Sashe 72
Kutkale Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
yana kallonta ya ce" ki bani amsa ke nake sauraro Hafsat, me ya maki? Me da me ya maki? Wai wa kake nufi Abdul? Hafsat ta fada tana dan matsawa daga irin maysewa juna wajen da suka yi A hankali ya maida bayansa jikin kujerar ya jinginar Ya jima a haka dan a kadan ya dauki minti goma sha biyar inda Hafsat ta takure jikinta tana kallon kasa tana murza hannayenta a kasan zuciyarta kuwa sai yawo take mata, tsoro ne ke faman halakata, a gaskiya ta tsorata da yannayinsa gashi ya yi mata tambayar da bata fahimta ba Hannayensa gaba daya ya dora saman kansa, gashin kansa da ya caje ya yi tsaf da shi ne ya saka yatsunsa ya cakule tsarin gashin Yatsun nasa ya yi ta cusawa cikin kan kafin yake samu ya dan saisaita kansa A hankali ya kai dubansa jikin rigarsa , wajen wandonsa Ajiyar zuciya ya sauke ya kali agogon hannunsa sannan ya tayar da motar ya kama hanya Tuki yake ba tare da ya kuma yi mata magana ba a haka har suka isa kofar gidan malan Ja ya yi ya tsayar da motar, bai kaleta ba bai kuma yin magana ba sai dan sada idannuwansa da ya yi dan baya son ta san waye shi a fagen bacin rai, zuciyarsa idan ta kai makura suma yake , hakan kuwa shi ya fi zama alkhairi domin da bai suman ba sai dai kuwa shi ya summar dan riko yake yiwa mutun wanda sai dai idan ya fadi mutun ya gudu hakan kuwa komai girmanka raf yake yi da kai sai dai a yi abinda za.a yi, baya gudun ya kama mutun du shekarunsa Kallonsa ta kara yi, jikinta ne ta ji ya yi mata mugun sanyi, eh lale ta san waye shi, tana iya fadin kadan daga halayarsa da ta sani , ta san rigimame ne shi mai mugun fada aman kuma bata san shi da hadiye bacin ransa a kanta ba hakan ya saka jikinta yin mugu mugun sanyin A hankali ta saka hannunta ta bude motar Kafarta daya ta fitar tana kokarin fitar da dayar ya riko hannunta na hagu dake kusa da shi Murya can ciki ya ce " ban lamunce fitarki ko kofar gida ba Yana gama fada ya sakar mata hannun, a hankali ta juyo da dubanta ta tsayar a ka fuskarsa Dan tsai ta yi sannan ta fice gaba dayanta ta bara masa motar Daga wannan lokacin, Abdul bai kuma kiran layinta ba , ya san ita ba zata kiraye shi ba dan haka bai kankara hakori a hakan ba, bai kuma zuwa gidan malan dan su hadu ba daga karshe tafiama ya yi bayan kuma an saka ranar da za.a kaita gidanta wace bata fi sati daya ba domin malan ba.ai masa kowani sabgar aure da ta fi saukar alkur.ani Sosai abin nan ya tsaye mata a rai, takan zauna a dakinta idan yan uwanta sun bata sarari ta dan huta ta zurfafa a tunanin me kuma hakan ke nufi? Me abdul ke nufi da ita ne? Ta sha ta dauki waya dan yi masa message sai kuma ta ajiye ta yatsina fuska a fili ta ambata koma me kake nufi da ni daidai nake da kai malan, nima ba sonka nake ba bare abin ya dame ni Abinda ya fi madaukakin bata mamaki shi ne message din bank da ta samu da makudan kudi a ciki, sai bakuwar lambar kasar waje da ta yi mata message cewa kudin aikinta da ta yi a matsayin bodyguard ne, Sai kuma wasu kudadan da suka shigo mata bankin ne dai, accmpte din da bata san lokacin da ta bude ba dan ita dai bata taba budawa ba aka kuma shaida mata da kudi sun shigo wayarta da sabon message da number dai an saka mata Idan kina da wata bukata ki min message Kanta ta girgiza ta ajiye wayar, bata ma fadawa kowa ba dan ta fahimci cewa Abdul ne ke wannan aikin, shi mai kudi ko? Ita zai hau ta haka ko? Itama ta shiga layin matan nasa kennan, ya aura ya wulakanta so yake ya ga tana biye da shi tamkar jela, yo ita da ba dan ta san idan ta tsiro da maganar bata sonsa da aure ba mahaifiyarta zata fita hankalinta ba da ta nuna masa ita zata fara neman sakin a wajensa, ba zata taba bari ya wulakantata ba a haka, bata nemi ya rufa mata asiri ya aureta ba bale har ya mata iza! Abdul kam ya sadar da kansa garin Minna, Gidan horon da ya kai Muhammad ya yiwa tsinke, nan ya tarar da shi tamkar ba shi abinka ga farin mutun da ya saba rayuwar hutu, Tsayuwa ya yi gabansa bai furta masa A ba yana kallonsa yana so ya dago su yi ido cikin ido sai dai ina ya kasa dago da kansa bale har ya yi ido hudu da shi dan kuwa wani mugun tsoronsa yake ji, yanzu haka da aka barshi daga shi sai shi gaba daya jikinsa bati yake, da haka azabar wahala take? Da haka duniyar da ba dadi ba sanyin ac ba abinci ba barcin kirki bare wajen kirki yake? Da haka matsatsatsin gidan duniya yake bama na kiyama ba? Shi da yake daukan kansa wani shege har yake tunanin a kan soyayarsa ba abinda ba zai iya ba, ba irin wahalar ba zai jura ba sai gashi wahalar duniya kawai ta saka shi ya fara zarewa dan a yanzu daga ya ga duhun magariba ya fara yowa ya fara ihu tun karfinsa yana neman ceto, wai hakan a duniyar kennan, shi da ya kashe rayuka tamkar kiyashi ashe ko karfin jinnin su ba zai masa adalci ya saka shi zama fitacen masifafe ba? Shi kam ya ga rayuwa, yana cikin ganninta.... Yana so ya buda bakinsa ya duka gaban Abdallah, sai dai ya sani ne mai yiwuwa ya matso da zuwansa kabari! Sai da Abdul ya gama kallonsa sannan ya juya ya fice a wajen, nan aka ja shi kiiiii aka jefar cikin gagan yan kurkukun dake jiran ko ta kwana! Ya jima cikin mota, kansa hade da sitiyarin motar ya rintse idannuwansa, Zuciyarsa yake ji ba dadi, abubuwan da zuciyarsa ke raya masa a kan rayuwa da rayuwar amininsa ya saka shi dagawa zuwa saudiya Ya kusanta kansa da Allah ko zai samu sasaucin sake saken da ruhinsa ke masa... wannan shi ne mafarin dagawarsa zuwa saudiya Yan uwa sun je gidan da Abdallah ya fada dan gyarawa Hafsat daki wanda ba yanda bai yi ba kan ba sai an kai komai ba aman malan ya ce ya jima yana shirin kayan dakin mamansa Sun gigita da gannin wai a wannan gidan ne Hafsat zata yi zaman aure, Hafsat dai maman malan? Ita ce da daukaka haka? (Yanzu mutanen mu idan ka yi aure ba.a wani tunani sai na sharetan gidan da aka kai ka Lale yar malan ta samu waje Har suka yi suka gama basu ji alamun da wata halita a gidan ba, basu ma san mijin na da wata matar ba, haka suka dawo gida a lokacin an rufe daki anaiwa Hafsat kunshin tukunya ga dumin dakin kadai wani tashin hankalin ne, suka zo suna ta santin gidan da tsare tsaren gidan da irin abincin da aka kawo masu wai daga gidan mamansa sai dai basu ga maman nasa ba Ita dai mama bata ce komai ba, sai su aunty dake amsawa a haka har aka gama aka watse da niyar gobe wajen yama za.a dawo a raka amarya dan kowa ya sani gidan malan ba.ai masa bidi.a Tsakiyar dare wajen karfe uku mama ta tasota daga dakinta ta kamo hannunta ta hau da ita dakin malan A lokacin yana zaune saman salayarsa yana jan carbi, suna shigowa ya daga hannayensa ya shafa fatiya sannan ya mike ya dawo saman kafet din kamar yanda suka zauna suka tankwashe kafafuwansu shi dinma hakan ya yi Sai da ya sauke ajiyar zuciya sannan ya ce" Alhamdulilah, yau dai Allah ya nuna min ranar da zan sada mamana da dakin aurenta, Mama? Da sauri ta dago da dubanta domin kanta a sade jikinta kuwa sai rawa yake, Subahannallah shi ne abinda na fada, domin wani irin goshin amare da ake cewa da na hanga a fuskar Hafsat yana wani irin kyali, gaba dayanta ta canza, gyaran amare ya mugun karbanta, ga jan kunshin da akai mata na zamani na amare abin ba.a cewa komai Idannuwanta kuwa tamkar sun kumbura, da alama kuka maman maman malan ta yi, yannayinta da ya gani ya dan karyar masa da zuciya sai dai ina a yau ita ce ranar karshe, baya so safiya ta waye bai yi magana da ita ba, dan haka ya ci gaba da fadin" shin zaki zauna a dakin mijinki ki yi biyaya ki girmama sunnar ma.aiki? Mamana, zaki je ki rayu da niyar sai dai a fitar da gawarki daga dakin ki? Ummana zaki je zaman bauta, gwagwarmaya da zuciya daya da niyar neman sakamako a wajen Allah? Gabanta ne ya shiga dokawa, irin yanda mahaifinta ke mata magana a yanzu A hankali kuma ya sasauta muryarsa ya ce" kowani uba burinsa ya yiwa yayansa aure, Allah ya cikan burina, zan so y'ata ta zauna dakin aure, Mamana rayuwar aure wata sabuwar rayuwa ce da zaki shiga mai wuyar fasara, Hakuri, hakuri, umana hakuri, Ko wa kike aure, komai girman son da yake maki to fa lale sai kin juri wannan kalma ta hakuri sannan zaki ga haske a rayuwar zaman auren ku, Ki yi masa biyaya, sai ku wanye lafia Mamana, Abdallah dai mai aure ne, kin san da yana da aure, kema kin tashi gidan da mahaifinki ba daya ya ajiye ba, ke koda mamanki daya nake aure idan kin auri mai mata sai ku zauna lafia! Na hane ki fitina, na hane ki taurin kai, rashin kunya ko gardama, Mamana ki kasance........ kukan da ta rushe da shi ne ya saka mahaifinta sada kansa, har cikin ransa yake jin irin yanda take kuka, da ba dan mamanta na kusa ba ya tabata zai yi shiru ne da nasihar ko zara daina kuka, Allah ya saka masa kaunar yarsa