← Book details Kutkale Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 66 OF 94

Sashe 66

Kutkale Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

shine yanzu tsautsayin tozarci ya kai ka ga afkawa wajen da zaka tonawa kanka asiri ka tona min? Waima yar gidan wa ka je ka saka kanka a ciki da har ya saka shi tasowa da kansa da niyar yin bincike a kanka? Haushi, takaici hadi da kishin lamarin abdul ne ya turnike BS, haka kuma haushin mahaifinsa ya kama shi, shi ya san du abinda ya saka babansa a taro a taro din nan dan baya so duniya ta san ya haifi dan gaba da fatiya ne, aman ba komai zai nuna masa shi din ya iya iskanci A dake ya ce" yarinyar nan ce da ka kawo daga prison *KUTKALE* na horata ta zama bodyguard Da sauri ya kale shi, Kansa ya girgiza sannan ya ce" lale a mahaukatanma kai baba ne, ka san da shugaban kasar nan ya yi kira cewa a kurce sunnanta a matsayin mai laifi ko mai bashin kasa a kanta? Yarinyar da ta gagari yan ta.adar Kutkale? Yarinyar da ta fito lafia daga kutkale? Ta zo nan ta zama zakararsu? Yarinyar da ta tsare mutuncin kanta take adu.ar Allah ya tsareta? BS ya ce" wannan abinda take nuna mana kennan! Ni kaina da farko na dauka hakan ne, aman daga bakin lokacin da ta fara yiwa Abdul aiki na gane cewa itama watsatsar ce sai dai bata haraka sai da manya, yarinyar da ta bi Abdul kuma ta kare da abokinsa? Idan ba aikinta ba ta ya ta gane shi ne mai neman rayuwar Abdallah? Idan ba kwaratanta ba ta yaya muka tarda ita a yannayin da muka tarda ita? Ta raina arzikina ne, bata san ba wanda ta gama watsewar da shi ba aurentan zai yi ba! Eh na je gidansu, kuma ina son aurenta dan haka a aura min ita ba ruwan kowa Ikon Allah kawai yake kallo kafin ya ce" ka sani, ni kaina mai tsayawa shara.a da kai ne idan ka cutar da rayuwar yarinyar nan, bare na tabata ba za.a rasa mai iya wujijiga namanka ba, dan ka sani *yar kamilin datijo yar kuma baban gida ce*, yanzu fice min a motar nan tun kafin ka hadasa min wani ciwo! Bakinsa ya tabe, sannan ya fice a motar, yana kallo babansa ya shige cikin gidan horon da motarsa sannan ya kara tabe baki a fili ya ce" idanma iskanci ne ai gado na yi, kuma yan mata yanzu na fara haye ruwan cikin du wanda ta dagan buje! Itama wancen tunda na lura ba zan samu dan arzikina ba zan aureta na haye ruwan cikinta na ga meye banbancin sa da na sauran da har ake min iskanci a kansa, dama dama ni na zubar da cikin ban bari ta haifo min dan ba! Kai da ka haife nin sai na saka ka a uku! A haka ya gama magangannunsa na rashin kunya sannan ya aro fuskar jarumin namijin ya kutsa kansa cikin wajen da yana shiga du suka shiga bashi girma suna kauce masa har ya isa inda zai hori yaren Bangaren Hafsat bata ga wani canji daga wajen BS ba, yakan kirayeta su sha hirarsu, hirar soyaya, bai taba kauce hanya wajen yi mata hira ba, yakan nuna mata soyayarsa tsakani da Allah ne, tsantsar tausayinta da nuna mata so ya saka ta ita kanta fara shakuwa da shi, A haka har ya yi sauran kwana uku a kwanakin da Malan ya diban masa kan ya turo da magabatansa su zo neman aurenta da komai sai dai shiru ba.a irin daya daga cikin manyansa ya zo dan jin karin haske a batun Abdul kuwa, ya zamewa dangin Hasfat tashin hankali, bashi da lokacin shiga gidan malan, kowani lokaci ta raya masa zai zo gidan malan ne ya dauki kujeru ya ajiye kasan katon dalbejiyar gidan mai sanyin ni.ima wace da yawancin lokuta matan sukan zauna a nan aman kirikiri wajen ya haramta wa su sai dai su hade a daki hajia uwar gudan malan su yi abinda suke yi a labe, abin na basu mamaki, na basu takaici irin yanda malan ko yayan cikinsa bai sake masun da zasu ringa shiga gidansa a lokacin da suka yi ra.ayi ba ko dan yayansa mata aman sai gashi wani garjejen kato dan kawai hannunsa na rike da hatimin nasara ya mayar masa da gida wajen zama sannan ya saka wannan tsaura idon a gaba har ka ringa hango hakoranta tana washkala dariya , dariyar da ba.a san me yake ce da ita ba, duda rabonta da ta yi wata shiga ta ba daidai ba tun da ta dawo aman ai ba daga shigar mutun abin yake ba! Fitowa ta yi daga dakinta cikin nutsuwa ta shiga dakin mahaifiyarta, Yayarta ce zaune tana ninke kayan da aka wanke kafin a kaisu guga , yaronta kuwa yana can cikin kuryar dakin da mahaifiyarsu tana neman kaeanfanin da ta saka aka siyo mata mai yawa ta raba biyu fan baiwa yarinyar nata rabi dan anfaninta sai wasansa yake ita kuwa tana taro shi Da murmushi ta karasa kusa da yayar tata ta zauna itana ta dauka ta kade ta shiga ninkewa, Kallonta yayar tata ta yi tana murmushi ta ce" amarya amarya Itama kallonta ta yi, ta kawar da kanta a hankali ta ce" aunty gabana na yawon faduwa a duk lokacin da kika kirayeni da wannan sunnan, wai dama nima zan yi aure? Na auri mai sona haka? Harma na yi tunanin samun yanci? Murmushi ta yi, ta ce" bawa baya cire rai da rahamar Allah, koda ace zaman kanki kikai kika hayayafa Allah zai baki malamuncinki bale yanda kowace y'a take haka kike? Ina so a kaiki gidanki da raina da lafiata auta, zan so na ga takun rayuwae aurenki na tafia cikin salama Murmushi ta yi har hakoranta suka bayana fili , sai kuma ta sada kanta irin ta ji kunyar nan Shigarta yayar tata ta kala, sabuwar abaya ce mai ruwan ja mai duhu ta yane kanta da dan kwalin abayar, ta yi kyau karshen kyau a haka bata shafa komai ba koda kwali ne Tana shirin yi mata magana sai ga mahaifiyar tasu ta fito, kallonsu ta yi kafin a hankali ta ce" Anmih, yaya haka? Wancen bawan Allahn ba ke yake jiraba? Bakinta ta dan cuno gaba ta ce" mama, fada fa mukai da shi jiya a eaya shine yau zai wani zo min haka kawai mutun sai neman fitina bayan na fada masa ya fita a harkar yan gidanmu, cewa fa ya yi zai zane yaya fa, kuma a gabansa da gaban hajia, kuma ya fadawa Aba cewa wai shi ya girmi yaya aman ya shigo gida bai gaishe shi ba shi zai xane shi idan ya ci gaba da yi masa rashin kunya, yanzu mama tsakani da Allah abdallahh ba zai shiryu ba? Yayanmu mu duka gidan zai zane? To mu mu shiga ina da ranmu? Baya gudun rigima sam, sai kace gidansu wai ya shigo gida bai gaishe shi ba Ta karashe tana turo baki Dariya auntynta ta saka sosai har tana rike cikinta, ta nunata da yatsarta ta ce" zan so na ga idannuwan hajiar gidannan, wai wai wai za.a zane mata elhaji a gabanta, kuma a cikin gidan ubansa Mama ta harareta ta ce" ke ba zaki girma ba ko? Bana so Ki ce da Abdallahn ni nace dan Allah ya yi hakuri ya daina biyewa kowa a gidan nan, idan kuwa dukan ne ya daki anmih dan kuwa ke ce bakya jin magana, maza tashi ki je ku zauna dan na tabata zaman nan da bawan Allahn nan ke yi a wajen nan dan kawai ya tare maki rigimarsu ce, kin ga kuwa da sauki dan ni kaina an jima ba.a zage ni ba bare ke................. *KUTKALE* *(PRISON)* NA *SAJIDA* Marubuciyar DUK KARYAR KADA YAR MAHAUKACIYA DAGA TAFIA DAUKAR SOJA NEMAN NA KAINA BANI DA ZABI IDAN KA RAINA INDA KAKE BAK'A CE INA KUKE MASOYAN NOVELS DINA, GANI NA DAWO DA SABON SALO, SABUWAR TAFIA, NA ZO MAKU DA SABON NVL DINA MAI TAKE *KUTKALE* WATO GIDAN PRISON, WANNAN NVL ZAI ZO MAKU DA LAMURA DA YAWA, KU BIYO NI KU SHA LABARI........ *WANNAN NOVEL NA SIYARWA NE, DU MAI SO ZAI IYA TURA KUDINSA TA wannan acct NAIRA DARI BIYU : Usman Muhammad 3072998062 First bank. Sai ya turo shaidar ya biya ta wannan number +22791466605....sannan a yi adding dinsa cikin grup, MUTANENA NA NIGER KUWA SANADIYAR RASHIN SAMUN ORANGE MONEY DA KUKE YI, KUNA IYA TURO HOTON KATIN SAHELCOM KO NA AIRTEL TA NUMBER KAMAR HAKA 91466605 SAI A SAKA KU A GRUP DIN, .....* taku ce, Sajida 5 Aunty kam murmushi take ita kuwa ta karasa ninke na hannunta ta juya tana tura baki gaba waima kar ya ga damarta ta fice a dakin Murmushi aunty ta yi tana duban mamansu ta ce" ina mamakin shakuwarsu, mutun baban mutun irin wannan, da farko aban Fahad na fada min ko shi waye a kasar nan na ji tsoro ko wani abin yake kawo shi gidannan? Sai dai irin yanda mu.amalarsa da malan da kuma ita kanta Maman malan abin sai ya fara yi min haske, a hankali na gane shi din ne mai saukin hali domin kuwa da akama shi ya saka maman malan nutsuwa Tun da ta tunkaro inda yake zaune ya tsayar da danna wayar da yake ya tsura mata ido, Yanda ka san ta zauna ta tsara yanda halitarta zata kasance mata , Daga sama ba wani mugun tudu aman daga kasa ko batai niya ba sai sun shaida kansu Kawar da kansa ya yi, dan baya so ya ringa irin wannan tunanin, yau dai alhamiss ce in sha Allah a gobe za.a zo tambayar aurenta a yi a gama shikenan A haka ta karaso ta zauna bayan ta yi salama ciki ciki Shareta ya yi ya ki amsa salamar a bayane saima ya fitar da wayar ya ci gaba da dadanawa Ta kai dubanta kansa ya fi a irga , sai da ta gaji ta ce" meye? Shiru ya yi mata ya ki kallonta Hafsat ta ce" Abdallah, menene wai? Dago da kansa ya yi, ya zuba mata manyan idannuwansa masu zama da launin ja kusan koda yaushe sannan ya ce" Hafsat,
Chapter 66 · 0% Book details