← Book details Kuskuren Baya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 36 OF 160

Sashe 36

Kuskuren Baya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

A hankali ya shiga  d'akinsa  Kai tsaye  had'ad'd'en  bayinsa ya nufa ya  tsaya  gaban mirrow Wanda ke hade da  washing hand basing ya fara  wanke fuskarsa a hankali qirjinsa na wani irin bugawa da karfin gaske , sai da yayi minti biyar duke sannan ya d'ago fuskarsa kwance da ruwa,  fuskar  nan nashi a had'e tamkar hadari ya tsurawa  mirrow bayin Idanunsa  yana  kallon kyakkyawar  fuskarsa yana zurfafa tunanin yadda zai yi da tanweer arayuwarsa shi kansa ya fahimci yarinyar ta fara tasiri a zuciyarsa amman zai yakiceta ta karfin tsiya  .a naste ya soma daga kafafunsa ya fito zuwa falonsa  ya karasa  gaban fridge ya bude ya tsurawa lemunka dake jere  idanunshi  yayinda zuciyarsa ke tafarfasa da quna   baya jin daya daga cikin lemunka zasu sanyaya masa zuciya yana Jin kamar yasa akawo msa giya mai  sanyi ya kwankwad'a ko zuciyarsa zatayi sanyi ,sai yanzu yake nadamar sanin ko shi waye da tayi shiru yayi  agurin yana tunanin mafuta ."

Ita Kuwa tanweer sai data ci  kuka  mai isarta sannan ta tashi ta fad'a bayi ta cika bathtub da ruwa ta shiga ta kwanta lamo cikin ruwa tana sauke ajiyar zuciya ta d'auki tsawon lokaci tana tunanin yadda zata gudu ta bar gidan "idan na tafi ya zanyi da matsanacin soyayyar da nake masa ?tsaki taja" soyayyar banza karki yarda ki biyewa wata  soyayya ki cutar da kanki  ,a yanzu tsana ce ya kamata  ya maye gurbin soyayyar,  ta dade acikin bayin   sannan  ta fito daf da magariba , yana shigowa tana fitowa daga bayi  ya tsaya  ajikin kofa d'akin  yana aika mata da wani irin kallo  me kashe  gabobin jiki ,kallonta  yake yana kallon santala santalar cinyoyinta dake fitar da sheki .
a hankali yayiwa Kansa mazauni agefen gado tare da jingina rabin jikinsa da filo yayi mugun tsura mata Ido , kallo d'aya tayi masa ta d'auke idanunta akansa qirjinta na wani irin bugawa da karfin gaske ,a halin yanzu  kallosa ma   storon  yake bata ko ma tace  bata qaunar ganinsa kyawun  dan  maciji garesa tunda babu hali  ,  cikin sauri ta d'auki  kayanta ta sake shiga bayi.
shiru  yayi   zaune  yana kallon d'akin har  kusan bakwai  da wani abu  bata fita ba , ganin bata da niyyar fitowa ga lokacin sallah na ƙoƙarin wucewa  ya tashi ya fice  .."

*****
Da misalin karfe tara na dare  ya shigo d'akin sanye da kananan kaya army green  riga da  wando  three quarter ,kafafunsa sanye da farin  silifas , hannunsa d'aure da agogon silver  sai kamshi jikinsa yake fitarwa  , ya kawo mata abinci  ya ajiye akan table   zai fita tace "dama ka dawo ka d'auki  d'an iskan  abincinka  dan wallahi bazan ci ba gara na mutu da yunwa   dana Kara cin abun hannun dan fashi." banza yay mata tare da jan tsaki ya sake d'aga kafafunsa yana soke hannunsa cikin aljihu "dan Allah karki ci idan yunwa ta kasheki bani da hasara, ni mu hudu ne agurin mahaifiyata kefa ? ya karasa maganar tare da juyowa gbdy  ya fuskanceta sosai , Ido cikin Ido suke kallon kwayar idanun junansu " idan kin mutu iyayenki kikawa hasara sannan  karki dauka idan kin mutu ni jaguwa  zan kaiwa iyayenki gawarki , no  a ruwan  teku  zan watsaki kifaye  suyi wuf da gangar jikinki  ". Ai ko gama rufe baki bai yi ba ta bare baki ta fara kukan  shagwa'ba  "Allah ya Isa  tsakanina da Kai  mugu azalumin sai  Allah ya saka min ". bai sake saurarata ba ya kama  gabansa yana jan dogon  tsaki ."

Bangaren ammi kuwa har qarfe goma saura na dare tana jiran Kiran Adnan  dinta da yace ta jirashi kome dare kar tayi  bacci zai kira  ,ta tashi daga falonta  ta  shiga  dakinta  dan tuni yaranta sun shige d'akinsu  ta fara shirin bacci har ta gama shirin bacci bata ga Kiran Adnan dinta ba  tai shiru tana tunaninsa  "ai har yanzu da sauran lokaci bari naga bugawar 11 idan bai kirani ba sai na kirasa ".ta kwanta akan gado tana ambaton sunan Allah  kwanciyarta ke da wuya sai ga kiransa ya shigo  ta d'auka had'e  da sallama byn ya amsa  "tace yanzu na gama maganarka a zuciyata , "okay  fatan dai Lafiya  yasu shafiq da hally "duk muna lafiya ya aikin ? "Alhamdulillah ammina yau dai naji jiki sosai ,  gbdy jikina ciwo yake kamar na taho gida "ai kaga irinta shiyasa kaga na damu kayi aure Adnan bamu da lokaci idan kaji ance babu lokaci to  mutuwa ake nufi zata iya  zuwa ma mutun Ako wani lokaci ,baka rasa komai ba , Allah ya rufa maka asirin da zaka iya ajiye  mata  hud'u a karkashinka  me yasa bazakayi ba ?",zanyi ammin inshallahu nan kusa  "ko na nemo maka mata  ?shiru yayi ya kasa ce mata "eh ! sannan ya kasa cewa a'a
"Kayi shiru kana jina idan na nemo maka ne sai na bazama ko cikin ya'yan kawaye da dangi ne na nema irin wacce nake so ? murmushin gefen baki yayi kana yace "duk yadda kikayi daidai ne ammina zabinki abun so ne , hira sukayi sosai  na tsakanin uwa da d'a Wanda hakan ya sanyaya  zuciyarsa  ya dan ji damuwarsa ta Kau, sun dan jima suna hira sannan sukayi  sallama ."

*******

zahra basu Isa   garin Edo ba sai gurin karfe goma da wani Abu  na dare kasancewar motarsu bata samu passger da wuri ba gashi motar  tayita tsayawa a hanya dan haka basu yi tunanin zuwa gurin boka ba sai suka  kama  hotel , washegari kuwa karfe shida a gidan boka tayi musu, tunda  suka shiga cikin gidan bokan gaban Zahra ke fad'uwa , sun  iske mutane dayawa  da manya motoci parke a haraban  gurin  ta sha mamaki ganin lokacin da suka zo amman still sai da suka tarar da mutane ,suka  k'arasa gurin amsar kati suka  amsa suka samu guri suka zauna suna tautauna  akan matsalarta  , a hankali har layi ya kawo kansu suka mike suka nufi d'akin da bokan yake aikinsa ,  da baya da baya  suka shiga wanda haka dokarsa take ba'a shiga ta gaba sai da baya .
babu  komai ajikin bokan sai wani gaye  da yasa ya   rufe gabansa dashi suna k'arasa shiga cikin d'akin suka fuskancesa sannan suka  buga kafarsu na hagu  sau uku wanda shima  kaida ne ga  duk wanda  yazo sai yayi.
da hannu yayi musu alama da gurin zama suka zauna shi kuma ya fuskanci gunki dake daskare a gefensa mai yatsu bila'adadin  fuskar gunki kamar na aljanu gbdy ilahirin jikin  gunki jini ne  kuma na mutane .
Blessing  ta bud'e baki zata fara masa bayani ya d'aga mata hannu "karki fara cewa komai ni ne shad'anin boka, bokan da baya gudun mutuwa sai dai mutuwa ta gujeshi, bokan da ba'a  fad'awa abinda zai faru sai dai ya fad'a "kin kawo kawarki adalilin tana son ta mallaki zuciyar  saurayinta  wanda shi a halin yanzu zuciyarsa naga  diyar minister of health  ,zahra da blessing  sukayi shiru gabansu na faduwa barin  zahra da hankalinta yay mugu mugun tashi jin zuciyar jaguwa ta kamu da soyayyar yarinyar".

  "hatsabibin boka ne ni  zan tabbatar da nayiwa kawarki   abinda take bukata , zan biya mata bukatarta ta duniya,   ya juya ya kalli zahra " zakiyi  nasara akan rabashi da  yarinyar amman   shi da wahala ki mallakesa  kamar yadda kike so , domin kuwa  wannan  mutumi ya wuce da tunaninki yana  da hatsarin tunkara domin kuwa akwai  tsari mai karfi  ajikinsa , kafafunsa yafi naki tsawo ,Inda ya taka har ki mutu  kafafunki bazasu taka ba . "
"yanzu boka  ya za'a yi kenan   wallahi idan ban mallakesa ba zan iya  mutuwa sannan babban burina na rabashi da yarinyar nan koda diyar talaka ce bare diyar mai  kudi.
sai daya numfasa sannan yace " na fada miki bazaki mallakesa ba sai dai ki rabashi da yarinyar ,Kuma  aikin da za'a rabasu  na  bukatar  budurwar wacce    bata taba aikata zina ba  Kuma an yi nasara domin kuwa  yarinyar budurwa ce wani nmj bai taba amfani daita ba ,Ina tabbatar miki  muddin ya kusancenta zaki iya rabasu  zai dai ya saurareki   amman  ba  zakiyi yadda kika ga dama dashi  ba  yana gama fad'ar haka yace  "me kika gani ayi  aikin ko abari? "

hankalinta a matukar tashe tace "yanzu boka babu wani mafuta sai wannan ?" wallahi Ina matukar kishin Adnan bazan so ya rabi wata mace ba byn ni "wannan ne  kawai hanya mafi sauki  Shima din   ba shine zai Kai Kansa gareta ba  itace zata Kai masa kanta  , Kinga wannan saurayin  naki akwai abubuwa da yawa akansa shiyasa ma ya  rufe ma Kansa  taurari dan kar mutane su san ko waye shi   yana kaiwa nan yace ku tashi ku wuce "kafin  sati biyu  da kanki zaki kirani  ki bani labarin cigaba da aka samu  ta bud'e jakarta  ta dibo kudi masu yawa zata ajiye a gabansa  ya nuna mata gurin gunkinsa , nan taga wata tukuyar tsafi  daskare da jini ta saka kudin ,jiki a sanyaye suka baro gurin boka zuciyar Zahra cike da matsanacin kishi "gsky banji dadin wannan aikin ba nifa banason ya kusance kowace mace byn ni , yanzu ance dole sai ya kusanci yarinyar nan Kuma gashi budurwa ce Kinsa amsar budurcin mace akwai tsayawa arai   .
"ki  kwantar da hankaliki  Zahra kibi maganar boka Inda akwai wata mafutar byn wannan  zai  miki  ,ke yanzu ma meye abun d'aga  hankali dan ya kusancenta  ke da zai dawo hannunki  "wani zai dawo hannuna ko baki ji abinda  bokan yace ba ? cewa fa yayi bazan mallakesa ba ni wallahi dama na hakura da aikin nan ta karasa maganar tana yastina fuska ."
Chapter 36 · 0% Book details