← Book details Kuskuren Baya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 91 OF 160

Sashe 91

Kuskuren Baya Part 1 Complete Hausa Novel · about 4 min read

da misalin karfe uku tana zaune a falo taji motsin shigowa  dolapo   ya  shigo da manya ledodi ya ajiye a gefe yana gaisheta ta amsa fuskarta babu yabo babu fallasa ta mike ta koma d'akinta ta kwanta , dolapo  bai k'arasa fita ba dady yasanyo Kai yayi saurin yin gefe ya bashi hanya mumy tayi masa sannu da zuwa kallon da yayiwa mumy gabansa ya fadi sannan ya amsa mata sannu da zuwan datai masa ya zauna a falo yayinda ta tashi ta shiga kitchen ta dauko masa ruwa mai sanyi ta kawo masa ta zauna a gefensa tana sake masa sannu da zuwa byn ya sha tayi masa ya aiki " alhamdulillah yana ganki ke  kadai shiru  ina ita wannan yarinyar ?" ya tambayeta gabansa na faduwa kar ace bata nan .
"Tana d'aki yanzu ta shiga "
naunayen ajiyar zuciya ya sauke yana samun natsuwar zuciya "hankalina na kanku saboda nasan na barki cikin wani hali "ai inshallahu komai yazo karshe ta fad'a tana fad'a masa yadda sukayi daita da safe byn fitarsa  "Allah yasa Iya wahalarmu kenan  tace Ameen "ai muddin ta saba alkwarin taki natsuwa acikin gidan nan zan bata mamaki domin dole ta zaba komu ko shi wancan dan iskan barawon banza inji cewar dady.
ita kuwa uwar gayya tunaninta ba'a kansu yake ba dan tana shiga daki ta d'auki wayarta abun mamaki missed calls din jaguwa ta gani guda uku ajere murmushin jin dadi tayi ta soma neman layinsa kira d'aya ya dauka alokacin yana zaune akan kujera a falonsa system ne a gabansa ya dauka ya manna a kunne idanunsa na kan screen din wayar "hello tanweer ?"
Shiru tayi tana sauke naunayen ajiyar zuciya tare da Jin dadin zazzakar muryarsa "ina yini ?"
"Lafiya ya Kike fatan komai lfy ko dan jiya da tunanin abinda zai faru a gidanku na kwanta hope babu abinda aka miki?"
Babu komai fad'a ne kawai Kuma kamar yadda kace hakuri nayita basu "that's good haka ake so ".
yayi shiru itama tayi har sai data d'auka ko ya kashene ta cire wayar a kunnenta ta duba taga har lokacin yana kan layi ta maida tana sauke masa numfashi tana cewa "hello !
"Ina jinki tanweer yaakayi ?"
"last Kafin zuwana jiya gurinka kace min zaka zo gidanmu ?"
Shiru yayi yana sauraronta batare daya ce komai ba illa mikewa da yayi tare da gyara rigarsa sannan ya nufi d'akinsa ya d'auki wasu abubuwan amfaninsa ya karaso Inda akwatinsa  red and black yake ya bud'e sama ya zubasu sai lokacin yace "ina sauraronki sauri nake domin akan hanya nake tafiya zanyi zuwa Abuja jirgina karfe shida daidai zai tashi ".
me zakaje yi abuja ?" Tayi mgnr kmr zatai kuka dan tuni idanunta sun cicciko.
"alqalla !" Yana daure fuska dan karta kawo masa wasa a aikinsa.
shiru tayi kamar ta karasa fashewa  da kuka "banason aikin nan  adnan ......"
"kullum maganarki kenan " ya katseta ta hanyar fadar haka cikin zafin rai "shine damuwata nafi son ka zauna empty baka aikin komai akan wannan sana'ar, ka tausaya min mana  "naji !" Kukan da take dannewa ne yayi nasarar kufce mata ta soma rera masa kuka har da shesheka "meye hk Kuma ?"ke me yasa kuka baya miki wahala né ?"
"idan wani abu ya sameka ya kake son nayi ?
Sosai tausayinta ya kamashi dan hk ya kwantar da muryarsa kmr tana gabansa "ki kwantar da hankalinki babu abinda zai sameni zama yayi domin rarrashinta wanda bai san yanayin hakan ba ,
" kwana nawa zakayi ?" zanyi kamar sati daya zuwa kwana goma "haba Adnan me yasa baka tausayina ne kwanakin nan sunyi yawa ".
Ya sake yin kasa da murya abinda zai kaimu  din ne dole sai munyi  taking time   "shikenan Allah ya tsare min Kai  "ameen ya furta a can kasan makoshi  yana lumshe idanunshi "yanzu sauran awa daya da wani abu kenan ku bar gida yace  "um ! "zanzo na ganka kafin ku fito zuwa airport Kona zo airport din direct "?
"No karki zo "
ya fad'a atakaice tare da katse Kiran dan bai  son tazo sannan bai son mgn dayawa  dan ma itace shiru tayi rike da wayar taso taje ta ganshi kafin ya wuce har ta fito mumy ta kasa ta tsare kamar tayi kuka ganin take iyayenta basa mata adalci a hukuncin da suka yanke mata a zatonsu zata iya zama na tsawon lokaci batare data d'aura idanunta akanshi ba ?".
ta lumshe idanunta daga tsayen da take "bazan iya ba gsky sai daí kuyi hakuri wallahi ta cigaba da sakar zuci .
Chapter 91 · 0% Book details