Sashe 70
Kutkale Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Allah da kudin haram ba! Ita dai mama tsayuwa ta yi sai da ta gama ta sakar mata hijab ta shiga daki Tana shiga ta ga wayam ba Hafsat, Da sauri ta daga kafarta ta shiga dakinta Tarar da ita ta yi tsaye, daga ita sai dan dogon wando da rigarsa sai kai kawo take, Yannayin fitina da neman balaki ya bayana a tare da ita Kallon tsaf ta yi mata kafin ta tabe baki, lale Hafsat ta raina mata hankali, kuma ta yarda da ake cewa likita ya fi kowa rikicewa idan abin ya shafe shi. Sai da ta gama kallonta sannan ta ce" ki lulube jikin ki, daga yanzu bana son na kuma ganninki ba da lulubi ba kafin a kawo magungunnan ki Da kallo ta raka maman nata, iyeah? Shi ne abinda ta fada Da sauri ta warto wayar nata, karfe goma sha biyun dare ne fa aman da yake ranar ta zo masu wani iri du gidan malan yara kananu kawai suka samu rintsa idannuwansu Wayar ta danna ta danna masa kira Ta yi ya kai sau hudu kafin ya daga da wata irin murya Sai da gaban Hafsat ya fadi domin muryar wani irin kasa kasa, sannan bata fita da kyau A hankali ya ce" Hafsat Hafsat ta kara rintse idannuwanta ta kai zaune saman bed din dakinta Niyarta ta daga murya ta darza rashin mutunci sai gata da sasauta murya ta ce" Abdul, dan me zaka min haka? Me na maka ne wai ni? Dan me zaka saka a aura maka ni bayan ka san da wanda ke so na yake shirin zuwa ya aure ni? Yanzu idan ya zo sakina zaka yi a kara aura min shi ko me? Abdul ya kara lumshe idannuwansa yana sauraronta , a nitse ya ce" *ni ban aure ki dan na sake ki ba* Me kake nufi da baka aure ni dan ka sake ni ba? Wani irin aure kake jiran yi da ni haka? Baka so na Abdul, bana son ka!, dan me ka min haka? Ta fada muryarta a sanyaye haka kuma tana rawa rawa Abdul ya sauke ajiyar zuciya, a hankali ya ce" *na san bakya so na, ban roki ki so ni ba, Hafsat baki ga lokaci ba ne ni? Lokacin neman nutsuwa ne, idan kuwa zaki iya....ina nufin idan har kin san kina bukata, a yau kin saka haka a ran ki .... sai na sauka daga nan na zo in hau naki bed din* Abdul ya karashe yana mai duban Na.ima dake kwonce kusa da shi Shiru ya ji wayar, ba magana dan haka ya dubi screen din, An kashe, murmushi ya yi yana girgiza kansa, dubansa ya kai wajen Na.ima, baci take kashirban, baiwar Allah, a gaskiya yana tausayinta, shi baima taba tunanin ta yanda zai fadi abu sai wannan lokacin Kwonciyarsa ya gyara yana mika, a hankali ya furta" *na san bakya so na Hafsat, na jima da sani....sai dai ba zan iya sakin ki ba, ke na yiwa rabon wani garaje dan Allah ya kashe ni kafin ya fito daga tsatson ki ....Hafsat idan na rabu da ke ni kuwa na rayu a yaya?* Bayan kwana biyu aka kawo lefen Hafsat Lefen da ya kara kashe bakin mutanen gidan malan kowa sai dai ya labe daga daki yana leke ba um ba umum, Anguwa du an dauka, maganar uwar malan kawai ake, da yawa na fadin alkhairin da yawa na kushewa Kwana biyar kennan da maman malan ke zaune da auren Abddallah a kanta, Bata kuma jin duriyar BS ba, haka kuma shi kansa abdul din daga daren da ta yi kiran nan nasa da ta kashe bata kuma nemansa ba A yau ta tashi ta gama shiri da sanyin safiya cikin nikaf da abin hannun da mama ta bata, shima an ce dole sai ta je da kanta gidan mai dinki ne, hakan ya saka mama ta ce maza ta je ta dawo su yi dilkar safe domin ko dilkar basu yi ba Har ta yiwa mama salama mama ta dawo da ita A hankali ta ce" kin nemi izininsa ne? Da sauri ta kalli mama cike da mamakinta, izini? Wai izinin wa? Mama ta daure fuska ta mika mata wayarta da aka karbe du idan za.ai mata dilka ake amshewar Amsar wayar ta yi ta kuma kallon mama gani ta yi ta tsareta da kallo dan haka ta danna wayar ta shiga kiran numbersa Sabon wulakancin da take gani ya dauka yanzu ne ya yi mata dan sai a kira na biyu ya daga sannan ya ki yin magana A hankali ta yi salama domin mama na kallonta ido cikin ido Amsawa ya yi yana mamakin salamar daidai ya tsaya wajen danja A hankali ta ce" an aike ni wajen mai dinki zan je na dawo Ajiyar zuciya ya sauke kamar wanda ya yi tsere, a hankali ya ce" ki jira Bai karasa ba ya kashe kiran , ta bi wayar da kallo Sarai mama ta fahimci abinda ya ce dan haka sai ta dauko kujera ta zauna a kofar dakin mama Ta kusan minti ashirin a zaunen nan, tana yi tana duba agogon wayarta tana kuma kallon hanyar fita Kanshin turaran da ta jiyo ne ya sakata yin shiru ta ki motsi A hankali yake takowa har ya iso inda take zaune Bai yi mata magana ba sai tura kofar da ya yi ya yi salama Da mamaki ta dago tana kallon wai da gaske dakin maman zai shiga? Yau ta ga ikon Allah, mazan yayunta basu taba shiga dakin mama ba sai yau shi bakon jiya zai shige har dakin mamanta Mikewa ta yi ta yi gaba dan har an fara leke, bata son a bata mata rai da safiyar nan Sai da ya gama gaishe su ya fito ya fita wajen Ganninta waje tsaye ya sosa ransa, aman bai nuna a nan ba ya bude ya shiga itama ta bude ta shigan A hankali ya tayar da motar ya dauki hanya Batai masa magana ba sai murza yan yatsunta da take, A hankali a hankali har suka karasa wajen da bata fada masa ba sai dai gani ta yi ya kaita ta tabata mama ya tambaya Fita ta yi ta shiga akai mata aune aunen da za.ai mata baki daya ta fito ta dawo motar Dagawa ya yi suka fara tafia, Suna tafiar ya canza hanya a hankali ya ce" bana so kina fita Hafsat, A hankali ta dan kale shi sai kuma ta kawar da kan nata Hafsat talk to me; Dubanta ta kai wajensa, sai kuma ta shiga shashekar kuka, Kuka take a hankali a hankali wanda ya saka shi ja ya tsaya a cikin kwanar da suka shigo sabuwar anguwar yan gayu ba wasu mutane a waje da yake safia ce sai jefi jefi du suna gida suna baci Mitar ya tsayar kasan wata shuka, A hankali ya karkata yana kallonta, Rufar fuskar nata ya dage ya cire mata baki daya yana kallonta Gashin idannuwanta sun yi gazar gazar da su, sun shiga idannuwansa har sun zarta A hankali ya fora yatsarsa saman girarta ya dan shafa kafin ya lumshe idannuwansa, Muryarsa ya sanyayar ya ce" menene? Hafsat ta dago da dubanta a hankali ta dube shi, Muryarta ta sanyayar ita din ma ta ce" Abdul, ina BS ya shiga? Abdul ya tsura mata ido, gabansa ne ya ji ya fadi lokaci guda, Bai yi shishigi ba kuwa? Bai sako kansa wajen da zai zauce ba kuwa? BS? Tare fa ka gansu Abdul, shin wannan damuwa da shi ka san da tana son sa, idan fa bayan so din Hafsan ka ta yarda da BS ne? Gabansa ne ya kara faduwa, hankalinsa ya ji ya tashi a hankali ya saka hannayensa bibiyu ya kamo fuskarta, Matso da fuskar tata ya yi ya samu da kyar ya hada ido da ita, A hankali ya ce"....... *KUTKALE* *(PRISON)* NA *SAJIDA* Marubuciyar DUK KARYAR KADA YAR MAHAUKACIYA DAGA TAFIA DAUKAR SOJA NEMAN NA KAINA BANI DA ZABI IDAN KA RAINA INDA KAKE BAK'A CE INA KUKE MASOYAN NOVELS DINA, GANI NA DAWO DA SABON SALO, SABUWAR TAFIA, NA ZO MAKU DA SABON NVL DINA MAI TAKE *KUTKALE* WATO GIDAN PRISON, WANNAN NVL ZAI ZO MAKU DA LAMURA DA YAWA, KU BIYO NI KU SHA LABARI........ *WANNAN NOVEL NA SIYARWA NE, DU MAI SO ZAI IYA TURA KUDINSA TA wannan acct NAIRA DARI BIYU : Usman Muhammad 3072998062 First bank. Sai ya turo shaidar ya biya ta wannan number +22791466605....sannan a yi adding dinsa cikin grup, MUTANENA NA NIGER KUWA SANADIYAR RASHIN SAMUN ORANGE MONEY DA KUKE YI, KUNA IYA TURO HOTON KATIN SAHELCOM KO NA AIRTEL TA NUMBER KAMAR HAKA 91466605 SAI A SAKA KU A GRUP DIN, .....* taku ce, Sajida 5 A hankali ya ce" kin kasance mai fadin gaskiya Hafsana, Ki fada min, a cikin mazan da suka ringa kawo maki hari shin shi ya samu galaba a kanki ko menene wannan damuwar da shi? Sai da ta wanna idannuwanta a cikin nasa sannan ta saka hannnayenta biyu ta janye hannunsa Sakar mata fuskar ya yi yana kallonta, a hankali ta ce" haba Abdallah, me zan yi kwadayi da zaman yau da kulun? Na zauna da kai Abdallah! Bana son irin rayuwar nan, rayuwar da ba kula ba yanci? Ni wa na fi da zan yi tunani ai ni ce zaka waiwayeni? Ni ta nawa ce? Abdul shin ka taba so a rayuwarka? So wani abu ne mai nauyi mai wahala, Abdul ni na taba so, so yakan saka mutun tsalake maganar manyansa, Abdul Bashir ya nunan so, ya bi ni sau da kafa...ya waka min, ya yi hakuri har na samu kaina sannan ya zo har gidanmu ya nemi soyayata da aurena Shin me ya tsayar da shi? Ina cike da zulumin abinda ya tsayar da shi mai girma ne, Abdul du irin zagina da ake a kulun sai ya furtan kalmar so Idannuwansa ya lumshe ya kuma budewa yana kallonta Sai da ta sauke ajiyar zuciya ta kale shi ta ce" ban san kansu mazan ba bale har na ware shi dan hakan! Ka kaini nesa Abdul, ka yi yawo da ni sama a zuciyarka ka ajiye ni