← Book details Kuskuren Baya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 26 OF 160

Sashe 26

Kuskuren Baya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"subhanallah  tanweer  ta furta a ranta tana  mamakin  "wai yau itace a irin wannan  gurin wasu hawaye ne masu zafi  sukayi nasarar biyo gefen fuskarta tana k'okarin sharesu jaguwa ya  qaraso gabanta yana girgiza mata  Kai alamar kartayi kuka sannan ya  rungumota  jikinsa ta kwantar da kanta a faffadan qirjinsa dake fitar da sihirtaccen  kamshi , cikin tsananin  tashin hankali yasa hannunsa ya share  mata    hawaye  ya  sake rungumeta  tsam yana zagaye weist dinta da hannunwansa duka wani irin tsalle hade buguwar zuciya tanweer tayi  Wanda har hakan ya  haifar mata da tsayawan numfashi na wasu yan  mintuna haka duk wani tunani dake tafiyar da bugun zuciyarta sai daya motsa ta dinga Jin wani iri a gbdy ilahirin jikinta.
yau ce rana ta farko da jaguwa ya rungume mace acikin mutane batare daya    ji   komai ba ajikinsa  hasalima wani  sanyi  yaji yana bin jijiyon jikinsa ,bakinsa ya Kai cikin kunnenta yana mata rad'a  wanda hkn yasa tsigar jikinta tashi  "kukan ya Isa haka please  kar zazzabi ya kamaki "  cike da muryar kuka tace "me yasa ka kawo ni nan  ? shiru yay mata  tausayinta na kamashi  ya  d'ago  fuskarta  suna kallon kwayar idanun  juna can ya motsa lip's dinsa "baki so mu wuce na mai dake  gida  yanzu  ?shiru  tayi ta  cigaba da kallonsa  yayinda zuwa lokacin  idanun mutane sunyi caa akansu ciki  kuwa  har  da  abokansa  da  alqali daya samu nasarar  shigowa  "kiyi min magana idan baki bukatar kasancewa damu  anan na mayar dake " nan ma shiru tayi hawaye na sake  zubo  mata masu zafi da radadi "wai  kasancewa dasu ko su dawa oho masa ?tafiya ya soma yi daita tana makale ajikinsa har ya Kaita kan table din  daya fara zama ya zaunar daita a hankali .
kuka tayi sosai taki  yin shiru  yayi  mata magana yafi sau goma dan gbdy ya manta Kansa a gabanta  sai wani narke mata  yake zuciyarsa na sanyi akanta  sannan baya son rabuwa daita   shiru  tayi kawai tana makale ajikinsa  tayi  yawo  kasashen duniya sosai  amman bata ta'ba Kai kanta irin wad'an guraren ba sai gashi a kasarta ta tsinci  kanta da kyar ya rarrasheta  tayi  shiru ya bude mata kwalban malt  ya  Kai bakinta idanunshi na kanta  . suna  nan  zaune mawakiyar  ta fara bin Site by site  tana waka yayinda  mazauna  kan table   suka dinga mata liki har ta k'araso table din da jaguwa ke zaune  bai daga idanunshi ya kalleta ba sai anas ne ya taso daga mazauninsa ya shiga lika mata 'yan dubu day day ta dan durkusa tare da furta "thank you sir shiyasa nake son ganinka  sannan ta tsaida wakar tare da cewa ayi mata tafi nan take gurin ya d'auki tafi raf raf  banda jaguwa da tanweer , sautinta ne ya cigaba da karad'e gurin anas  ya tashi yana layi ya shiga rawa bayan ya gama rawa ya nufi gurin zamansa Yana rawa  aikuwa makiyar  ta biyosa nan gurin ya hargitse da dariya har shi   anas  din  dariya yake sakamakon ya fahimci abinda take bukata daga garesa kudi take so ya fito da bandir din  kudi ya shiga lika mata yana rawa irin tasu ta mashaya ."

Yammata  ne  su uku  zaune  acikin  runfa  me  zagaye  da wutar lantarki sai  tsirarun bishiyoyi   kowacce  daga cikinsu hannunta rike  da  karan    sigari da  glass cup dake cike  da  ruwan  giya "Kalli   d'an  iskan mutumin nan , ai na sha fad'awa  sweet  zahra  ta fita  hanyarsa  ta  tsaya taci  lokacinta  taki kamar jijiyarsa ce kadai ke da dadi , "ai  Ina  ganin sai  ta  tsinci  kanta a lahira  zata  gane  matakin  daya dace daita , sam  taki yarda tayi  muamula da masu bukatarta  inji cewar helen  "kyale  banza yanzu  dey  kirata tazo ta ganewa   idanunta  wata Killa  tasan  Inda  ke mata  ciwo  wallahi tunda ta had'u  da mutumin  nan komai nata  yayi  qasa Ina dalili  inji  cewar   hafcy no-no suna cewa mata haka kasancewarsa tana da  dukiyar Fulani over  "haka  za'a yi  hafcy  bari na kira shegiya ta bud'e jakarta ta  ciro wayarta  kira d'aya  zahra ta d'aga wayar   cikin  fara'a"   sweety nah  dake  haka  suke Kiran junansu  dashi "yes sweet  Helen  meye labari ne  ? ta  amsa mata   ciki fara'a.

   "sweety   kina  ina ?" Ina gida  kwance wallahi Ina hutawata  " bazaki  fito bane  ma yau  ? cikin Marairaicewa murya Zahra   tace "da wahala na fito Ina son na  cigaba da kame kaina a gida dan ta haka ne  kawai  burina zai cika akan Adnan idan ya daina ganina a guraren shakawata ko  hotel hotel   may be zai yi kewata  har ya nemini ,ni Kuma ta haka zan bijiro masa da lallai sai dai muyi aure "wani dogon  tsaki helen taja  "Kinga ki raba  mutane da zance wani  Adnan  mutumin nan ba aurenki zai yi ba sau nawa yana fad'a miki bazai aureki ba amman da yake ke karamin brain gareki kin kasa ganewa? "me Kuma ya kawo wannan maganar  sweety ? kin kirani ne  dan ki ta'ba zuciyata  ko me ? Ko d'aya na kiraki ne dan na fahimtar dake wani abu me mahimmam na tura miki Sako ta what's app dinki ki shiga ki duba  idan  km zaki iya zuwa  Rita  Lori  hotel yanzu  kina iya zuwa  ki ganewa  idanunki  komai  tana gama  fad'ar  haka ta katse  Kiran  .
zahra tayi shiru  sororo da waya a hannunta tana tunanin maganar Helen what's app dinta ta shiga nan idanunta suka ci karo da mugun Abu domin kuwa  adana  dinta ne rungume da  wata yarinya  da bata san  kowacece   ba , ta sake bude wani hoto su din ne yarinyar na tsaye a gabansa shi km  yana rike da kugunta wani irin abu taji yayi mata diran makiya a qirjinta nan take ta  fara  jin  zafi   a zuciyarta  tasa hannu ta dafe daidai saitin zuciyarta adalilin bugawar da take .

  take gumi ya shiga  karyo mata ciwon  daya dade yana damun zuciyarta ya sake taso mata ya mamaye kahon zuciyarta , wannan alamarin akwai ciwo, ciwon da mikinsa ke azabtar da zuciya da gangar jikinta ,ciwon da kullum yake qara girma acikin zuciyarta, tunda ta fara son Adnan ta tsani ganinsa da kowace mace sannan   Kuma  zuciyarta ke cikin tashin hankali , ta zabura  ta mike ta sauya kaya  riga fara sol  iya gwiwarta ta sakala jaka fara , haka ma takalimi fari   ta fito cikin sauri tana  Uber  ,cikin kankanin  lokaci mai Uber ya k'araso dan yana kusa  daita, ta shiga gidan baya ta kame zuciyarta na wani irin zafi da ciwon da batasan ranar dainashi ba "why Adnan?  me na
 rasa ? "me kake so ajikin mace da bani dashi ?.me wannan yarinyar ta fini dan Allah karka bari bakincikinka ya kasheni Ina sonka fiyye da komai ta k'arasa maganar tana goge hawayenta  .."

tana gama  karasowa Rita Lori ta sallami  me  Uber sannan ta  kira layin Helen kira daya  ta d'auka tayi mata kwatance gurin da suke  zaune ."ta k'araso ciki  hankalinta a matukar tashe  tana baza idanu taga ta  Inda jaguwa  yake  da yarinyar  dan  idanunta babu abinda suke son da burin  gani    agurin kamar  tagansa   aiko  cikin sa'a idanunta  ya  sauka akansa   makale da tanweer  kamar  zai  mata  numfashi  ita Kuma  ta d'aura  kanta a saman  kafad'arsa  saboda  baccin data soma  ji  ga sanyi gurin dake ratsa  jikinta ta shige masa sosai har suna  iya jiyo numfashin juna  tuni  idanun Zahra suka  kawo  ruwa  wani tunani yazo  mata  ko dai yayi aure  ne ?"  kai impossible ace  Adnan dinta  yayi aure Kuma ko yayi aure  bazai  ta'ba  zuwa da  matarsa gurin nan ba sai  dai  idan  sabuwar karuwa   yayi  wani  naunayen  ajiyar  zuciya ta sauke  ,hankalin   zahra yayi kololuwar tashi gadan  gadan  ta nufi Inda  suke  zaune  tana gama  Isa  gurin tasa kafarta  d'aya  ta  take kafar  tanweer  qara ta saki mara sauti tana furta " subhanallah   tare da  runtse  tsamammun idanunta  dake  cike da mayen  bacci  ,a hankali jaguwa yabi  inuwar da ya gani tsaye  akansu  itama tanweer  ta d'ago  domin taga  abinda ya take mata  kafa  kafin tanweer ta gama kare mata kallo har zahra ta cakumi wuyan rigarta da iyakacin karfinta  "dan  ubanki me kike  yi tare da mijin da zan  aura ? nan da nan jikin tanweer ya d'auki rawa  wata razananniyar tsawa zahra ta buga mata wanda yasa jikin tanweer ya sake d'aukar qyarma  zuciyarta ta karye hawaye ya soma sintiri bisa  kuncinta muryarta na rawa tace "ki...kiyi hakuri wallahi  babu komai a tsakaninmu kawai  tai ..."
"Shut up useless kawai  hakurin uwarki zanyi  ko da yake da ganin  nasan kema  sabuwar  shigowa  karuwanci  ce  bancin haka da  Koda  millioyoyin   kudi  ba zaki Kalli  Inda Adnan yake ba bare har ki yarda ya daukeki "inna lillahi karuwa?  ta furta kalmar a matukar firgice .

cikin tsananin faduwar gaba jaguwa ya lumshe sexy  eye's dinsa na second  biyu sannan  ya bude su fess   yana mai jin  bakinciki mara misaltuwa sam bai ji dadin Kalmar  data fadawa tanweer ba   murya qasa qasa yace " ke  wacce  irin mahaukaciya  ce  daga zuwanki kin  fara wa mutane  hauka saboda ke din mara mutunci ce ki saketa  kafin na tashi na  targadaki  yanzu  yayi maganar  yana  janye idanunshi  akanta tsayuwa zahra ta gyara sannan ta maida dubanta ga jaguwa tana  kira sunansa kusan minti biyar tana Kiran sunansa batare da ta saki wuyan tanweer ba  ranta ya Kai koluluwar baci wato cin mutuncinsa gareta yayi yawan  da  zai  mata a gaban  sabuwar karuwarsa yana jinta yaki amsa mata  yayi  kamar bai san da tsayuwarta ba "Adana !!!! ta qara Kiran sunansa a fusace wannan karon  idanuwansa  a  lumshe ya  mike ya ɗauketa da wasu maruka har biyu ajire   da sauri  ta saki  wuyan  tanweer  zuciyarta na bugu  da  karfi "ka mareni adnan ?na mareki idan kika sake wata magana ko kiran yarinyar nan  da karuwa sai na  ballaki  sannan   minti biyu  kawai  na  baki ki 'bacewa  idanuna banason ganinki .
Chapter 26 · 0% Book details