← Book details Kutkale Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 5 OF 94

Sashe 5

Kutkale Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

da desespoir din dake nuna bai san kan abinda ya hadasawa Sire wannan rashin lafia ba bana gannin komai, Yana maimaita ko ya shaki wata iska ne? Ko wani abin? Yace a kai shi asibiti dan su shiga bincike su ga abinda ya same shi ya hadasa masa haka, binciken da kan iya daukan awowi domin inji ke bada amsoshin ba mutun ba, Shiru ta yi kafin ta kara dubansa da idannuwanta da suka ciciko da kwallah cikin wani irin sanyi da murya mai rawa rawa ta ce" *idan fa ya mutu kafin lokacin?* jinni ne fa ke zuba daga hancinsa *Bashir* Tsai ya tsayar da idannuwansa cikin nata jin yau na farko kennan da ta taba kiran sunnansa kai tsaye, ashe ta san sunnan? Ashe ta san sunnansa? A gaskiya maimakun yannayinta ya saka shi cikin shaukinta sai ya saka shi cikin halin damuwa, shi fa ko me za.a ce ba za.a iya saka shi yarda da wai Hafsa na haka dan samun yanci bane! Dan haka shima cikin dakewa ya ce" idan ya mutu, ai lokacinsa ne ya yi, akoy wanda ya isa ya hana shi tafia ne? Mamaki, tsoro, duka suka daketa tana duban BS yana dubanta ya furta mata haka? A hankali ta hadiyi yawun dake bakinta dan kadan wanda da shi da babu kusan daya, ta lumshe idannuwanta hakan ya saka hawayenta zubowa bisan kumatunta, Wannan karron muryarta ta daga ta ce" na rantse da wanda raina ke hannunsa idan akoy wanda zai fita da wannan mutumen yau sai dai idan harbe ni zaka yi kafin a fice da shi! Ban ga wani dan adam din da zai kara nisan kusancina da Malan ba! Juyawa ta yi da sauri tana kokarin ciro karamar bindigar dake kugunta BS ya yi saurin damko hannunta ya juyo da ida inda du su Muhammad da docter suka juyo wajen da suke dan kuwa da gaske ta tayar da kukuma gata tsurut a gabansa BS na kallonta da takaici ya ce" kin san ba ke daya ke anfani da bindiga a wajen nan ba ko? Kuma kin san gaba dayanmu manyanki ne ko? Ke ko kunya bakya ji saboda shi zaki yi haka? Hannunta ta fizge ta ruruko idannuwanta, wato dai masifar ta motsa ta ce" me ya kai kudi daraja a wajenka? Kai saboda kudi kana iya yin komai ko? A tsaka mai wuya muke daga ni har kai! Ka harbe ni kawai ka huta da ni, idan ka harbe ni me za.a yi? Ba abinda za.a yi kana iya cewa kan aikinka kake na tare maka hanya BS! Hannunta ta kara fuzgewa daidai lokacin Hasana ta shigo domin dai sabon Bodyguard dinma na casan kokowa da Ni.ima wace sai zuwa lokacin da ta ji kukan Ambulance ake fada mata mijinta ne ba lafia dan haka ta fito da rigimar sai ta je inda yake Hasana na shigowa ta kai dubanta wajen BS tana jiran umarnin yanda za.a yi da Hafsat, sai dai ga mamakinta sai ta ga ya saki hannun na Hafsat din ya barta sai da ta fara tafia wai kamar BS ya sandeta ya buga mata hannunsa dake mike a bayan keyarta hakan ya hadasa mata zuwa duniyar summa Bata gama jin tsanar Hafsat ta darsun mata ba sai da ta ga BS ya kinkimeta ya dorata saman kujera mai cin gurin mutun hudu ya mikar da ita ya gyara mata kwonciya sannan ya mike yana kallon Muhammad dake jefo masa kausasun tambayoyi kan abinda ke faruwa, Muryar docter ce ta katse masa hanzarinsa inda ya furta cewa maza a shirya shi a dora shi kan gadon mararsa lafia a fita da shi a saka shi Ambulance A lokaci guda BS ya mike ya zuba masu ido su duka ya kalli wannan , ya kalli wancen, ya kalli Hafsat dake kwonce filat da ita, Ya shiga rudu, gashi a tsaka mai wuya........ Sai da ya fara tafia ya ce""" *shin, za.a yarda a fita da Abdul bayan tabas gaskiyar Hafsat ne komai na iya faruwa, dan kuwa ko doctern kansa ana iya sayensa irin wannan naci na a fita da Abdul? Waye wannan bawan Allah da ya damki hannun Hafsat? Zai bada taimako ko zai cutar ne? Meye dalilinsa na yin daya cikin biyun? Me ya faru a wajen daurin auren da Abdul ya tarwatsa? Hafsat, me ke damunta? Idan wannan magani da ta fada na cutarwa ne fa? Idan aka ki yi masa kuma a je shi din ne magannin da zai bashi taimakon? Ku biyo ni mu je zuwa daga alkalamin yar mutan Niger........* Dan Allah ki yi hakuri da rashin yawansa, ina jinyar yar muleka *KUTKALE* *(PRISON)* NA *SAJIDA* Marubuciyar DUK KARYAR KADA YAR MAHAUKACIYA DAGA TAFIA DAUKAR SOJA NEMAN NA KAINA BANI DA ZABI IDAN KA RAINA INDA KAKE BAK'A CE INA KUKE MASOYAN NOVELS DINA, GANI NA DAWO DA SABON SALO, SABUWAR TAFIA, NA ZO MAKU DA SABON NVL DINA MAI TAKE *KUTKALE* WATO GIDAN PRISON, WANNAN NVL ZAI ZO MAKU DA LAMURA DA YAWA, KU BIYO NI KU SHA LABARI........ *WANNAN NOVEL NA SIYARWA NE, DU MAI SO ZAI IYA TURA KUDINSA TA wannan acct NAIRA DARI BIYU : Usman Muhammad 3072998062 First bank. Sai ya turo shaidar ya biya ta wannan number +22791466605....sannan a yi adding dinsa cikin grup, MUTANENA NA NIGER KUWA SANADIYAR RASHIN SAMUN ORANGE MONEY DA KUKE YI, KUNA IYA TURO HOTON KATIN SAHELCOM KO NA AIRTEL TA NUMBER KAMAR HAKA 91466605 SAI A SAKA KU A GRUP DIN, .....* taku ce, Sajida 1 *HELLO READERS, DAN ALLAH KAR KU DAMU DA YAWAN PAGES, DU RANAR DA NA GA DA HALI ZAN KAWO MAKU 2, AMAN A HAKANMA KUN GA AI DA YAWA Irin dirar da ya yi ya kare ainahin wajen da ba.a son gannin da tawul dinsa kafin ya dafe goshinsa ya leko gaba dayansa yana daura tawul din ya dubeta irin yanda ta rintse ido, bata ga ainahin abinda ba.a son a gannin ba, aman ta ga cinyoyinsa, kai harma da kusan cibinsa ta gani, ga kirjinsa dake dauke da wani gashi tsakiya har zuwa cikin tawul dinsa, wanda da gangan yake aske sauran ya bar iya nan su wani bada kala, Kansa ya dafe da hannunsa ya fito daga bayin ya karaso inda take tsaye ya tsaya sosai daf da ita, ba abinda ya dame shi da irin yanda jikinsa ke bugawa sanadiyar wuni cir a wajen da sai shi kawai ya sani, ba wanka ba iska, gashi garjejen kato me zai hana shi bugawa? Ya dubeta da kyau ya ce" yanzu, fisabililahi, banda soyaya da dan ta.ada da kike wai harda neman gannin ogana? To me kike son ganni in ba fitina ba, Hafsat shekarunki duka duka 21 fa, kin shiga ta da biyu yau da wata hudu da kwana ashirin da biyu da awa ashirin da minti goma sha hudu da second tik tak tik tak tik tak......., yaushe kika san dadin namiji haka? A gidan yarin *KUTKALE* , ko a yawon neman fada lungu lungu? Ko dai da saurayin naki ne dan gidan abansa? Ko mijin da aka baiwa ke sadaka ya dana ne can dama a biye ba.a sani ba? Da sauri ta dube shi, duba irinnan tsoro, da fargaba, A hankali ta ce" kaka je neman labarina ne? Dama fitar da ka yi tawa ce? Wata dariyar da ya jima bai yi bace ta kubuce masa, kafin ya dubeta da kyau ya ce" du na rasa aikin yi, na tashi na fita zuwa neman labarin ki? Kin manta wanda ya dauko ki daga gidan yarin gaba dayansa a tafin hannu na yake? Kin manta yanzu duniya ta zama ta yanar gizo? Ina zaune sai da na gama hutawa, na shiga yanar gizo na bincika wacece ke, nan aka bani labarin da na kasa hadiyewa, dan haka ina zaunen nan ina shan shayi hankalina kwonce na danna kira aka bani cikaken wacece ke, duka a yan mintunan da basu cika sitin ba, wato awa! Yaya zaki yi tunanin darajar ki, ko haye min da kike zai saka har na yi irin fitar nan da na yi dan sannin ke ko wacece? Ba ke ce yar gidan malan ba? Wace kika ci sunnan mahaifiyarsa, kin taso cike da abubuwan mamaki, kin kare a soyaya da dan ta.ada da dan gidan dad? Abinda ya fi tsaye min a rai shine dan ta.ada, ta yaya? A ina kika gan shi? Na kasa yarda da hakan, ni ba sakarai bane da za.a bani wannan labarin na hadiye, ki sani wani labarin duniyar medias, da bakunnan mutane basu isa su baka ba, kamar yanda kika ji wasu abubuwan a kaina, baki isa a duniyar bincike ki san wasun ba sai dai idan ni na fda maki, haka naki labarin rayuwar ban isa na san wasu abubuwan ba, du irin fitinata da neme neme na, du karfina da dukiyata sai idan mai labarin ta fada da bakinta, meye sirrin rayuwar ki? Me ke damun ki? Me ya kai ki gidan yari da tsauri haka? Wace ratuwa kika yi a gidan yari? Yaya aka yi daga zama budurwar dan ta.ada kika dire a gagarumar bodyguard da kasa da mutan wajen kasa ke rububi? Kin zama karamar hamshakiya daga yar caskale, Hafsat, wacece ke? Idannuwanta ta bude daga lumshe sun da ta yi, ta zuba masa su, sun kara wani girma, sun cika da ruwan hawaye, haka kuma bakin na ciki ya kara girma, Sai da ta hadiyi yawu ya kai sau uku kafin ta dube shi da kyau ta kuma lumshe idannuwan nata ta bude a hankali ta ce" *ina ka je? Ka saka mu a balaki, ka bamu damar kawo maka talafi Abdul, ka taimake ni mu yi mu bar maka gidanka Abdul* Ta karashe maganar sosai tana mai sauke ajiyar zuciya, Gabansa ne ke ta faduwa, shi kam ya rasa wannan jarabar da me ta yi kama, du in zai kadaice ya yi koda maganar minti daya da yarinyar sai gabansa ya fadi, baya son faduwar gaba dan kuwa saka shi take jikinsa ya yi sanyi, komaima nasa ya yi sanyi, Haka ta juya ta fice a dakin ta jingina da kofar ta sada kanta kasa, a rayuwa daga bakin lokacin da ta
Chapter 5 · 0% Book details