← Book details Kutkale Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 59 OF 94

Sashe 59

Kutkale Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Tana haki da komai ta ce" Aba, ba guduwa na yi ba Abana, Abana ka min auren da du wanda ka zaba min na maka alkawarin da zauna da shi koda kuwa yankan naman jikina yake, Abana ka yafe min, ina mamana? Abana ka san inda aka kai ni? Ka san me aka min? Abana gidan yarin *KUTKALE* aka kai ni a matsayin wace ta yi laifi na zama budurwar dan ta.ada, Abana daga nan aka kai ni ..... *UWATA* ya fada cikin nutsuwa yana kallonta, Hannunsa ya saka ya share hawayenta sannan ya ce" Abdallah ya je ya fada min, Shiru ta yi tana kallonsa, sai a lokacin mamaki ya kamata na jin wai Abdallah ya je wajen mahaifinya ya fada masa wannan maganar, Ikon Allah, sai yanzu tunanin me ya zo yi asibitin ya dirar mata, Dubanta ta kai cikin dakin marar lafiar nan ta hango Abdul kuri su yake kallo Gabanta ne ta ji ya yanke ya fadi lokaci daya kuma ta damki hannun mahaifinta a hankali ta ce" Abana, ya farka Malan ya kai dubansa wajen Abdul din, ya ga gaba daya hankalinsa a kansu dan haka ya ja hannunta da niyar shiga da ita, sai dai ga mamakinsa hannun ne ya fara rawa ta kasa motsawa harma ta iya furta cewa" Aba Tsayawa ya kuma yi da mamaki ya kalli yannayinta, a hankali ya cika hannun nata sannan ya juya ya shiga dakin , sai dai ya kasa rufe kofar dan du ji yake idan ya rufe ba zai bude ya kuma ganninta a wajen ba BS ne ya zo ya yi mata magana fuskarsa a tamke hakan ya sakata bin bayansa suka je suka tsaya nesa da dakin, bai ce da ita komai ba sai dai shirun da ya yi shima yana kallon waje daya kamar yanda ya ga hankalinta ya raja.a dakin da mahaifinta da kuma Abdul ke ciki Tun da malan ya shiga ya nemi waje ya zauna, ba abinda yake karantawa Abdul sai girman hakuri mahinmancinsa da sakamakon da ake samu mai kyau idan an yi shi, Jarabawar da ya shiga mai girma da duhu ya ringa bashi baki da musalai da kuma ribar da zai samu idan ya yi hakuri da ita a hakan, Shiru ya yi yana kallon yanda Abdul ke kallon kasa bai ce da shi komai ba Ci gaba ya yi da bashi baki, da nuna masa kar ya dauki maganar cewa zai dauki fansa shima, hakan ba zai kai shi ga ci ba, ba zai samu wata nasara ba Abdul ya dago idannuwansa da suka yi jajajir da mugun nauyin da sukai masa ya sauke a kan malan Sai da ya hadiyi yawu mai daci da kuma yauki a hankali ya ce" ba komai *ABA, ALLAH YA JIKAN DU WA.INDA SUKA MUTU* Sai da ya ji zuciyarsa ta girgiza, ba komai fa yace? Tabas yana iya karbar abin aman ba komai din na lokaci daya ya bashi mamaki, ko dan yana cikin hali na rashin dadin yannayi shi sai ya ce kamar yau baya cikin yan magana ma, Ajiyar zuciya ya sauke ya mike da niyar fita, sai dai muryar Abdul ta dawo da shi cewa" Aba, Dama amini na zama makiyi? Aba dama alkhairi na jazawa mutun kiyaya? Aba, shin a gabanan zan iya yarda da wani dan adam komai kusancina da shi kuwa? Aba ashe aminina ya kashe min kanwata? Ya kashe min mahaifiyata? Ya kashe mutanen dake tare da ni? Du dan ya kai ni ga ciwon hauka kafin na bar duniya? Aba........zuciyata sai nake jin tamkar ba zata kuma gannin haske ba, ji nake tamkar na gama da farin ciki, idannuwana na gannin kowa da fuska biyu, *ABA, shin me zai saka na yarda da kai kanka?* Halin rudani na rudar da zukatanmu a likacin da wani lamari ya dake mu , sauki na Allah ne *KUTKALE* *(PRISON)* NA *SAJIDA* Marubuciyar DUK KARYAR KADA YAR MAHAUKACIYA DAGA TAFIA DAUKAR SOJA NEMAN NA KAINA BANI DA ZABI IDAN KA RAINA INDA KAKE BAK'A CE INA KUKE MASOYAN NOVELS DINA, GANI NA DAWO DA SABON SALO, SABUWAR TAFIA, NA ZO MAKU DA SABON NVL DINA MAI TAKE *KUTKALE* WATO GIDAN PRISON, WANNAN NVL ZAI ZO MAKU DA LAMURA DA YAWA, KU BIYO NI KU SHA LABARI........ *WANNAN NOVEL NA SIYARWA NE, DU MAI SO ZAI IYA TURA KUDINSA TA wannan acct NAIRA DARI BIYU : Usman Muhammad 3072998062 First bank. Sai ya turo shaidar ya biya ta wannan number +22791466605....sannan a yi adding dinsa cikin grup, MUTANENA NA NIGER KUWA SANADIYAR RASHIN SAMUN ORANGE MONEY DA KUKE YI, KUNA IYA TURO HOTON KATIN SAHELCOM KO NA AIRTEL TA NUMBER KAMAR HAKA 91466605 SAI A SAKA KU A GRUP DIN, .....* taku ce, Sajida 4 Jikinta ne ya dauki rawa gannin mamanta ta nufo motar, Kanta ta sada da sauri ta shiga murza yatsutsanta, ta saka a ranta ne tata ta kare, sai da ta yi mata nasiha, sannan tun da ta dawo kulun famanta nuna mata ta karyata abinda ake fadi a gidansu da kuma anguwarsu Shirun da ta ji ne ya sakata dan dago da kanta, Tsai ta tsayar da dubanta ga al.ajabin da take hange, Malan ne da amininsa ladan, da kuma mama a gefe tana amsa gaisuwar Abdul da ya duka har kasa kansa a kas yana gaisheta, Malan ne da kansa ya yi kiranta ta fito su gaisa da mutumen da Hafsat ta yiwa aiki Ita kanta tamkar wani sirikinta sai kara gyara zumbulelen hijabin jikinta take tana amsa masa cikin nutsuwa inda kunyarsa ta lulubeta dan ba karya abdul akoy cika ido da siffar kamilin mutun Sai da suka gama gaisawar Mama ta yi ciki kusa da yan uwanta, nan malan ya fara shiga ya ga kowace da shigar kamala ba wace ta yi shigar da zai ji kunyar nunata dan haka ya kara yiwa Abdallah iso ya shige suka shiga saman malan Gannin har an fito a sallar magariba sun kasa bata waje ko zata fito ya sakata ziro kafarta a hankali ta fita a motar da lipton din malan sai yar pos dinta Bata kula kowa ba ta shige bangarenta ta nufi dakinta Tana shiga ta fada bayi ta zauna ta shiga kuka, ita kanta bata san kukan me take ba, mari dai a gidan duniya ba kalar wanda bata sha ba, ta sha dukan balakima bare wani mari can? Sai da ta ji muryarta na shakewa sannan ta sasauta ta kunna ruwa ta wanke fuskarta ta dauro alwallah ta fito a dakin Sallah ta tayar cikin nutsuwa ta gabatar sannan ta mike saman bed ta kashe wayarta gaba daya ta shiga neman hutu Abdul kam sai da matan malan suka hau da kansu daya bayan daya suka gaisa, ya gabatar da shi a matsayin wanda Hafsat ke gidansu Ido ido suka ringa yi kowace na ciki na ciki har malan ya salame su suka fito a dakin Sai da Abdul ya kusan raba dare dan kuwa sun jima da malan suna tataunawa kan lamarin duniya, kafin ya mike ya sauko bayan sun yi salama da malan ya roki da ya yi zamansa ba sai ya raka shi ba A lokacin da ya sauko ya dan jima yana kallon kofar da ya tabata ita ce ta mama, kuma a ciki dakin Hafsat yake, Sai da ya ga daren na kara yi sannan ya juya ya fice a gidan ya tarda direban da ya kawo masa wata motar har ya fara baci bawan Allah ya tashe shi suka tafi Ko da suka karasa gida wanka kawai ya yi, ya gabatar da shafa.i da wuturi, ya gama adu.o.insa, har ya zo shafawa ya lumshe idannuwansa, wata adu.ar ya yi kamar haka" ya Allah, ka kare ni da mugayen mutane, Allah ka bani amini mai tsoronka wanda zan shiga aljanah dalilin zumuntar mu, Allah ka raba ni da mugayen mutane Bugun zuciyarsa ne ya ji na neman canzawa sakamakon kokarin tuno irin abinda ya faru tsakaninsa da Muhammad da kuma irin hukuncin da ya yi masa, da sauri ya dauki carbinsa ya shiga jan salatin annabi *MUHAMAD SALALAHU ALAIHI WA SALAM*, yi yake ba kakautawa, a hankali ya ringa jin nutsuwa na ratsa masa zuciyarsa har ya nemi damuwarsa ya rasa Bai tashi a wajen ba sai da ya rokawa malan gamawa da duniya lafia, domin shi ya bashi sirrin salatin annabi, da ba dan ya riki sirrin nan ba da bai san idan ransa ya baci ina zai tsoma ransa ya ji dadi ba Sai da ya kwonta saman bed dinsa, yana rintse ido ya ji passsssss Karar marin da ya sakar mata, Da sauri ya buda idannuwan nasa, Hannunsa ya daga yana kallo, hannunsa na dama wanda da shi ya mareta, A hankali ya mayar da hannun ya ajiye a fili ya ce" aman me ke damun zuciyarki Hafsana? Me ya sa kika zuran ido baki ce da ni komai ba? Na mare ki, na yi maki ihu a kai duka kina kallona baki bani amsa daidai da ni ba? Da gaske sunna mugun takura ki a gidan nan? In dai dalilinsu kike cikin yannayi na rashin walwala zan saka a yi maza a yi aurenki ko na maido ki nan a matsayin bodyguard dina har a maki aure ki yi tafiarki gidanki, Wayarsa ya dauko yana kallo, sunnan BS dake cikin wayar ya kurawa ido, Ya so ya rubuta masa message sai kuma ya fasa, Juyawa ya yi ya gyara kwonciyarsa da niyar idan ya kai gobe lafia zai nemi BS, zasu yi da wajewa idan ya auri Hafsat ya wulakanta masa ita walahi sai ya yi shara.a da shi! Dan rainin hankalin banza dan rainin hankalin wofi, dalilin wulakantata da Muhamad ya yi ba zai yarda kowani kato ya wulakantata a gidan aure ba, idan da hali zai saka camera dan gannin irin zaman da suke dan kar ya je ana cutarta a yanda ta zama lusarar nan yanzu ta rufe ta kasa fadi!!!!!!!!! (Sannu baba) Sai da mama ta gama salolinta ta shiga dakin Hafsat, nan ta tarar da ita ta yi wani kwonci a takure tana baci sai sauke ajiyar zuciya take A hankali ta shafi gefen fuskarya da ya tasa kadan, ya kumbura
Chapter 59 · 0% Book details