Sashe 37
Kuskuren Baya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
"Dan Allah kawata ki cire kishin nan a ranki mude bukatarmu ta biya ya rabu da yarinyar shine abinda muke so , har suka k'araso tasha magana daya dai suke yi blessing na kokarin shawo kan Zahra , shiru zahra tai taki cewa komai zuciyarta na tuttukin bakinciki Adnan zai kusanci tanweer Kuma shi zai amshi budurcinta.
bangaren tanweer kuwa taki cin abinci, yadda ya kawo mata abincin jiya haka ya fitar dashi bata ci ba ,ai ko shima ya hau dokin zuciya yaki bin ta kanta bare ya rarrasheta ." duk yadda blessing ke Jan zahra da hira acikin mota ta kasa cewa komai har suka sauka a lagos kowacce ta kama gabanta gbdy Zahra ta kasa samun kwanciyar hankali sam bata ji zata iya wannan kasadar sai tayi kmr ta kira boka tace ta fasa aikin sai Kuma ta fasa ."
*****
Zaune jaguwa yake cikin baban falonsa system ne a gabansa yana aiki eku ya shigo tare da rusunawa ya gaishesa ya amsa batare daya d'ago ba eku ya soma magana cike da ladabi "boss kamar ka manta da wancan mutumin " Jaguwa ya d'ago ya kallesa a tsanake yana bukatar qarin bayani "wancan mutumin dakace mu dauko a Rita Lori hotel mu killace maka shi " sai lokacin jaguwa ya tuna ya lumshe idanunshi "Yana Ina ne ?"yana boys quarter ya gyada Kanshi kawai ya cigaba da abinda yake eku bai wuce ba sai da jaguwa ya gama abinda yake ya mike yana tafiya kamar baya son taka kasa yayinda eku ke biye dashi har suka k'araso bakin kofar d'akin da alqali yake , eku yayi saurin bude masa kofar d'akin , alqali najin motsin mutane ya shiga zare Ido jaguwa ya tsura masa Ido ya rame sosai rama ta tashin hankali acikin kwana biyu da yayi wanda idan ka kallesa bazaka sake marmarin kallonsa ba duk ya fita haiyacinsa, zaune yake jugun hannunwansa da kafafunsa duk kulle su da handcuff kamar wanda yake prison a hankali jaguwa ya shiga Taku a hankali yana masa wani wulakantaccen kallo sannan ya tsaya a tsakiyar d'akin yana cewa"waye Kai menene yasa kake bibiyata ?alqali da bakinsa ya bushe sosai ya fara magana cikin wahala "babu dalilin da yasa na bibiyeka ya karasa maganar cikin tsananin tashin hankali .
"waye Kai ?"shiru alqali yayi ya kasa cewa komai jaguwa ya juya ya soma tafiya "Ina ganin azabar yunwar da'aka masa bai ishesa ba ka cigaba da barinsa babu ci babu sha har ya zamo sanadinsa " alqali wanda muryarsa ta fara dashewa babu karfi a tattare dashi yace "kayiwa Allah kayi hakuri na tuba "jaguwa ya cigaba da tafiya batare da juyo ba "idan na fada maka bazaka kasheni ba ?"yayi masa bmbyr a gigice cak jaguwa ya tsaya tare da goya hannuwansa duka a baya ya juyo
ya tsura masa Ido alamun yana sauraronsa "ni ..ni ...sai Kuma yayi shiru yaji tsoron sheida masa cewar shi din jami'in sirri ne " kayi hakuri dan Allah ka tausaya min nayi kuskure bazan sake ba "runtse idanu jaguwa yayi ,ba dan baya son aikata kissa a rayuwarsa ba da babu shakka da sai ya shake wuyan wannan
mutumin da hanunsa har sai ya mutu
"kaga nayi kama da wanda za'a bibiyi rayuwarsa for the last time ka fad'a min wanda yasa ka bibiyeni? yayi masa tmbyr yana hade fuskarsa kmr hadari. shiru alqali yay ya kasa magana Dan Bai San abinda zai ce ba har kusan minti biyar Yana tsaye yana jiransa ,eku ya Ciro karamar pestol ya saita gefen brain dinsa "na baka minti biyu ka fadi Wanda ya sakaka kafin na tarwatsa brain dinka na aikaka lahira "wa ..wallahi babu kowa Ina tafiya ne na gansa tare da yarinyar minister of health da ake nema shine na dinga binsa a baya naga Inda zashi daita wallahi byn wannan babu Wanda ya aikoni .
"ka cigaba da ajiyarsa anan har sanda zai fadi gskiyar wanda ya aikosa sannan ka ciyar dashi da gari zalla da ruwa ,ruwan ma kwatan tea cup haka ma gari muddin yayi wata bai fadi Wanda ya aikosa ba ka tashesa aiki yana gama fad'ar haka ya fice daga daki haka ma eku ya nufi kofar fita kmr wani zautacce alqali ya rarrafa da gwiwawinsa yana k'okarin riko ka'fafun eku Amman Ina tuni ya fice ya maida kofar ya rufe cikin rashin tausayawa, hawayen danasani suka silalowa alqali ya fara zubar da hawaye yana adduar Neman mafuta "me yasa ka biyosa gashi ka jefa rayuwarka cikin hatsari kuka yake sosai kamar karamin yaro."
******
"Wai waye wannna jaguwa din ne ? waye km ?.gbdy sai da tanko gote ya kira sunayensu d'aya bayan d'aya ka amsa min tambayata boka " ya san sunansu ne a bakin wasu daga cikin mufukan' yansanda da sukayi attacking dinsu a wancan satin ". shiru bokansa yayi yana dube dube acikin kasa ,abubuwa da yawa ya gani akan jaguwa km abun ya balain tsoratar dashi dan har wani gumi ya had'a da kyar yayi jarumtar yin magana "wannan yaron da Jamar'sa rikakkun y'an fashi da makami ne da suka ga gari kowa acikin garin nan yana da karfin da zai iya karawa da kowa acikin garin nan ,haka yana da karfin da zai iya shiga duk Inda yaso yayi sata batare da an dakatar dashi ba , yafi karfin kowa duk yadda kake tunanin yan fashi sun zarta tunaninka basa ji basa gani akan aikinsu sai dai abinda na gani a dubana shi jaguwa yana fanshinsa ne akan masu kudi da azzaluman kasar nan , yana da hatsarin fuskanta it's not easy to be known as the CEO of armerobber's association .
wannan ya wuce da tunaninka ranka shi dade karka bata lokacinka gurin sanin ko shi waye ko matakin d'auka akanshi tunda har ya barka da ranka da lafiyarka sai mu godewa Allah domin shifa satarsa me dalili ne Kuma ya dade acikin harkar Kuma shi kad'ai yasan abinda ya taka wanda yasa ya gagari kasa da kasa har da jami'an tsaro suka kasa kamashi tanko gote ya numfasa kana yace "zan so yayi aiki a karkashina domin irinsa nake nema "bazai had'a Kai da Kai ba dan baya zalinci burinsa ya taimakawa talakawa marasa galihu Kai Kuma burinka ka danne hakin mutane da talakawa "wai boka ya kake min magana haka ne ? " kayi wani Abu da zai kawo kanshi gareni "babu abinda zan iyayi domin duba taurarinsa ma kawai zai iya sa mutun cikin tashin hankali, kaima idan baka cire hannunka akansa ba zaka iya rasa komai naka jin abinda boka yace yasa tanko gote shiga damuwa bai sake cewa komai ba ya kakkabe bababan rigarsa ya baro gurin boka da zumar zai nemi had'in kan jaguwa ta kowani hali ".
*****
Jaguwa na zaune tare da abokinsa da yaransa a gurin shakatawarsa gabansu kwalban giya ne yayinda kowannensu hannunsa ke rike da karan sigari har jaguwa suna tautaunawa akan sabon aikin da zasu fita zuwa garin Ogun state sai ga me gadinsa ya rusuna ya gaishesa tare da cewa "ga wannan dattijon daya zo neman taimakonka ya dawo ranka shi dade" "shi da nace ya dawo karshen sati amman dai shigo dashi kawai " mai gadi ya juya da sauri jaguwa ya kashe sigarin hannunsa dan yana matukar jin kunyar wani yaga yana shan sigari eku tattara gurin nan kafin azo da dattijon nan take yabi umarninsa .ko cikakken minti biyar ba'a yi ba sai ga me gadi ya dawo tare da mutumin da yaronsa wanda bai wuce shekara talatin ba dattinjo na kokarin rusunawa
jaguwa ya tsaidashi yana nuna masa gurin zama "ka zauna baba dattijon ya zauna a Inda ya nuna masa yana rawar jiki, gbdy su jubi suka gaishesa ya amsa yana Saka musu albarka "d'ana ga yarona nazo dashi "jaguwa ya waigo ya kalli Inda yaron yake tsaye cikin wasu kod'ad'un kaya marasa fasali da sauri matashin saurayin ya dan rusuna ya gaishesa ya amsa da Kai tare da cewa " ya sunanka sannan wani course ka karanta ? " sunana aliyu Ahmed abinda na karanta lissafi wato accounting .ya bashi amsa cike da girmama.
shiru jaguwa yayi yana nazarin yaro kafin daga baya yace "shikenan zaka zauna damu ka zama dan aikenmu kafin lokacin da zan samo maka aiki inshallahu , dattijon najin haka ya fara hawaye yana godiya " na gode na gode Allah yayi maka albarka "karka damu baba mu daman aikinmu kenan taimakawa marasa shi ,aiki kuwa ka fara hasasho ganinsa cikin jerin ma'akatan banking kasar nan yana gama fad'ar haka yasa aka dibo kudi masu yawa aka bawa dattijon "baba ga wannan kudin kaje dashi kayi bukatunka dasu, sosai dattinjo ya zube yana godiya kafin daga baya yay sallama dasu ya wuce ya bar d'ansa ."
******
D'akin taro ne dake cike da manyan jami'an tsoro kowannensu sanye da kankinsu na aiki police, yayinda gabansu ruwan roba ne mai sanyi da abun magana a hankali cp ya fara magana cikin tsadaddan turancinsa "
Daga ashirin da biyar ga watan daya na wannan shekarar ta 2021 zuwa ga karshen shekarar shadaya da muke ciki an samu farmarki ta'addanci a qalla ashirin da biyar a cikin garin nan, duk da k'okarin da jami'an tsoro keyi akan suga sun kama wadan nan yan fashi abun ya faskara wanda ni a nawa tunanin ina ganin akwai manyan kasan nan dake mara musu baya, taya zamu samu nasarar kama wannan mutumin dake jagoransu wanda shi ke shirya komai na ta'addanci ? cp ya karasa maganar yana kallon hoton jaguwa dake ajiye akan makeken table din gabansa ." yanzu haka wannan shine tantiri na biyu da ake nema acikin kasar nan idan kuma acikin garin nan ne shine na daya , jaguwa kenan duk wani sata da'ake wa manyan kasar nan da yan siyasa da hannunsa aciki abun mamaki yadda wasu daga cikinmu suke bashi kariya ta hanyar sanar masa da halin da'ake aciki, a offishin hukumar tsoro kuma suna yi masa duk wani alfarma daidai da wani mai fada aji a kasar nan ".