Sashe 55
Kuskuren Baya Part 1 Complete Hausa Novel · about 6 min read
Da misalin karfe biyar na yamma ya fito daga d'akinsa cikin shirin fita riga da wando red and ash ne sanye ajikinsa ,
kafafunsa sanye cikin takalmi canvers Ash me ratsin red ta gefe da gefensa , hannunsa d'aure da agogon fata mai kyau da tsada yayinda kwantaccen sumar Kansa ya sha gyara ya kwanta luf luf Hakan ya karawa fuskarsa kyau da annuri sai dai fuskar a hade take babu alamun fara'a ko kad'an ,key din motarsa ferari ne rike a hannunsa Kai tsaye d'akin da tanweer take ya kutsa ya shiga bakinsa d'auke da sallama sai da aciki yayi ,kamshin turarensa daya saba amfanin dashi ne ya doki hancinta ta d'ago a natse ta tsura masa idanunta kamar Koda yaushe fuskar nan tashi babu wadataccen fara'a, muryarta a sanyaye ta motsa labbanta"Ina yini ?"bai amsa mata ba sai ma wani kallon banza daya bita dashi kafin ya d'auke kanshi daga kallonta ya nufi Inda bedside yake ya bude.
bata damu ba dan tasan dole zuciyarsa ta d'auki fushi daita sakamakon abinda tayi masa jiya wasu file ya ciro yana dubawa ya d'auki minti biyar yana tsaye yana dubawa sannan ya mayar ya ajiye ya juya ya fita ya nufi parlour yana taku a hankali kamar bai son taka kasa har sanda ya fito parlour'nsa .
Gbdy abokansa suna zaune kamil nacin abinci ,yayinda jubi ke k'okarin nada tabar wiwi , kunnen anas manne da waya yana ganinsa ya mike tsaye da sauri yana binsa da kallo .
Shima jaguwa Tsura masa Ido yayi yana karanta yanayin wayar da yake , anas ya karasa sosai kusa dashi ya rike masa hannu yana cewa "tanko gote ne wai yana da alqalla me kyau da yake son muyi masa ya kira layinka ba baka d'auka ba shine ya kirani kayi magana dashi ya mika masa wayar . "bazan yi magana dashi ba kaima karka sake d'aukar wayarsa sanin kanka ne anas bama Kulla alqalla da irinsu tanko gote mutumin da nake fatan a karshen rayuwarsa ya zamo mabaraci akan titi ya numfasa sannan ya cigaba da magana a sanyaye " ka kula da kyau anas banason wani abu ya sameka idan wani abu ya sameka bazan yafe maka ba ".duk maganar jaguwa d'aya byn d'aya suke shiga kunnen tanko gote ya runtse idanunshi tare da disconnecting din kira."
" Inshallahu zan kular maka da kaina Ina zuwa haka ga abinci anyi order da Kai ? numfashi ya fesar yana yamutsa fuska kafin yace "zanje ganin ahlina idan naje can zanci zan dan d'auki lokaci ban dawo ba dan zan fara da biyawa gidan marayu akwai sakon da zan Kai musu yana gama fad'ar haka ya zare hannunsa ya juya ya fice daga parlour'n dan yasan yanzu raunin anas zai bayyana .
ilai kuwa hakan ce ta kasance gbdy yanayin anas ya canza rauninsa ya bayyana kamar zai yi kuka ,ya danne hawayensa suka koma, a duk sanda yaga jaguwa za shi ga ahlinsa sai yaji zuciyarsa tayi rauni saboda rasa nashi ahlin da yayi bashi da kowa a halin yanzu sai jaguwa shine komai nashi zama yayi ya shiga duniyar tunani .Kai tsaye Inda motarsa ferari yake ya nufa ya danna keyn hannunsa ya bud'e ya shiga ya zauna yana me kunna motar tare da yin hon me gadi ya wangalemasa get din gidan ya fice.
tafiyar awa d'aya ce ta kawoshi gidan marayu babus'salam dake ikeja gra yayi hon aka bud'e masa get ya shiga, yasa guri ya
yi parking din motarsa ya fito ya bud'e bayan boot dinsa ya ciro bakar jaka dake shake da kudi ya kulle motar Kai tsaye office din shugaban makarantar ya nufa .malam yusif na ganinsa ya fad'ad'a fuskarsa da murmushin jin dadi dan yawon zuwan jaguwa yasa sabo me karfi ya shiga tsakaninsu ,ya nuna masa gurin zama byn jaguwa ya zauna ya mika masa hannunsa suka gaisa "yalla'bai barka da zuwa ya aiki da k'okari ? "alhamdulillah ya naku k'okarin da fama da yara ? malam yusif yayi murmushi kawai ,sun dan ta'ba hirar duniya sannan jaguwa ya mika masa jakar kudin daya zo dashi "ga wadan nan kudaden ayi wa marayu hidima dasu.
"Kai masha Allah ,Allah yasa Saka da alkhairi ,Allah yasa maka ladan a mizani ,yadda kake faranta zukatan marayu Allah ya faranta naka , Allah ya kawo farinciki a rayuwarka data iyalinka, Allah ya tsareka". "Ameen na gode sosai da addua ni zan wuce har ya juya malam yasif yace "yalla'bai har yau baka fad'a min sunanka ba gashi za'a Saka cikin sunayen masu tallafawa marayu "ya juyo a natse yana cewa"bana bukatar a Saka suna , sukayi sallama ya wuce ya d'auki hanya zuwa unguwarsu ko gama daidaita parking din motarsa bai yi ba Jamar'sa na unguwar suka zagaye motarsa tare da Kawo masa gaisuwa.
a natse ya fito yana ƙoƙarin kulle motar byn ya kulle ya mika musu hannunsa d'aya bayan suka gaisa ya Ciro kudi masu yawa ya shiga raba musu me dubu biyar me dubu goma cike da murna suka dinga masa addua shi km yana amsawa da Ameen sannan ya sa Kai zuwa cikin gidansu.
yana shiga gidan ya hargitse da murnar ganinsa ya samu guri ya zauna akan kujera me zaman mutun biyu idanunshi na kan fuskar amminsa dake zaune fuskarta d'auke da annurin ganinsa duk cikin ya'yanta tafi qaunarsa saboda tausayin dake garesa, yana qaunarta da qaunar kannensa ,yana tausaya musu, duk abinda suke so zai musu batare da bata lokaci ba shine komai nasu ita da yaranta.
kannensa suka durkusa har
suka gaishesa ,bayan sun gaishesa kowacce ta samu guri ta zauna akan hannun kujerar da yake zaune.
yayi murmushi kana ya dan zamo ya gaishe da mahaifiyarsa "ammi Ina yini ?Lafiya lau ya gida ya fama da aiki ?
"alhamdulillah ammina ya fad'a tare da juyowa ya Kalli hally "Ina sadiq ko ya fita aiki ne ?bai fita ba father yana gida yanzu nan ya fita raka ya marwan bata qarasa rufe bakinta ba sai gashi ya shigo fuskarsa da murmushi dan tun daya ga motarsa a kofar gida yasan yazo ya gaishesa yana tmbyr me jiki jaguwa ya waske tamkar ba dashi yake magana ba.
ammi taso ta tambayesa abinda ya faru dashi jiya amman ganin Babu damuwa atare dashi sai zallar farinciki yasa ta kame bakinta sadiq ya samu guri ya zauna a gefen ammi yana sake tmbyrsa tanweer , ammi ta gyara zamanta tana cewa wacece babu Lafiya ne ?"budurwarsa ce ammi "ya fad'a cikin tsigar zolaya Jin haka yasa jaguwa ya waigo ya watsa masa katuwar harara "Kai haba sadiq yanzu daman yayanka yana da budurwa baka ta'ba fad'a min ba ? lallai kayi min laifi me girma zaka fuskanci hukunci ? Tayi mgnr kmr Adnan ba dan farinta bane, ta rasa dalilin da soyayyar dan nata yake hana kunyarta tasiri idan tagansa neman kunyar take ta rasa "Allah ammi Nima ban dade da sani ba "oh nace dai ta Kalli jaguwa banda abunka ai sai kayi magana a tura gidansu ba sai a had'a dana shafiqa ba a wuce gurin" .