← Book details Kutkale Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 80 OF 94

Sashe 80

Kutkale Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

zata kara sumewa Dubansa ya kai wajen nurse din ya umarta da a yi mata hoton cikin da na.urar haskawar Yana gefe yana kallo yanda suka ja rigar, Sai da aka shafa mata wani ruwa ruwa mai mai sannan aka dora abin haskawar, A hankali suka ringa bin shafafiyar mararta suna haskawa, lokaci daya kuma suna daykan hoton wajen da ya dace, doctern kuwa yana tsaye yana ganni da kyau Sai da suka gama sannan ya amsa , Sai a lokacin ya tsira ruwan allura ya tsira mata A hankali a hankali ta fara sauke ajiyar zuciya, a haka har ta saku ta ji ya lafa mata sosai da sosai Sai a lokacin ta bi dakin da kallo, nurse daya ce can gefe kusa da docter, sai ita dake kwonce saman gado an rufa mata wani abin rufa wajen kirjinta A hankali ta sauke kafarta daya, dayar ra miko ta sauko cikin nutsuwa baki dayanta ta sauka daga saman bed din Mararta take ji ta yi mata wani mugun daurewa da nauyi, Bata yi kasa da gwuiwa ba ta tunkari wajen doctern, shima lokacin ya ga ta sauko Nurse din ce ta kamata ta zauna a wajen da ya nuna mata Sai da ta yamutsa fuska domin yana kara murda mata kadan kadan sannan ta fuskanci doctern da kawai yake binta da kallo Sai da ya dan sosa kansa sannan ya shiga yi mata tambayoyin da suka shafi aikinta ko karatu, shekarunta, shekarunta nawa da aure, Tambayarta ya yi cewa, shin kafin ta yi aure ta ringa shan maganin hana daukan ciki? Jin cewa auren nata gaba daya bai fi wata biyu ba Ido ta tsura masa, cike da mamaki, Kanta ta girgiza Ajiye biron hannunsa ya yi ya ce" look, zan so ki bani gamsashiyar amsar da zata bani damar dora ki abinda ya dace, mararki na cinkushe ne da maganin hana daukan ciki, na.urar da muka yi anfani da ita ta bamu damar fahimtar hakan Ajiyar zuciya ta sauke, a hankali ta ce" ban taba sannin kalarsa ba Docter ya dubeta da yannayin mamaki, aikinsa ne ya zama wajibi ya bi didigi, dan haka ya ce" ko dai kin sayi magani a bakin titi na mura ko wani abin a rashin sani an baki wannan? Shi kansa sai da ya fadi hakan ya ga abin wani baibai, a bakin titi? Hafsat ta dago da dubanta, zuwa lokacin hankalinta ya fara tashi, Idannuwanta ta saka cikin na docter ta ce" bana shan magani na fi kaunar a min allura da na hadiyi magani! Rabona da na hadiyi magani na kusan shekara hudu! Bana sha, bana bukatar shan magani docter! Kansa ya daure, dan haka ya ce" magani ne mai hatsari kika ringa sha, ba sai kin sha shi a gudajinsa zai tarun maki a mara ba, koda a narke kike shan sa idan ya fi karfin ki zai je ya tarun maki ya zame maki matsala, magani ne mai narkar da sperm, muna samun irin cas din nan sosai, bamu bata a hakan, aikina ne fannin mata, yanzu haka zamu dauki fitsarinki dan mu ko ahigar cikin kika samu yake faman barewa ya saka haka? Hannayenta gaba daya biyun ta dora saman table din, a hankali ta dora su saman yalwatacen gashin kanta dake fitar da ni.imtacen kamshi Gabanta ne ke faduwa, lokaci daya rigimarsu ta baya son haihuwa ba zai daina baiwa matarsa maganin rashin daukan ciki ba ta shiga fado mata a rai, tun tana matsayin bodyguard dinsa, tun a lokacin da yake yi mata maganar matsalarsa a ranar da ta yi fushi ta shige dakinta ya bi bayanta yake mata bayani, har ta yi masa nunin yana tunanin ya isa ya zagaye abinda Allah ya hukunta a kansa? Da sauri ta dago da dubanta ta ce" docter, ko a cikin abinci, ko a jus ana iya narkar da shi? Docter ya bata amsar kwarai kuwa Gabanta ne ya kara faduwa, lokaci daya kuma ta samu ta mike daga zaunen da take, Lale yau ta yarda cewa rayuwar da suke da shi ana yinta ne bisa tafarkin sha.awar jikinta, ta sani mace bata daraja a wajen Abdul, rashin nuna mata soyayarsa bai dameta ba gannin suna zaman lafia, sai dai a yau ta gane yana zaune da ita ne da zuciya biyu, suna zaune gida daya karkashin innuwa daya suna wasa da dariya suna raba shinfida daya yana tatalinta yana rungumeta ba dan so ba sai dan albarkatun jikinta, ita kuwa me ya rufe idannuwanta har haka? Me ya yi mata dadi haka? A yau a duniya ba zata iya zama da mutumen da baya tsoron Allah har haka! Da ta mutu fa? Da ta samu mugun ciwo fa? Yanzu haka wa ya san me ya samu mahaifarta? Sam, bata ma fara yi masa son da idannuwanta zasu rufe ta zauna da shi yana bata maganin da zai cutar da ita a duniya sannan ta je ta tarda Allah, yo ita wani dadi ta ji na duniya da har zata ki mararin samun dan jaririn da zai debe mata kewa? Namiji? Zara yi ta zama da shi kulun a dadi zuma ne? Watarana sai ya nuna mata halin, wata rana sai ya yi mata abin, idan ya mayar mata da wuninta tamkar tana prison din KUTKALE wani sanyin idanniya zata kalla ta ji sanyi? Yau du wanfa baya son haihuwa da kai baya son ka, koda mutuwa ce zai maka fata Likitan ne ke kiran madame, ji mana? Nurse din ma ta biyo bayanta sai dai ina, gashin kanta ya yi mata male male a jikinta, rigar ta mugun karbarta du kuwa da jigatar da ta yi ta fito a dakin Abdul dake tsaye yana kallon kofar dakin urgence din ya tako da sauri yana kallonta da mamakin har ta mike likitan bai fito ya kiraye ahi ba?? Hannunsa ya mika wajen fuskarta, murna, mamaki, da fargaba ya dan dago habarta yana kallonta, a hankali ya ce" Kauriyata, kin tashi? Ni na san sai kin fi karfin wannan ciwon! Me aka ce ke damun ki? Mu koma na ji bayanin likitan A hankali ta saka hannunta ta cire nasa daga habarta, Idannuwanta da suka canza mata ta dago ta saka cikin nasa cikin wani irin kallo na kakausa, A hankali ta ce" Abdul, dama haka ne rayuwa? Ashe ki ba zai tana zama so ba? Abdul na godewa Allah da bana jin ko digon son ka a raina! Gabansa ne ya kwonci kwonci ya fadi, da sauri ya kara buda idannuwansa yana kallonta, a hankali ya ce" Hafsat, kwakwaluwarki ta tabu ko.me? Me aka baki a cikin dakin can??? Hafsat ta yi murmushi tana kallonsa, a hankali ta ce" Alhamdulilah, ban haukace ba, hasalima na fi kowani lokaci nutsuwa, Abdul dan Allah na roke ka, ka je gida ko ka tsaya a hanya ka rubuto min takardata, na hakura zama da kai! Da karfi ya ce" *KE* Hafsat ma ta ce" *KAI!* Na tsane ka Abdul! Na tsane ka! Ka sake ni, in sha Allah koda ka bata min mahaifa ba zan rasa mai kwasana a haka ba! Hannunta da ya rike ba da karfi ba ta fizge daga rikon ta juya da sauri ta fice a haka Summar seconni ne Abdul ya yi a tsaye sakamakon jin cewa ta farga da abinda ya ringa bata cikin jus ko abinci, Kalamanta suka kasance ruwan farfadowarsa, Lokaci daya ya daga kafarsa da gudu ya bi bayanta, Har ya kusan fita ya dawo doctern dake tsaye ya ciro baje dinsa ya nuna masa, a gagauce, murya cike da jaraba da tashin hankali ya ce" walahi sai na tagayaraka! Na rantse ba zan barka haka ba! Doctern ya bi rubutun da kallo lokaci daya kuma Abdul ya fice daga wajen, Doctern ya kalli nurse din itama shi take kallo, Muryarta na rawa ta ce" docter dama ana haka? Ba aikin ka ka yi ba??? Doctern ya juya da sauri ya shige Office yana danna wayarsa Abdul da ya fito a kafarsa da mugun gudu, sai dai me...adaidaita ya hangi ta dauki Hafsat har sun falfala da gudu Wani irin ihu ya saki a wajen ya ce" Hafsat! HAFSAT! Burbudin hayakin adaidaitar kawai ya bade shi, lokaci daya ya ringa jin duniyar ta yi masa zafi, Hankalinsa ne ya ringa jin ya gama tashi, a hankali ya ringa jin numfashinsa tamkar na mai ciwon huka sai sama yake yana kasa, Hafsat ce zata bar shi? Hafsat din sa ce zata bar shi? Ky din motarsa ya laaluba ya ji baya jikinsa, Ya tataba ita ta lalube dan kar ya bi ta da gagawa! A hankali ya ce" Hafsat, kar ki bar ni....na tuba Idannuwansa ya rintse yana jiran wani adaidaitan, dan ya san kawai gidan malan zata je, zai kai kansa da kansa , a yi masa du hukuncin da ya dace aman walahi ba mai raba shi da matarsa! A lokacin daa Adaidaitan ya tsaya ya shiga, sunnan anguwar kaawai ya fada masa, bai damu da yau ya taba shiga adaidaita ba, hankalinsa a tashe kawai yake! A hankali ya kuma fadin" ko hijab babu a jikin ki Hafsat, na san darajar du wata halita taki Hafsat, yaya zaki fita cikin garin dake cike da kuraye a haka? Hafsat, ina *Kishin ki *, .............. *KUTKALE* *(PRISON)* NA *SAJIDA* Marubuciyar DUK KARYAR KADA YAR MAHAUKACIYA DAGA TAFIA DAUKAR SOJA NEMAN NA KAINA BANI DA ZABI IDAN KA RAINA INDA KAKE BAK'A CE INA KUKE MASOYAN NOVELS DINA, GANI NA DAWO DA SABON SALO, SABUWAR TAFIA, NA ZO MAKU DA SABON NVL DINA MAI TAKE *KUTKALE* WATO GIDAN PRISON, WANNAN NVL ZAI ZO MAKU DA LAMURA DA YAWA, KU BIYO NI KU SHA LABARI........ *WANNAN NOVEL NA SIYARWA NE, DU MAI SO ZAI IYA TURA KUDINSA TA wannan acct NAIRA DARI BIYU : Usman Muhammad 3072998062 First bank. Sai ya turo shaidar ya biya ta wannan number +22791466605....sannan a yi adding dinsa cikin grup, MUTANENA NA NIGER KUWA SANADIYAR RASHIN SAMUN ORANGE MONEY DA KUKE YI, KUNA IYA TURO HOTON KATIN SAHELCOM KO NA AIRTEL TA NUMBER KAMAR HAKA 91466605 SAI A SAKA KU A GRUP DIN, .....* taku ce, Sajida 6 Direct bakin makaranta Abdul ya nufa, dan ya tabatar cewa
Chapter 80 · 0% Book details