonta da su hade haduwa irin haka da rana? An jima, a gaskiya an jima, sai tace tun da aka daukota daga *KUTKALE* , Lauyar na kallonta ta ce da ita " mu je, Bin bayanta ta yi suka nufi motar da ta zo da ita, Har zata saka ky ta bude motar su shiga, Hafsat ta yi gagawar dakatar da ita, Ky din motar ta karba tana dubanta kafin ta ce" duniya ta ci gaba fiye da tunaninki, Ana saka yar karamar Bomb wace zata daki wajen gidan mai ta tayar da mota cikin kankannin lokacin da damar da gareka kawai ta ka saka kys din motar ka juya kys din ne, Ki matsa, Da mamaki take kallon yarinyar da ta tabata ta haifeta da cikinta, aman wama ya san da ta zo
Chapter 2 · 0% Book details