← Book details Kuskuren Baya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 60 OF 160

Sashe 60

Kuskuren Baya Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

da misalin karfe takwas  jaguwa  na  kwance a falonsa  yana kallon Tashar   labarai  domin yasan  halin da gari da kasar  gbdy  take ciki, gabansa ne yayi wani  irin mummunar  fad'uwa kamar  Wanda aka  buga masa guduma  ,shiru yayi kawai  yana tunani  sai  dai idanunshi na kan tv  ,duk sanda gabansa  yayi irin wannan faduwar tabbas akwai  gagarumar matsalar dake shirin kunno Kai cikin rayuwarsa  .
Remut ya ɗauka  ya  kashe tv sannan  ya mike ya koma uwar  dakansa ya kwanta akan makeken gadonsa ya  fuskacin kofar shigowa  gidan gbdy  tare da  runtse idanuwanshi ."
a daidai wannan lokacin kuwa jami'n tsaro ne kewaye da unguwar kowannensu rike da bindiga  tun daga nesa suka  hango gidan koina zagaye da hasken fitilu ,  a hankali sautin muryar dcp dake gaba ta  fito "
"be careful  lokacin mu ya fara kowa ya kasance cikin shiri a hankali suka fara tafiya cikin sand'a suna taku da k'okarin isowa gidan  suna gama karasowa suka nemi gidan kasa ko sama  suka rasa gabad'aya gidan ya dawo rafi a matukar firgice sukayo baya da sauri kowannensu  na kallon dan'uwansa cike da  tsananin tashin hankali  ,bayan kamar minti biyar dcp yayi gaba kad'an ya  kira wayar IPO investigation police"kana ina yanzu IPO  ?"Ina cikin gidan "kamar yadda mukayi  fa mun zo sai dai babu gidan sai rafi "what ?"rafi Kuma?"tabbas haka ne abinda muka gani kenan "kana  dai lafiya   ko ?Ina lafiya Anya kuwa zan cigaba da aikin nan na fara karaya da lamarinsa ?
"tantiri ne na karshe ,asirin  jikinsa yayi yawa  "ka dai  ka Kara hakuri tukun nan tunda har yanzu bai gane kana tare dashi ba  ka cigaba da bincike akansa ka gano mana  makarin asirinsa   zan sake  komawa    malami nan gsky layar daya bani bata yi aiki komai ba shi daya ce zamu samu nasarar shiga gidan sai gashi gida ya dawo rafi    "shinkenan sir  jiki a sanyaye suka juya cikin sauri suka bar unguwar .

Gudu sosai suke akan titi karfe goma daidai suka Isa station  zuciyar dcp kmr ta kama da wuta mafuta kawai yake nema "ta Ina zai yi galaba akanshi ,sam baya bukatar wani ya kamashi sai shi ko IPO abokinsa Kuma yaronsa   wannan nasarar da zasu  samu shine silar daukakarsu wujiga wujiga suka shigo office  suna haki  shigowarsu bai  fi minti talatin ba wayar dcp ta soma ringing kamr bazai d'auka ba sai Kuma ya d'auka yana cewa "hello !Ya furta  hello ya Kai sau uku sannan yaji   an kwanshe masa  da dariya  "masoyina  kenan wallahi har  na fara Jin wani Abu akanka  yana Jin hk ya fahimci jaguwa ne shi kuwa yana gama fad'ar  haka yace sai anjima masoyina mara nasara .
" no ka tsaya  Ina son  muyi magana da Kai abinda kake aikatawa babban kuskure ne Wanda zakayi danasani akansa "wani  irin kuskure Kuma bayan Wanda aka aikata a can baya ? har kullum bazan gaji da fada maka ka daina bibiyata ba domin bibiyaar mutne masu laifi Abu ne me wahala bana tsammanin zaka iya samu wani Abu ballatana ka shigo inda nake".
" meye abun bata loakcin da Kai da yaranka  ?ku manta da ni kawai idan Kuma Kuna bukatar wani tamako zaku iya sanar dani na taimaka muku dashi  "what?
"Haka nake nufi domin dukkanin ku babu Allah a ranku kanku kawai  kuke so ,kuje ku jajurce akan masu aikata miyagun laifufuka wanda zasu cutar da mutane  daku gbdy.
"ka sani kaima hakan zai cutar da kai  tunda kana da yan'uwa "haba da gaske ? to shikenan na fahimta Ina bukatar komawa bacci  yanzu  sai wani lokaci .
"Ka dawo da diyar minister
kada ka bari ta Kai mu ga daukar mugun mataki akanka. cikin sauri jaguwa ya dakatar dashi "kamata yayi yalla'bai yaje ya huta haka nan yayi aiki tukuru shi da yaransa  shiru dukkaninsu sukayi jaguwa bai kashe waya ba haka dcp  .
sun d'auki tsawon minti biyar suna misayar yawu  sannan dcp ya numfasa yace  "me kake bukata ayi maka ka dawo da diyar minister ?  bangaren shigo da miyagun kwayoyin sunyi  yawa a wannan garin namu domin har satificate ga masu shigo dashi  suke da  wanda daga hannunku suka samu."
kashe kashe da fayde ga yara kananan da'ake  wani irin mataki kuka  dauka?
"Kun kasa daukar mataki  alhalin kuna  da karfi da makamai Kuma    kunsan masu aikatawa har  lasisi kuke basu suyi yadda suke so  duk  baku damu da  masu aikata   wannan  laifi  ba sai akan me  tayaku aiki .
" me kake k'okarin cewa ?", abinda nake so ku janye jikinku ga abinda bai shafeku ba shine zai fiyye muku ni nan nasan yadda zan hukunta duk wasu masu  aikata laifi idan da dama Kuma ku maida hankalinku izuwa kan tayani aiki idan Kuma babu dama ku share kawai  duk Kuma abinda zakuyi tunani akaina baxai ta'ba muku  amfani ba ku tsaya a matakin da kuke domin wuce  gurin zai iya zamo muku tangarda a rayuwarku wanda ya shiryawa mutuwa yayi k'okarin sake dumfarar gidana wallahi nayi alkwari  zan kawar dashi a doron kasa bazan taba canzawa daga abinda nakeyi  sai dai ban sani ba ko ta bangarenku zakuyi sorounder  ku fita a rayuwar jaguwa ."
shiru sukayi gbdy suna saurarensa suna daukar maganarsa  kowannensu da abinda zuciyarsa ke sakawa akan yadda za'a bullowa jaguwa gbdy idanun dcp ya canza kala babu komai acikin kwayar idanunshi sai tsantsar bacin rai hannunwansa duka ya hade guri d'aya ya rufe fuskarsa  dashi   yana dogon   nazari   da  zance zuci  yayinda har lokacin idanunshi ke kan wayarsa ."

tashi yayi ya soma tafiya har yayi taku uku d'aya daga cikin yaransa  ya tsaidashi ta hanyar cewa"yalla'bai yanzu me ya kama muyi ?"ka dauki bindigarka  kaje ka kwanta kawai  "kayi hakuri sir ban san tmbyata zata bata maka rai  ba "ka sani  mana , idan ba haka ba meye na tmbyta abinda za'a yi byn kasan dole zamu sake  nemo mafuta  yadda zai shigo hannunmu ?"irin wannan lokaci nazari ake bukata idan ba haka ba  zamu tashi a tutar babu yana gama fad'ar haka ya juya cikin tsananin fushi ya bar  d'akin taron  yana fita kowa ya kama gabansa .

****
A hankali ya shigo d'akinta  bai ganta ba  saukar ruwa yaji abayi nan ya fahimci wanka take a natse ya karasa ya jiye mata kwado da macijin  roba a tsakiyar gado  ya juya  da sauri ya fita ya koma d'akinsa ya zauna zaman jiran abinda zai faru yana bukatar Jin dumin jikinta sai dai yasan bai Isa ya Kai Kansa ba duba ga irin rashin mutuncin da yayi mata yana zaune har minti ashirin ta wuce har ya fidda rai da zai Jiyo sautin ihunta sai kawai yaji ta kwalla Kara "wayyohhhly Allah na shiga uku sai kuma yaji shiru  da sauri ya shigo  d'akin kwance ya ganta a  kasa bata numfashi ya tsugunna gabanta yana karewa dukiyar fulaninta kallo dake cikin riga  gasu nan  tsaye  kyam Kuma a cike hannusa ya Kai yayi kasa da rigar  yana zagaye  kan nipples dinta a ransa yace   "sarkin rashin kunya da tsoro kenan   ya  Kai hannuwansa ya tattarota gbdy   zuwa jikinsa daga ita har doguwar rigar jikinta tunda ya siyo su ta daina fitowa daga wanka daga ita sai towel sai dai ta shiga  da riga Kuma ta rike wata rigar da zata canza   ya rungumeta  tsam ya nufi uwar dakansa  ya kwantar daita ya janyo stood ya zauna a gabanta  ya tsura mata tsumammun idanunshi yana kallonta "why Adnan !
"karka taba diyar mutane ka barta da gibin dakayi ma rayuwarta ai babu abinda zan mata dumin jikinta kawai zanji ya bawa zuciyarsa amsa da hakan.
Ya  dade   zaune yana   Saka da warwara  kafin daga baya ya dibo ruwa ya shafa mata a fuska zuwa qirjinta naunayen ajiyar zuciya ta sauke amman taki bude idanunta  ya cire  kayan  jikinsa ya fad'a bayi ya kusan awa d'aya a bayi yana saba jikinsa Wanda zuwa lokacin ta bud'e idanunta tare da yin  shiru tana tunanin abinda ta gani gbdy a tsorace take  .ya fito d'aure  da towel a kugunshi sai dan karamin towel din dake rike a hannushi yana tsane ruwan jikinshi a gaban mirrow dakinsa  ya tsaya  , yayinda ita kuma  take kwance    tana faman rarrashin  zuciyarta  akan abinda ta gani  wanda ya kusan   tarwatsa zuciyarta kwadon  da micijin  data gani  idanunta suka cicciko da ruwan hawaye komai na gidan tsoro yake bata a halin yanzu ,ahankali ta sauke naunauyen ajiyar zuciya tana dauke Hawayen idanunta  da tafin hannunta ta yunkura ta mike zaune  tana kallon  sanda   jaguwa  ya d'auko lotion yana shafawa a ilahirin jikinshi hankalisa   kwace yake yin komai da   fesawa jikinshi   turare masu sanyin kamshi  ta mirrow suka had'a  idanu dashi.
ya dage mata girasa daya
alamun tmby yana sakar mata murmushin mugunta  ,ta d'auke kanta   kawai batare da tace masa komai ba  ya k'arasa wordrob dinsa ya bud'e ya  d'auko short niker wanda  bai gama kaiwa gwiwarsa ba     da wata riga me budadden gaba da shara shara  wanda da gani  na shan iska ne,  gabadaya sifar qirkinshi a bayyane yake,
yayinda  gashin jikinshi dake  kwance luuuuf  dasu ke zuba  sheki  suna daukar hankali..'
Chapter 60 · 0% Book details