← Book details Kuskuren Baya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 131 OF 160

Sashe 131

Kuskuren Baya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

wani irin yanayi ya shiga    mai wuyar misaltuwa sosai tsigar jikinsa ke mikewa  ,ta kwantar da murya sosai tana fada masa zantuttuka masu sanyi da ratsa sansar jiki ,sosai ta dinga zayyane masa muraran qaunar da take masa ,a hankali ya fara jin jikinsa yana samun sauyi tamkar ana  masa wanka  da ruwan sanyi ,cikin mintuna da basu wuce goma ba komai nasa ya sake  sauyawa  maganarta ba iya gangar jikinsa kawai ta tsaya ba har  kunnuwansa sun daina fahimtar maganar kowa sai nata ,suna cikin  haka ya jiyo sautin muryar mahaifiyarta tana kiran sunanta "habibi I will call you back " ta fada tana katse kiran ."

ya dan lashi lip's dinsa na  kasa yana mai maimaita sabon sunan data kirasa dashi  a saman lip's dinsa "habibi! ta yadda babu mai ji "Oh my god tanwer  allah yasa karki zautar dani ,gbdy hakurina ya kusan karewa akanki ,ya  ajiye wayar hannunsa akan table din gabansa ya had'e hannunwansa guri d'aya ya tsarkesu yana sake lumshe rikitattun idanunshi anas ya sauke numfashi tare da d'auke bakin bindiga akan alhaji tahir ya kai goshinsa batare daya ce komai ba  ,a natse jaguwa ya d'auki kwalban wine da d'an yatsantsa ya mike tsaye a rikice  cikin tsananin tashin hankali duk suka dukar da kansu kasa kar kwalbar ta subuce a yatsansa ya samesu ,ya soma  tafiya a hankali dan kar kwalbar ta subuce ta fadi ,duk suka d'ago kansu suka juya suna dubansa yana yawo acikin lambum cike da matsanancin mamakinsa  dan basu ta'ba ganinsa cikin wannan yanayin mai tattare da shaukin soyayya  ba ."

sun sha jin ana's na fad'a masa cewar ya fad'a soyayyarta  amman sai ya karyata hakan  ,yau dai  ga zahiri sun gani da idanuwansu bai  kuma isa  ya  karyata  hakan ba,ahankali ya juyo still da kwalbar a d'an yatsan hannunsa yana gama juyowa kwalbar ta fad'i akan table dake tsakiyarsu gabadayansu suka ja da baya da sauri sukayi ta kansu shi kuwa dafe goshinsa  yayi yana runtse idanunshi  ya koma mazauninsa ya zauna dafe da  keyarsa da hannunwansa duka yana fesar da numfashi bai ma lura da halin da suke ciki ba ,anas ya cire bindiga a goshinsa dan tun daya dafe goshinsa da bindiga bai cire ya kalli jaguwa  daga diramar soyayyarsa ba sai yanzu ,ya waigo  inda yake zaune yana murmushi yayi  masa kallon tsaf gbdy baya cikin haiyacinsa,
suka shiga kallon juna  ,gano yanayin baya cikin haiyacinsa yasa suka sake tattara hankalinsu garesa suna kallonsa har nazifi ."

ganin yadda gbdy  jaguwa  ya susuce  tare da lulawa duniyar tunanin soyayya yasa anas ya maida hankalinsa sosai a kan nazifi "za,a d'aukeka yanzu a fitar da kai yau daga gidan  nan ,zaka koma gidanka  ka cigaba rayuwarka da lamuran gabanka kamar yadda ka saba ,kasa aranka  cewar babu wani baraza da za'a sake yi maka ko kawowa zuciyarka farmakin boye an gama da wannan matsalar "ya karasa maganar yana kiran sunan eku !.
"Yes boss ya amsa masa cike da girmamawa da yake da haka suke kiran gbdynsu ,"ka tasa keyar wannan mutumin  ka mai dashi inda ka d,aukosa har zuwa lokacin da shi wannan zai dawo haiyacinsa asan yadda za'a yi dashi anas yayi maganar yana nuna alhj tahir dake rakube  wanda ruwan sama dake sauka  ahankali ya gama jika masa kayansa da jaguwa  wanda bai san a duniyar da yake ciki  ba ,
Batare da bata lokaci ba eku ya tasa keyar alhji tahir gaba suka nufi bangaren bq ya bude dakin daya kasance nashi né shi kadai  ya turasa ya janyo kofar ya rufe sannan ya kulle kofar da mukulli ya juya . "

Nazifi ya dube anas fuskarsa cike da matsanancin farinciki yace "na gode sosai  ranka ya dade  allah yasa ku gama da duniya lafiya ,allah kuma ya jikan iyayenku  idan sun  riga mu gidan gsky idan kuma suna raye ,allah ya kara musu lafiya mai amfani "Ameen suka had'a  baki gbdy ,amman  ranka ya dade wayata dake dauke da sheidu akan dady fa ?"Karka damu a yanzu zamu kwashe komai dake ciki mu baka wayarka ,sheidu zai cigaba da kasancewa agurinmu  ne kawai , gyada kai nazifi  yayi dan ya yarda dasu dari bisa dari a dan zaman da yayi tare dasu ya amince bazasu yaudaresa ba tunda ga kamanin  alhji tahir nan   ya canza ba sai an fada masa ba a inda aka ajiyesa muguwar wahala yake sha  ."wanda shi bai sani ba ba iya alhj tahir ne kawai ke cikin wannan halin baka'i zaune acikin gidan ba suna dayawa ."

a hankali ya  dan juya yana satar kallon jaguwa da shaukin soyayya ke dibarsa yana son yayi masa sallama da karin godiya akan taimakon da yayi masa mman babu halin yin haka , ya juyo da hankalinsa ya fuskanci ana's yana cewa "ranka ya dade ina da wata yar tambaya da zanyi maka idan bazaka damu ba ?karka damu kayi tambayarka Ana's ya fada yana bawa sky umarnin ya kwashe komai daya danganci sheida akan alhj tahir acikin wayar nazifi ya kawowa nazifi wayar ,ya juya da sauri ya bar gurin domin aiwatar da abinda aka sakashi."

"Tambayata shine ku din su waye domin ya kamata nasanin kafin na bar gidan nan dan ina komawa  gida dole yan'uwa da abokan arzikina zasu so suji komai daya faru dani ,sannan zasu so suji su wadan ni mutane ne  suka taimaka min  jami'an tsaro ne ko kuwa akasin haka?"kada  kayi mafarkin fad'awa kowa komai daya faru da kai dan bama son asani shiyasa ma muka rabaka da sheidar hannunka, bama bukatar kowa yasan su wayemu dan duk aikin da zakayi dan allah bai dace wasu su sani ba .
nazifi yayi shiru yana sauraransa yana nazarin maganarsa só yake ya gano gaskiyar su din su waye ga bindigu kala dabam dabam agabansu  kamar jami'an tsaro kamar kuma yan fashi da makami a shigowarsa gida yaga abubuwa dabam dabam duk da  a killace yake amman ya kan leka ta window  dakin daaka masa masauki idan yaji motsi, mutane dabam dabam suna shigowa gidan  idan kuma dare yayi yana jin Ihun mutane suna kuka da neman dauki wanda ya rasa dalilin haka  ,sannan yanzu haka gashi agabansu amman bashi da dalilin sake antaya masa wata tambayar yaja bakinsa ."

yayi shiru yana kallon cikin lambun yana saka da war wara acikin zuciyarsa gargadin da anas yayiwa alhj tahir ne dazu ya shiga dawo masa daya bayan daya yana samun kyakkyawan mazauni acikin kwakwaluwarsa "lallai su din sunfi kama da yan fashi da makami  abinda  ma zuciyarsa  yafi yarda dashi  kenan sune sukayiwa mahaifin tanwer fashi sannan suka wuce daita  na tsawonlokaci , idan ba haka bane a ina suka san alhji tahir ? me ye kuma hujjarsu nayi masa gargadi akansa? tambayar da yayiwa kansa kenan wanda bashi da mai basu amsarta .shiru  ya cigaba dayi agurin  yana sake yiwa tunaninsa dalla dalla  lallai so yake ya gano wani abu a tattare dasu  da zai bayyana masa gaskiya sai dai duk dogon tunaninsa da nazarinsa bai hango  abinda zuciyarsa ke zarginsu akai ba dan kuwa  babu ta inda sukayi kama da yan fashi ,idan kuma sun tabbata yan fashi ne to kuwa nasu fashin mai kyau ne da adalci "to ma ina tanwer din take ?tambayar da zuciyarsa ta sake aikawa kwakwaluwarsa kenan har ya bude  baki da niyyar yi magana sai kuma ya fasa yaji kamar an saka superglue ya manne masa baki ne ."

cikin kankanin lokaci sky ya dawo  hannunsa rike da wayar nazifi ya mikowa anas shi kuma yace ya mikawa nazifi ,ya karba yana sake yin godiya  sannan anas ya bawa scorpion umarnin ya kai shi gida atare suka mike suka soma tafiya ,yayinda gbdynsu suka tsura wa jaguwa idanunsu suka cigaba da kallonsa eku sky suka kallesu sannan suka kalli jaguwa  tare da kwashewa da wata dariya garin subawa juna hannu dan su kashe suka bugi table din gabansa nan take glas cup's din dake ajiye akai suka tarwatse ,bugun table din ne ya dawo da hankalin jaguwa jikinsa ya kuma ankarar dashi halin da yake ciki  "Am ranka ya dade daman haka idanunka suke ?" "Sosai ya sake dawo wa haiyacinsa yana dubansu fuskarsa tattare da alamun tambaya "lallai wannna soyayya hakika ta tabbata sosai  jabir ya fad'a yana murmushin tsokana" da wa kenna?jaguwa ya tambayesa  ya dan kallonsa  idanushi still  a lumshe tamkar wani mashayi "da kai mana idan ma ba kai ba wa za'a nunawa irin wannan soyayyar ? "uhm ka duba dan allah sai kace ita  din ba diyar  minister  ba,  idan tana yin wasu  abubuwa  sai ka dauka ita din ba diyar  babban mutun bace ,amman kowa ya ganta yasan yar gidan manya  ce jubi ya fad'a yana kwashewa da dariya."

"Nata kuke gani shi fa ?gbdy ya canza tamkar ba jaguwa ba ,yau dai kowannenmu ya gano wani sirri atattare dai kai ba kuma ka isa ka mutsa mana ba ,mu dai zamu maka fatan alkhairi dan gaskiya jaguwa ka dace kaji dadi  wallahi karka tsaya sanya ka duba yarinya irin wannan haka amman ta makale sai kai  congratulations kamil ya fada yana mika masa hannu yana sakar masa murmushi amman kememe jaguwa yaki bashi hannu dan wani mugun haushinsu da haushin kansa yaji ."

"yanzu dai ku me kuke tunanin abun zai  kasance ? jaguwa ya mike tsaye cike da jin haushi  "kai dan allah kuyi min shiru karku dame ni da wata magnr soyayya"  ya soma tafiya anas yabi bayansa da ido cikin jimami kawai yana kallonsa ko har sai yaushe zai fahimci halin da yake ciki ?yana gudar masa randa soyayya zata wujijigashi tayi waccajali dashi ,
yaso yadda ya samu damar nan  yayi amfani daita "kaji abinda yace Ana's wai kar mu damesa a zuwan ba gskiya bane ?"Haka zai ta nuna mana anas ya fada tare da kokarin mikewa tsaye "ina ma zanga wannan yarinyar dana fada mata ta rabu dashi da fita rayuwarsa wallahi zai fito da abinda ke ransa "bazata iya ba domin ba irinsu jaguwa mace
kewa irin wannan wasan ba , ko kun manta cewar shi din dokin tsare ne  ya fada yana cigaba da tafiya ya nufi hanyar fita daga cikin lambum."
Chapter 131 · 0% Book details