← Book details Kuskuren Baya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 46 OF 160

Sashe 46

Kuskuren Baya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

wani  irin  sarawa kanta ya dinga yi da  karfi  kmr zai ra'be gida biyu  tayi matukar firgita da  Jin mgnr shi , ta d'auka zai tsorata da maganarta  sai dai taga sa'banin haka atattare dashi sam shi din ba matsoraci bane zuciyarsa  a dake take ,kallonsa tayi tare da ciza lips dinta  batare data sake yunkurin cewa komai ba "ki tashi ki 'bace min da gani  banason ganin wannan banzar   fuskarki, karki qara kuskuren zuwa  Inda nake sannan   duk abinda kikaga  Ina yi miki karki d'auka so ne , ba so bane tanweer  dan ko digo d'aya na sonki babu shi acikin  zuciyata  bakya cikin  irin tsarin matan da zan  so , idan Kuma kin koma gaban iyayenki  dan  Allah karki fasa idar da nufinki  akaina  kiyi  Ina jiranki  wani irin zafi da ciwo kai ne me karfi   yayi mata diran makiya gbdy  jikinta ya sake d'aukar zafi tayi karfin halin dafe kanta cike da sanyi jiki ta mike  ta nufi hanyar komawa d'aki  sai da tayi da tasanin fitowarta ."

da kyar ta  dinga d'aga ka'fafunta da
idanu ya bi  bayanta  yana kallonta  rai a 'bace  har ta bace wa  ganinsa sannan ya d'auke idanunshi  yana   fesar da iska zuciyarsa ban da zafi babu abinda  take sai  faman  tsaki yake ja da karfi  ya fad'a kan kujera  ya runtse idanunshi tare dafe goshinsa cikin haka abokansa suka shigo suka samu guri suka zauna   ganinsa haka yasa  suka fara tmbyrsa abinda ke damunsa shiru yayi yaki cewa komai  sai tsaki yake ja anas ya dafa kafadarsa "meye damuwarka  Kuma ? Still shiru yayi yana ciza lip's dinsa jabir da jubi suka tashi suka fita  dan sun San  tunda yayi haka ba magana zai yi ba "ya kamata ka rage  damuwar nan  jaguwa nasan duk damuwarka  bata wuce akan yarinyar nan ba "Ina matukar tausayin yarinyar nan  anas amman ita  burinta bai wuce taga bayana ba
yayi mgnr a fusace idanunshi sun yi jajur "kayi hakuri nasan da haka nasan kana tausayinta da qau...." wani irin   kallo yayi masa wanda yasa anas ya hadiye abinda zai fad'a "na sha fad'a maka ka daina cewa Ina son yarinyar nan amman tunda haka kake tunani ka zuba Ido zan baka mamaki"

"yauwa haka nake so Ji  abokina Ka bani  mamaki  ka rabu daita mu hutu tunda baka sonta banga amfanin   zamanta damu ba  dan kasancewarta damu matsala ne mu sallameta kawai  anas ya fad'a yana cigaba da   bashi shawara  akan tanweer ..."
Ita Kuwa tanweer tana shiga d'akin ta shiga har  gitsa d'akin tamkar mahaukaciya  a karshe ta fad'a kan gado hawaye na zubo mata sharrrrr akan quncinta  tasan hawayenta nada halaka da bakaken maganganun daya fad'a mata , zuciyarta ta karye madadin  soyayyarsa ta bar zuciyarta kamar yadda take buri sai ta  dawo mata sabo fil tunda take baa ta'ba kallon idanunta aka furta ba'a sonta ba sai Adnan shine mutun na farko jikinta ya sake d'aukar zafi sosai  wuni ranar bai shigo Inda take ba har dare  ita Kuwa zazzabi da  dacin maganarsa  da ciwon gajiyar sex din  jiya suka hade  mata  guri d'aya tayi kuka har hawayenta suka kafe bai shigo  Inda take ba ya kama kanshi dan yasan koya shiga gurinta  wani rashin mutunci zata masa shi Kuma bazai dauka ba ."

washegari  tun karfe goma suka bar gidan batare daya lekata ba , dan har lokacin haushin abinda tayi masa bai bar zuciyarsa ba  Kowani titi jami'an tsaro ne over fiyye da duk wani abun hawa, duk motar  data  zo wucewa sai an tsaresa an bincika ciki da wajenta  tun daga nesa suka hango motar jaguwa tun kafin  motar ya gama karasowa garesu suka daga ma eku  hannu alamar ya tsaya a hankali motar ta rage gudu  tare da k'okarin yin gefen titi ,a hankali  eku yayi waning  glass din motar  yana mazurai  ,daya daga cikin police officer ya dan leko cikin motar, cikinsa ne ya duri  ruwa  sakamakon ganin pesto a hannun jubi ,  ya ware Idanunsa sosai yaga ak 47  akan cinyar eku  dake tuki ya Kai Idanunsa baya nan yaga sabon tashin hankali domin kuwa manya  bindigu  ya gani akan cinyar anas da  jaguwa wanda ya kawar da fuskarsa gefe yana kallon titi da sauri Police office's  din  da suke  zagaye  da motar suka yi baya jiki na rawa .
daya daga cikin police yace "sorry ban San ku bane you can be on your way " a hankali glass din motar ya fara yin sama motar ta fara move  police sukayi sauri  suka tsaida wani me adaidaita suka duba cikin motarsa kana suka bashi hannu ya wuce direct   to Ogun state suka nufa   basu  suka dawo gidan ba  sai daf da sallar magriba  wanka ya fad'a tare da alwala ya fito ya soma k'okarin gabatar da sallah  byn ya  idar da sallah magrib ya nufo d'akinta    hannuwansa duka zube cikin aljihun wandonsa   ya  hangota   kwance tayi ruf da ciki   ko motsi kirki bata iyawa , ganin yanayinta  yasa qirjinsa bugawa da sauri  sai dai bai nuna hakan ba a fili   tun kayan jiya ne sanye  ajikinta, harara ya wurga mata  sakamakon tuno abinda tayi masa   a natse ya qaraso Inda take ya Kai hannunsa wuyanta nan yaji wani zafi ya ratsa tafin hannunsa  kmr ta buge masa hannu sai dai bazata iya ba dan jikinta babu karfi "baki da lfy ne ?ya tambayeta  banza  tai masa taki motsa labbanta  "raguwa banza kawai  ya fad'a acikin zuciyarsa ."

"Kinyi  sallah ma kuwa  ?
Still shiru tayi masa bai damu ba ya cigaba da mgn "idan kinyi sallah  ki canza kaya ki sameni a falon dan naga alamun tun kayan jiya ne ajikinki  yana gama  fad'ar hk ya juya har ya kai  tsakiyar daki yaja ya tsaya yana cewa  "na sanki da shegen  d'aurin Kan tsiya   ,minti goma kawai  na baki ki sauya kaya ki  fito dan Allah karkiyi abinda nace ya cigaba da tafiya ya  fice daga daki .
Babu yadda ta iya ta mike ta shiga bayi alwala tayi ta fito ta tada sallah  byn ta idar taki sauya kaya  kmr yadda ya bukata ta fito , yana tsaye tare da friends dinsa  ta fito duk suka tsura mata Ido suna kallonta  maganar jaguwa ta jiya ce ta fad'o musu sosai suka qura mata Ido
suna yabawa da kyawunta .
yaji motsin fitowarta amman yaki juyawa "muje  ko yace daita sannan ya fuskanci abokansa "zan dan fita amman bazan dade ba zan  dawo  ya karasa  maganar ya  nufi kofar fita .."Tabi bayansa tana adduar Allah yasa gidansu  zai kaita ta huta  ..

suka bisu da kallo kowannensu  na maganar zuci .yana gaba tana biye dashi abaya har suka ƙaraso inda motarsa ke fake eku na ganinsa ya taso  da  hannu  jaguwa ya dakatar dashi ya   buɗe  murfin motar ya shiga  itama ta shiga yayiwa motar  key ya tada motar  mai gadi  na ganinsa yayi hanzarin tashi ya bud'e masa yana daga masa hannu ya fice ya hau kan titi tafiya kad'an yayi ya waigo  gefen da take zaune   cike da takaici"sai nace kisa  seatbelt zaki sa kome  ?"  ya tambayeta cikin yanayi na ɗan jin haushi. Janyo belt tayi ta saka batare da tace umm ba bare Uhmmm sai  qirjinta dake bugawa  kamar zai fito waje.Sunyi tafiya me d'an nisa  akan titi bata  waigo ta kallesa ba,  sai faman  wasa take da yatsun hanunta tana addua acikin ranta  ."

Kai  tsaye   1829 plaza   ya shiga   har    ya  gama daidaita parking ɗin motar bata d'ago ba  ya ciro wayarsa ya lalu'bo number aliyu  yayi  dealing     ya manna a kunnensa maganar minti  biyu yayi ya katse ya kira sadiq shima bai dade ba yayi disconnect din Kiran ya  fito  ya barta ya kulle motar  gbdy, taja tsaki aranta  ,shiru tayi tana zance zuci da dube dube da  idanunta sai lokacin ta fahimci  inda ya kawota,  kallo d'aya tayiwa gurin ta fahimci gurin sun ta'ba zuwa da ib  ta cigaba da zance zuci kmr ance ta Kalli kan kujerar daya tashi idanunta suka sauka akan wayarsa ta d'auka da sauri ta shiga daddana code din data ga ya danna jiya tana addaur Allah yasa haka ne 2020 ta danna sai ga wayar ta bud'e  jikinta  na rawa tashiga dealing number dad dinta  kira  biyu ya d'auka bakinta na rawa tace "dad ..."!daga  can bangarensa a zaune yake amman sai daya mike tsaye cikin firgice yace"tan !!!  where are you ? dad ka zo  1829  plaza ...." ai bata Kai karshen maganrta ba taga yana tahowa da sauri ta sauke wayar a kunnenta tana kokarin goge number ta kashe waya gby da sauri ta ajiye wayar zuciyarta na bugawa da karfin gaske ta sunkuyar da kanta tana danne kukan dake kokarin fito mata ".

ya bude  murfin bayan motar ya jefa ledar hannunsa sannan ya bude   banagaren mazaunin  direba ya shiga yaja  Kai  tsaye fmc  hospital ya nufa a hankali ta d'ago idanunta nan ta fahimci asibiti ya kawota yayi parking Yana kokarin fitowa  yace "fito muje" ya faɗa yana ciccin magani .jiki a sanyaye ta fito daga cikin motar ya rike tsintsiyar hannunta gam  cikin nashi suka jera koina hasken fitilu ne  kowa ya gansu sai ya sake kallonsu dan bakaramin dacewa sukayi da juna ba  zaka d'auka su din mata da miji ne ,yayinda gabanta ya dinga  faɗuwa aranta  tace   "Allah Ka bani iKon tserewa yau daga hannunsa  ".
Tafiya   kad'an sukayi taga sun tsaya  a bakin wani  ƙofa  ya Kai hannu yana  knocking din kofar   daga ciki aka bashi izinin shigowa." shiga muje "babu yadda ta iya ta shiga kmr zatayi kuka  Sadiq  na ganinsu  ya miƙe  yana fad'ad'a fuskarsa da murmushin jin dadi  Dan bai taba ganin yayansa da wata  mace  ba sai yau shiyasa murnarsa a fili take da hannu ya nuna mata gurin zama ita Kuwa kallonsa take saboda tsananin kamaninsu zaka rantse tagwaye ne , babu shakka wannan mutumin dake gabanta  dan'uwansa ne km na jini dan kamar ta baci a natse muryarsa ta fito tmkr ta dan'uwansa   "father ya sunanta ne ?"ga tan a gabanka ta fad'a maka  sunanta tunda shishigi kake son yi ".
Chapter 46 · 0% Book details