← Book details Kuskuren Baya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 16 OF 160

Sashe 16

Kuskuren Baya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

*****
A hankali ya bude  kyawawan idanunshi ya  daura akan  ƙaramin agogon dake ajiye akan abun gado,  karfe  takwas ya gani har  ta wuce da wasu yan mintuna tsaki yaja saboda ya makara idan akwai abinda ya tsana bai wuce makara gurin sallah ba , ya  kwantar daita tare da lullu'beta da bargo ya mirgina ya sauko  ya janyo towel ya d'aura ajikinsa cike da natsuwa ya  shiga   bathorrom , bathtube ya shiga ya tsaya ya soma sakarwa jikinsa ruwa, wankar tsarki yayi tukuna  domin tsaftace jikinsa sannan yayi wanka soso da sabulu bai dade ba   ya fito yana goge jikinsa yana kallon fuskarta da gashin kanta mai tsantse da sheki komai nata mai kyau  ya furta hakan a kasan ranshi ..

Jallabiya ya ciro wani design din yasa ya  karasa kibabben gurin sallarsa ya soma gabatar da sallah gabansa na faduwa , yana matukar fargaba da tsoron mahalincisa a duk sanda zai yi sallah sai yaji gaba-daya komai ya kwance masa ,yasan abinda yake aikatawa bai da kyau har yana jin tamkar ibadar da yake ma ba'a amsa ,yayinda take zuciyarsa ta kawar masa da wasi wasin data shiga ya dinga yi mata naci da karfafa gwiwar da   ana amsa har ya idar zuciyarsa rawa take ya  mike ya dawo inda take kwance tana sauke numfashi hannuwansa duka ya kai jikinta ya d'agota ta zube jikinsa ta lafe tare da turo masa karamin bakinta gaba , bakinsa ya kai cikin kunneta "ki tashi kiyi sallah lokaci ya tafi  mika tayi ajikinsa wanda ya haddasa masa jin wani irin shock , "uhm zanyi  zuwa anjima bacci nake ji jikina duk ciwo yake min ,gefen kunneta ya  ciza da dan karfi ta saki qara tana sake  shigewa jikinsa "dole ki tashi kiyi sallah me kika yi da kika gaji  ya k'arasa maganar yana busa mata iskan bakinsa take tsigar jikinta suka mike sake turo masa  bakinta  tayi tana kokarin buɗe bakinta taji yayi sama daita ya shige bathorrom daita ya sakata  a bathtube "ba'a lattin sallah a gidana oya kiyi alwala ya juya ya koma d'aki bayan kamar minti uku ya dawo hannunsa rike da jallabiya ya ajiye mata ya sake fita ..

Jiki a mace ta fito tana kallon inda yake zaune rigingine da gado ta isa inda taga dadduma ta tada sallah bayan ta idar    ta koma dayan bangaren da yake ta zauna "good morning ?"morning ya faɗa atakaice batare daya kalleta ba "ya kamata na koma gida ina so..
"zaki tafi nan da wasu awani dan zamanki bashi da  wani amfani , ya fada yana mik'ewa akan  katifa    bata sake cewa komai ba  ta zame ta kwanta tana runtse idanunta "komai cikin gadara da isa da nuna rashin kulawa ta fadi haka a kasan ranta .......

ya mike ya fita daga dakin zuwa  wani dakin , yayi shirin fita operation dinsa tsaf ya shirya cikin bakaken kaya  riga da wonda na suit  ya ɗauki bindigarsa pistor guda  har guda biyu ya soke ajikinsa yabi jikinsa da turare mai sanyi  kamshi  sannan ya  fito zuwa babban  parlou'n gidan  yana d'aura agogo a tsintsiyar hannunsa turus yayi ganin jabir kamil jubi da Anas zaune suna   tautaunawa akansa  ganinsa yasa  suka mike  suna kallonsa , kallonsu shima  yayi daya bayan daya yana tabe baki  sannan yace "ku kuma fa ? "a tare  suka bude baki mun zo ne akan wannan fitartaka  bama son ka fita aikin nan dan Allah ka hakura  ,"me yasa bakwa gajiya da magana ɗaya nifa wannan ba sabon abu bane agurina,",Koda yaushe kana jayayya damu akan ra'ayinka  amman  akan  wannan   dole  mu fi karfin ka "karfin wa ? ya furta   yana musu wani irin  kallon kasan ido
"Duk ma abinda zakuce kuce but I must   face tanko gote zasu sake magana ya dakatarsu har zai  fita yaji jikinsa yayi masa  wani iri a hankali ya juya ya koma ciki ,kai tsaye d'akin  da tanweer take ya shiga ya hawo har saman  gado  ya shige jikinta yana kissing din bayan wuyanta jinta yake kamar matarsa ya zira harshensa cikin kunneta sannan ya kamo hannunta cikin  nashi "zani wani aiki mai mahimmanci da zarar na dawo zan kai ki gidanku  ajiyar zuciya ta sauke tana juyo ta zuba masa ido batare da tace komai ba shima bai sake furta komai ba wani iri suka ji ajikinsu a lokacin da kwayar idanunsu suka tsarke cikin juna ,bai sake cewa  komai ba ya fice tabi bayansa da kallo kamar ta hanashi fitar duk da batasan inda zashi ba , har lokacin su Anas   suna  tsaye ya nufi haraban gidan suka biyo bayansa   suna masa magana amman ko tari bai yi bare su saka rai zai amsa musu   , kai tsaye dakin ajiye makamansa ya nufa ya dibi harsashi da kudi masu yawa ya ɗauki keyn motarsa city ya  fito still suna biye dashi ya karasa inda aka tanada domin ajiye motocinsa  ya danna key din hannunsa ya bude  kofa mazaunin direba  ya shiga ya tayar mai gadi na ganin hancin motarsa ya bude masa, ya cilla motarsa waje  .

mutanen dake tsaye jiran fitowarsa suka mike tsaye ,kamar ba zai tsaya ba sai kuma ya tsaya   batare daya kashe motar ba ,yayi warning glass din motar ya  ciro bandir din kudi yan dubu day day ya soma  raba musu kamar yadda ya saba suka dinga  amsa suna zuba masa ruwan addu'a da samun nasara  yana kada kai ,sai  daya sallamesu sannan ya dauki hanyar zuwa donping estate   ..

     "Taurin kai taurin kai mutun kamar mutanen farko duk abinda kaji ance ka barshi barinsa shine alkhairi duk kuma abinda zaka samu a duniya zaka bar shi jubi ya faɗa cike da taikaici da bakinciki taurin kan Jaguwa "wayyohlly Allah wallahi har na fara tausayawa yan'uwansa da halin da zasu shiga idan wani abu ya faru dashi  kamil ya fada yana marairaice fuska , jabir yace " wallahi tunda ya soma shirin aikin nan naji ajikina babu nasara  "muyi masa addu'a kawai Allah ya dawo dashi lafiya domin shine karfin gwiwarmu bamu taba samun saɓanin ra'ayi ba sai a wannan lokacin inji cewar anas daya fi kowa shiga damuwa " ameen suka had'a baki gurin fadar haka..

A hankali yake murza stearing  yana tunanin yadda abubuwan zasu kasance gaba-daya ya gama tsara komai da yadda zai shiga ya fito har ya dauki  titin da zai kai shi  estate din  ya  karaso bakin get din estate din yayi parking ya ɗan dade sannan ya fito     daga cikin motarsa yana gyara zaman suit d'insa kai tsaye gurin securitys din bakin get ya nufa suka gaisa a mutunce bazakace masa dan fashi ba bayan sun gaisa yace "ina son ganin Alhaji tanko gote  ..
Daya daga cikin securitys ya leko daga cikin wani karamin daki yana dubansa ganinsa cikin shiga ta kamala ya koma ya zauna dayan yace "me ye sunanka na duba ko kana cikin list din masu son ganinsa ? Shiru yayi ya kasa magana yana ciza lip's d'insa na kasa security ya sake kallonsa yana  tambayarsa "uhm don't worry bari na kirasa "better dan ba'a bawa Kowa damar shiga sai da izininsa  wayarsa ya ciro kamar zai yi kira ya koma cikin motarsa ya zauna yana tunanin yadda zai shiga cikin sauki .

"  Anas........"
jabir  ya kira sunansa yana zama a gefensa "na'am jabir Anas ya amsa jiki a sanyaye"  everything will be fine naga duk ka damu tunda jaguwa ya bar gidan nan  "dole na damu jabir ina jinsa tamkar danuwana bana son wani abu ya sameshi bana son na rasashi yayi mgnr kamar zai zubar da kwalla "jaguwa ba kamar sauran mutane bane , gabad'aya alamuransa akwai lisssfi  ,yana da kaifin kwakwaluwa bazai bari mu rasa shi ba saboda yasan muna son shi "jabir nasan da haka nasan yana son mu duk duniya bashi da aminan da suka kai mu but bansan me yasa yayi irin wannan taurin kan ba ,nayi kokari fahimtar dashi nayi komai akan ya bar wannan aikin amman yaki ya kasa fahimtata jabir zuciyata na cike da tsoro yanzu idan wani abu ya sameshi  adalilin tango gote ya zanyi da rayuwata ? "Anas kana tsoro da tausayinsa with  reason nima zuciyata tana cikin damuwa amman abinda na lura dashi  yana sane so yake mu rasa shi inji cewar kamil wallahi idan wani abu ya sameshi bazan taba yafe masa ba yayi maganar yana goge hawaye "ba haka bane kamil  Anas ya fada shima hawaye ne cike da idanunshi "zai dawo   zai dawo anas ya dinga maimaitawa zai dawo da kafafunsa domin shi din ba mutun bane kamar sauran mutane mutun ne mai matukar amfani ga rayuwar mutane yayi handling din matsaloli a rayuwar data gabata ina da tabbacin zai dawo da kafafunsa suka rungume juna suna kuka ..

****
Alhaji tanko gote  zaune a cikin  tangamemen parlou'n sa daya ji kayan more rayuwar duniya tare da manya abokansa kowane hannunsa rike da glass cup  suna kurban ruwan  win yayinda gabansu table ne dake dauke da kayan itatuwa kala dabam dabam,tun daga kan ginin gidan da tsarin da'aka bi dashi za ka san mamalakin gidan attajirin ne,gidan  zagaye  yaje da flowers sannan  yafi Kowane gida dake cikin estate din kyau da tsaruwa  .

shewa ne ke tashi acikin parlou'n "mutunen  da zasu ce meye namu acikin lamuran   kasar nan ina tunanin mutanen sun tabbata    dakikai ne , domin daga kasar nan tamu har  zuwa kashen ketari sunanmu ya zagaya sannan a san da zamanmu,   maga Wanda ya isa yace meye namu acikin lamarin kasar nan bayan mune gwanati  "wannan haka ne inji cewar Alhaji amadu dan iya wanda ke fuskantar alhj tanko gote   "muna da tarin kudi muna da tarin mutane muna da hanyoyi daban daban akwai connection me muke so  acikin kasar nan da bamu samu ba  da har wasu zasu dinga cewa meye namu aciki ?  "babu ma wanda ya isa domin mune gwanati kuma ko ana so ko ba'a so dole a dama damu  kuma muyi abinda muke so  "wannan gaskiya  ne ...
Chapter 16 · 0% Book details