← Book details Kuskuren Baya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 98 OF 160

Sashe 98

Kuskuren Baya Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

“Anas tunanin me kake yi haka har muka zauna bakasani ba?” yayi firgigib ya dawo haiyacinsa kana ya sauke ajiyar zuciya “rayuwa !
Ya bashi amsa da hakan yana runtse idanunshi “rayuwa ?!
Jaguwa ya tambayesa yana dubansa sky ya mike domin jin abinda anas ya fada yayi gaba kadan ya fito da kwalin sigari ya zari daya ya kuna ya kai bakinsa “
“Adnan ! ya kira sunansa bai amsa ya cigaba da kallonsa alamun yana sauraronsa “nagaji da wannan rayuwar me zai hana mu barta mu tuba domin samun rabauta da kuma hawa tudun tsira mu tuba jaguwa daga …..”saurin daga masa hannu jaguwa yayi “zamuyi maganar idan mun koma gida but for ka dawo daidai banason ganin wannan yanayin a fuskarka ka tashi kaje kayi wanka yana gama
fadar hk ya mike ya karasa inda sky yake yana ganinsa ya saki sigarin hannunsa yasa kafa ya murje suka cigaba da zantawa har kusan karfe biyun dare da zai wuce aka sake fitowa da ajirebi byn an rufe masa ido aka sake turasa a byn boot aka nufi area 1 dashi a bakin wani madaidacin gida yayi parking eku da sky suka fito suka shiga dashi ranar yaga tashin hankali ganin idanunshi sannan yayi kwana tashin hankali yadda yaga rana haka yaga dare dayasani sani kuwa yayi sa yafi sau babu adadi inda zaa sake dawo da tarihin rayuwarsa da babu kudin wanda zai ci .”
Washegari 1:dot a gidan tayiwa su jaguwa da abokansa kallo daya yayiwa ajirebi wanda ya fita haiyacinsa sannan yace”kamil ina wayarsa?”Kamil ya ciro ya mika masa “amsa ka kira daya daga cikinsu galadima ko garunmallam jikinsa na rawa ya amsa yayi dialing number galadima jubi ya amshi wayar yasa a hands free kira daya ya dauka “hello ajirebi wai kana ina ne jiya byn mun gama waya nayita kiranka baka dauka fatan dai Lfy”?
“Lafiya kana ina ne ?”
Shiru galadima yayi kafin daga baya yace akwai abinda zan maka ne ?”ya fada saboda yana yin dayaji muryarsa “uhm daman …..”
Kit galadima ya katse kiran jaguwa ya fusata “haka ake magana da mutun ?ga dukkanin alamun ba haka suka saba magana ba allah yasa bai fahimci wani abu ba inji cewar anas jaguwa ya bugi table din dake dakin da karfi wanda yasa gbdy kayan dake kai suka hargitse har mutanen dake gurin most especially ajirebi dan tuni ya saki fitsarin wahala“wallahi ka kirasa kayi masa magana yadda ya dace muci nasara if not zaka bakunci lahira yanzu “kayi hakuri dan allah karka kasheni zanyi mgn da kyau banyi wani abu da zai gane cewar akwai damuwa ba,zaka san baka yi wani abu da zai gane ba oya sake kiransa inda yake kawai muke bukata” jikinsa na rawa ya sake kiran layin tare da sakata a hands free cikin saa galadima ya d’auka wani naunayen numfashi jaguwa ya sauke “sorry muna magna naji motsin shigowa shine na katse naje na duba kasan dole yanzu mu dinga be careful saboda wadan nan yan iskan mutanen ,“haka ne ajirebi ya fada yana sake danne tashin hankalin da yake ciki .
“Kana ina ne yanzu ina son nazo na sameka dan gbdy a tsorace nake “wata mahaukaciyar dariya kwashe dashi “tun bakaje hannu ba ka fara tsorata ai ka manta da inda nake kawai dan bazan fada maka inda nake ba kai dai ka fada min kana ina nazo” naunayen ajiyar zuciya ajirebi ya sauke domin rasa abinda zai ce .

jaguwa ya amshi wayar ya katse yana kiran sunan sky “kayi mana tracking inda yake nan da nan sky ya amshi number ya fara aikinsa dayafi kwarewa akai cikin kankanin lokaci ya gane inda yake ya dago a tsanake ya dubi jaguwa “boss yana ma kusa da nan yana area 11 ,good fito da hotonsa ajirebi ya fito dashi ya nuna musu suka amshi wayarsa suka dauke hoton galadima da wayarsa dan wayar ajirebi iPhone ce mai face id bazai yiwu su tafi da wayar ba dole sai da fuskarsa zata bude .
Location din unguwar da trancking ya basu suka bi tafe tafe har kusa isa kofar gidan get din gidan a kulle alamun babu kowa ciki
“anya kuwa gidan ne “? tabbas gidan ya nuna min ,wannan gidan babu alamun akwai mutun hasali ma garkeme yake “.
“Bari na sake dubawa ya maida idanunshi akan system byn minti biyar ya dago kansa “allah boss gidan duba kagani jaguwa ya kalla,tabbas gidan ne ya fito daga cikin motar ya jingina jikinsa da mota tare da crossing leg’s dinsa yana duban gidan a tsanake kafin a hankali ya fara shawagi agurin har kusan awa biyu babu wani wanda ya fito daga cikin gidan ko wanda zai shiga ya tsaya cak yana jan tsaki sannna ya bude gaban mota ya shga ya zauna yayi baya da kujera “yanzu boss ya zaa yi “?
“I dont know ya fada yana runtse ritattatun idanunshi wani duhu ne ya tsarke qirjinsa zuciyarsa na sake bushewa yanzu da bai tsaya ya amsarwa yaran nan dukiyarsu ba da a karshe sai sun yi bara a bakin titi, kai mutane babu imani aransu an kashe musu mahaifi baku barsu sunji da wannan radadin ba kuka dannewa yara dukiyarsu wannan wace irin rayuwa ce fi sabilila?”
Har kusan karfe duhu suna gurin jaguwa na zaune acikin mota kamar gunki takun tafiya suka ji ta glass din motar ya hango wani matashi bai tsaya akoina ba sai kofar wannan gidan ya ciro makulli daga cikin aljihunsa ya bude get mai layi layi dan daga waje zaka iya hango haraban gidan ya shiga ya maida kofar ya kulle ya bi hanyar baya “me ka fahimta anan “?
Sky ya danyi shru na second biyu yana nazari sannan yace”da alamun akwai mutun aciki gidan baddda kama akayi ta hanyar kawar da hankalin mutane shiyasa idan zaa fita sai a kulle ta baya hakan bazai sa mutane su fahimci akwai mutun aciki ba.”
Yana rufe bakinsa mai gadi ya fito ya zauna akan karamin banci ya ciro wayaraa yana dubawa,cike da jarumta suka fito gurin mai gadi suka nufa jaguwa ya mikawa mai gadi hannu shma ya mika masa suka gaisa “dan allah ko galadima na ciki ?kai tsaye suka tambayesa domin ya tabbatar da sun San shi.
“su waye ku?ya tambayesu shima,“abokinsa sani fafe ne?mai gadi yayi shiru yana tunani can yace “ ku kirasa tukun dan bai fada min zaa zo nemansa ba “kenan yana ciki?kwarai kuwa yana ciki amman bazan bari ku shiga ba sai da izininsa dan haka kirasa zai kirani sai na bude muku mai gadi ya fada yana kokarin komawa mazauninsa wani kallo ka kama kanka sky yayi masa sannan ya daga rigarsa sama kadan bindiga idanun mai gadi yaci karo dashi ya zaro ido waje ya durkushe kasa bisa gwiwowinsa “kuyi hakuri ai ban san ku bane ,kun ga ba sai kun kirasa ba kuzo ku shige kawai allah ya baku saa cikin rawar jiki ya bude musu suka shigo “can zaku bi akwai kofa da zata kaiku inda yake suna gama jin bayanisa suka amshe wayarsa sannan suka turasa cikin karamin dakinsa suka rufe sannan suka nufi hanyar daya nuna musu a hankali suka iso bakin wani iron door sukai knocking galadima dake zaune rike da jarida ya mike tsaye ya dawo bakin window ya tsaya ya yaye labule kadan ya leka yaga mutun biyu a bakin kofar bai san kamaninsu ba hasalima ranar ya fara ganinsu dan haka yaki budewa ya soma kira police .
“zaka bude mana kofa cikin girma ne ko zaka bata mana lokaci ne? Yana Jin’s yaki budewa gashi number police yana kira sunki dauka nan ya fara neman layin Alhaji sani cikin saa ya dauaka “dan allah ahj sani ka taimakeni ka kiramin police gasu nan sunzo gurina ….”
“idan ka bari muka balla kofar muka shigo zamu fanshe wahalarmu “.cikin galadima ya duri ruwa sai dai yaki budewa, suka yi amfani da kwarewarsu suka balla kofar suka gansa yayi mutuwar tsaye ya tsaya yana kallonsu saboda tsananin tsoro da kyar yake fitar da numfashi suka
shiga suka rufesa da duka
Sai daya daku sosai sannan suka nuna masa bindiga “Ina kudin marayu ?!
Tambayar da jaguwa yayi masa kenan babu musu ya fada musu inda suke “suna ckin motata a kasan motata na jerasu.
“wai ku masu wayo ba wannan kudi bazaku cisu ba ko sun cuyu sai na tabbatar da an dawo dasu hakane boss yanzu motar tana ina“?
Tana byn gida suka tasa keyarsa da bindiga sukayo waje “kar yaku ta kare sauran wacan dan iska shegu azzalamai kawai gbdy zuciyar galadima cike take da tsoro har suka isa inda motarsa take jikisa na rawa ya bude motar ya dinga zaro dalolin kudi suna tsaye aka shi har ya fito dasu duka basu barshi haka ba suka tasa keyarsa suka wuce dashi suka hadashi da ajirebi suka dauresu sannan suka kama gabansu suka barsu da sky da eku ”.

******
Chapter 98 · 0% Book details