← Book details Kuskuren Baya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 3 OF 160

Sashe 3

Kuskuren Baya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Yatsina face dinta tayi nan ta soma tunanin ko gamo tayi dan ita da gaske taga lokacin da tayi hitting dinsa, sai dai Kuma su duka bazasu mata karyaba.
"Oh my first day is terrible". Ta fada lokacin data koma da baya ta kwanta kan bed din tare da rike kanta.
"But you did well, dan hospital d'in nan sai maganar ki ake kinyi matuk'ar bamu mamaki you know so much about your work gaskiya Allah dai ya taimaka ya k'aro mana irin ku a wannan k'asar tamu". Dr. Mansur ya fada cike da fara'a.

"Wow that's good! Dole muje gida ayi celebrating d'in wannan ranar". Alh.Abubakar ya fada cike da jin dad'in kalaman dr.Mansur.
"But Dady nayi accident fa".
"So what? We will still celebrate this day tunda you are safe Alhamdulillah.

Nan Dr.Mansur yayi rubuce-rubucensa ya basu sukai sallama, kiran Nurse yayi ta karba dan karbo musu drugs din kafin su shirya. Cikin kankanin lokaci suka bar hospital suka nufi gidansu.

Duk yadda minister yaso ayi celebrating tanweer taki hasalima zamanta tayi a daki akan stool tana kallon window batare da tasan me take tunani ba ji tayi an tabata a firgice ta juyo ta kalli bayanta Ibrahim ta gani tsaye ......

DARLING'S

💗💗💗💗💗💗
KUSKUREN BAYA
     💖💖💖💖
💗💗💗💗💗💗

    WRITING BY
*BAGUDO& MIMI'S QUEEN*

WATTPAD @HAUESH

bismillahirrahmanirrahim

https://my.w.tt/lcJskJdtpbb

🅿️02

A firgice ta juyo  Ibrahim ta  gani tsaye a bayanta yana sakar  mata  murmushi, ta yatsina  face d'inta  tana kauda  kanta gefe ,tsaye yayi yana kallonta gabansa na wani irin  fad'uwa, musamman daya tuna shine  dalilin accident din da tayi.
     Cike da sanyin jiki ya k'ara matsowa daf da ita ya rage tsawonsa har tana iya jin karar bugun zuciyarsa da hucin numfashinsa  a gefenta, runtse idannunta tayi ta juyo zata mishi magana karaf idanunsu  ya tsarke cikin juna  har saida hancinsu ya  da'n gogi  juna.

Tsura ma juna idanu sukai kafin daga baya  tayi ko'karin da'uke kanta shima yaso yin hakan sai dai ya kasa aiwatarwa,  sake juyo daita yayi akayi rashin saa hancinsu ya goge juna kanta ya bugi goshinsa  . "Ouch!". Ta furta a hankali cikin Jin zafi ta kai hannunta kan bandage din dake zagaye a kanta.

"So...sor...sorry!". Ya fada a rikice , ta  tsura masa Ido  tare da lumshe masa Ido tana radadi  , idannunsa ya runtse Shima  kamar ciwon a kanshi yake , ware idannunta tayi a hankali tana kallon yadda duk yabi ya rud'e yake bata hakuri a natse ta samu guri ta zauna  tuni  Shima gwiwowinsa suka   mazauni a gabanta  Yana kallonta kmr ranar ya fara ganinta .

          "I.B!". Ta Kira sunansa cikin sassanyar  muryarta  kamar yadda ta saba kiransa, lokaci guda ya d'ago rinannun idannunsa ya zuba mata Yana  kallonta itama shi take kallo cike da tsananin tausayawa."Tan I am really really sorry for causing you so much troubles on your special  day". Ya fada yana kallonta cike da kulawa da nuna lallai yana nufin abunda yake furta mata har cikin  ransa.

Lumshe idannunta tayi ta bud'e a hankali  " Hey is not your fault kawai haka Allah ya tsara karka yi blaming d'in kanka akan accident din Dana samu ". Ta fad'a tare da kauda kanta gefe  dan ko kada'n batason ganin irin wannan yanayin nasa , dan yana karya mata zuciya .

        "ni ne naja komai Kinga dole nayi  blamed kains akan   abinda ya faru idan  ban kira ba a wannan lokacin ba  this wouldn't have happened to you , nayi diverting attention di'nki I am very so......"."Oh my god  I.B!"ta sake  fada cike da bacin rai idannunta a rufe.

"I am s...".
        "I know you are Kuma nayi accepting kaima kayi hakuri". Ta faɗa lokacin data tashi tsaye tana binsa da kallo shima tashi yayi suka kalla juna murmushi ya sakar mata. Da sauri ta da'uke kanta tare da shooking d'in kanta  da murmushi me sauti.
         Jin sautin murmushinta yasa shima ya fad'ad'a nasa murmushi.

Taku tayi zuwa bakin window d'in shima cikin sauri yabi sahunta, yasa hannunsa biyu ya zagayeta dasu ya mannata a  jikinsa, Runtse idannunsa  yayi yana jin wani irin feelings d'inta, sam baisan  ya rasa ta a rayuwarsa.

Bangaren Tanweer kuwa  ajiyar zuciya ta sauke tare da runtse idannunta, tana matuk'ar tausaya ma d'an uwan nata da  irin son da yake mata tun bata san soba yake nuna kulawarsa akanta , ta rasa mai yasa har yau bata jin sonshi cikin ranta baya ga na 'yan uwanta   duk da tasan yana masifar sonta da rawar jiki a Duk abunda ya shafi lamarinta tare da rumgumarta  amma ta kasa sakin jiki dashi gashi shi  kusan bai da aiki saina  nuna mata tsantsar so da kulawa a ko yaushe Amman  hakan baya sata taji irin abunda take jin  friends dinta na bata labari sai dai kawai ta biye masa, Sun jima a tsaye yana rungume da ita inda sabo ta saba da wannan hug din nasa wanda iya abunda yake iya samu  kenan agunta  bayan shi ba wani.

"Salamu Alai... !".
      Momy tafad'a lokacin data turo kofar dakin  yanayin data gansu yasa tayi saurin kokarin komawa tare da jan ko'far da sauri Tanweer ta zame  jikinta daga rik'on da Ibrahim ya mata wanda shima tuni kunya ta gama rufe shi."Please Momy wait!". Ta fada lokacin data dan taka da sauri zuwa bakin ko'far tana kallon Momynta wacce ke kallonta cike ta tambayoyi ,ganin yadda take kamar tana Jin tsoron yin magana,  sun dauki minis a tsaye a haka tana jujjuya ka'farta ta rasa meyasa take jin tsoron yin magana akansa  duk da she don't know him.

"Tanweer I am waiting!". Momy ta fada lokacin data kalla Ibrahim wanda shima ya kasa kunne yake sauraran jin abunda ke zuciyar Masoyiyar tasa, wanda daga shi har Momy suna mamakin yadda take jimamin  yin tambayar bayan she is not the type to.

"Ahm Momy!". Ta fada tana wasa da dan igiyar gaban shirt dinta.
        "Oh Tan! Tunda baki da abun cewa I will have to leave inada abunyi". Momy ta fada lokacin data juya da sauri Tanweer ta riko hannunta cikin nata . "Please Mom!". Ta fada tana tabe lips d'inta cike da shagwaba kamar Wata 'yar karamar yarinya.

          Yanayin yadda tayi har saida yaba Ibrahim dariya me sauti wanda bai tsamanin fitowarshi ba sai gashi ya fito, d'an kallonshi Tanweer tayi ta maida dubanta ga Momy wacce ke murmushi, ganin yadda Tanweer ta juyo a fusace yasa tayi saurin rufe bakinta da hannunta.

"Momy!". Ta Kuma kiran sunanta.
       "Yes my angel!". Ta amsa itama cikin yanayin da  Tanweer d'in ta kirata  cikin zolaya ,d'an buga kafa Tanweer tayi a fusace ta  raba ta  gefen Momy ta wuce  tana bubbuga ka'fafunta , Kallon juna Momy sukai da Ibrahim  Momy tabi bayanta da sauri tana kiran sunanta shima jujjuyawa yayi  yabi bayansu.

Tanweer na fita falon Dadynta ta nufa Kai tsaye . Ko sallama batai ba ta danna Kai, hango shi tayi zaune da system a gabansa da alama akwai abunda yake important a wannan lokacin musamman Jin ana niyyar kiran Sallar Magrib amma bai tafi masallaci ba.
        "Dady! Dady!! Dady!!!". Cike da shagwaba take kiran sunan yana amsawa ba tare da ya waigo inda take ba tama kanta mazauni gefe, Ganin bai kalleta ba yasa ta fashe mishi da kuka.
         Jin hakan ya k'ara  d'aga masa hankali ya  ajiye komai  ya nufi inda take zaune. "Subhanallah me ya samu   Babyna  take kuka? Please tell me waya taba mun ke? Waya sa hawayenki me tsada tsiyaya ki fadamun Ko  wayeshi a fad'in duniya!". Ya karasa maganar cike da zafi, dan inda akwai abunda ya tsana a duniya to bai wuce hawayen Tanweer ba.

Shigowar su Momyne ya katse mushi abunda yake fad'i nan  take ya maida fad'an kansu, Tanweer har lokacin tana ji yana musu fad'a bata tanka ba sai da yayi me isarta tukunna ta d'ago. "Dady please I...inaso...". Sai Kuma tayi shiru tare da sunkui da kanta k'asa.

Da sauri Dady ya koma inda take zaune. "Me kike so? Ki fadamun komeye shi a kawo miki!". Ya fada yana hararar su Momy dake tsaye gefe guda.

         Girgiza kai Tanweer tayi da kyar ta bude 'yan kananun lips d'inta. "Dama wanda na kad'e akace ban kad'e ba inason ganin shi  domin nasan lafiyarsa". Ta fada cikin sanyin murya wanda ita kanta batasan tana da shiba, ta rasa me yasa tunda ta dawo hospital ta kasa samun  nutsuwa akansa  ta kasa cire kyawawan idannunsa daga zuciyarta.

"Tanweer yaron nan bashi ya kawo ki hospital ba, hasalima bai biyo suba ta Ina za'a nemosa Ko a samo  wanda ya sansa?". Ya jero mata tambayoyi wanda yasa bugun zuciyarta k'ara gudu saboda tsoron ace bazata k'ara ganinsa ba.
        "But I am worried". Ta furta hakan kamar zatai kuka.
         "Please Baby karki damu kanki kan wani wanda baki sani ba talakan banza da wofi he does not deserve your worries especially your tears my Tan". Ibrahim ne ya jero mata wadan nan kalaman ganin duk tabi ta damu, tuna yadda ya shiga da'kinta ta jima bata sanda  shigar shiba, ya tabbatar tausayi kawai ke damunta ba wani abuba, sai dai sam baiga abunda zaisa ta damu kanta akan wani talakan banza ba.

Nan suma  mahaifinta sukaita lallashinta wannan daren da kyar ta iya cin abinci ta koma da'kinta Ko hira batai dasu ba, haka shima Ibrahim ganin mutuniyar tasa ba face tun wuri ya kama hanyarsa ya bar gidan,  juyi kawai take akan makeken gadonta  idan ta runtse idanunta babu abinda take gani sai kyakkyawar fuskarsa mai ɗauke da kamala da natsuwa da alamun ya karantu yadda ya kamata saboda yasan mahimmancin dan adam, kafin ta gama fita haiyacinta taga yadda ya rude akanta Sai dai tayi mamakin da akace ba dashi aka kaita  hospital ba, wani irin bugawa qirjinta yake da matsanancin karfi ,ta sake  runtse idanunta gam   bata son ganin komai sai shi mikewa tayi ta janyo system d'inta ta shiga yanar gizo.
Chapter 3 · 0% Book details