Sashe 110
Kuskuren Baya Part 1 Complete Hausa Novel · about 6 min read
“Tanwer! ya kirata cikin wata kasalillyar muryasa dake tattare da tsananin shaawa ,ta tsura masa ido kawai tana kallonsa gabanta na dokawa batare data amsa ba “I dont wont to see your tears ya fada yana kashe mata idonsa daya “ nan take ta goge hawayenta tana kallonsa “ki saki fuskarki sannan ki bani labari wanda zai kwantar min da hankali if not zanyi miki abinda yafi na farko kuma anan dan haka ki bari mu rabu lafiya kafin nayi miki karfa karfa na gwada miki kunjina ya zarta duk yadda kikayi tsammani .
jarumta ta sanyawa jikinta sannan ta saki fuskarta ta fara magana a hankali "inda banyi tsammani ba anan na fadi sai dai banji zafi ba tunda adalilin kallonka ne, shiru yayi yaki cewa komai ya cigaba da kallonta yana murmushi daga ciki domin dai yasan ta rasa abinda zata fada ne "adnan ..!"
Ta kiran sunasa a shagwabe ya jita sarai amman yaki ansawa ya cigaba da kallonta murya a shagwabe tace “kace na saki fuskata nayi ,kace na baka labari gashi nayi amman kayi shiru kana kallona inata magana kaki kace komai “
“Baki fada abinda ya kamanta nayi magana bane ki cigaba ina jinki idan akwai abinda zance zanyi .
“Kana jina?ya gyada mata kai alamun "eh!tare da fito da bindigar pistol ya ajiye a saman table din gefensa dan ya sake tsoratata Da sauri ta zaro idanuwanta waje cikin tsananin tashin hankali tana dafe qirjinta da duka hannuwanta muryarta a sanyaye tace “dan girman allah ka maidaita mutane na kawo min kayan marmari a matsayin kayan dubiya amman kai ko sau daya baka kawo min komai ba sai bindiga zaka fito min daahi ?".
Ta karasa mgnr tana sake canza fuska tamkar an aiko mata da sakon mutuwa "gasky ban gode da zuwanka nan yau ba.."
Ganin yadda ta fassara abun yace "Ammmm….. "
tayi saurin katsesa ta hanyar cewa “No karka ce min komai ka dauka kawai ka maidaita inda ka fito daita tun kafin mumy da mutane suzo su gani na shiga uku .
naunayen ajiyar zuciya ya sauke da karfi sannan ya dauka ya soke bindigar ajikinsa shiru ne ya ratsa dakin na tsawon minti shabiyar banda saukar numfashi su baka jin komai a dakin kowannensu da abinda zuciyarsa ke tsakawa akan danuwansa ganin yadda ta hade rai tana hura hanci ya furzar da iska mai zafi sannan ya bude bakinsa da kyar "karki dauka wani abu ,nayi haka ne dan na takureki amman ban san hakan zai bata miki rai ba yana rufe baki mumy na turo kofar dakin bakinta dauke da sallama a hankali ya dago ya dubeta yana amsa sallamarta ta tsaya abakin kofar dakin tana kare masa kallo sama da kasa da sauri ya dan rusuna ya gaisheta tare da sunkuyar da kanshi kasa yana mai jin tsananin faduwar gaba da kunya.
"wannan shine adnan ?" ta fada tana kallon tanwer ta gyada mata kai tana wasa da yatsun hannunta,
gaban mumy ya shiga faduwa "wannan fuskar kamar ta taba ganinta amman wallahi ko zaa daura mata bindiga a yanzu ta manta inda tasanta amman tabbas ta san wannan fuskar bata sake cewa komai ba ta karasa inda table din da ake ajiye abincin mara lafiya ta ajiye basket din hannunta ta juya ta shiga wani karamin daki a lokacin ya dago kanshi ya bi bayanta da kallo yayinda tanwer ta rike habarta tana kallonsa shi kuwa tunanin yanayi da mumy ta shiga data ganshi yake so yake ya gano abinda ke tattare daita ya soma kokarin mikewa ta yatsina fuska alamun bata son ya tafi "mutane suna mana kallo wani irin wanda shi kanshi aikin fashi da muke muna yi né domin raya wasu da kwatowa wadan da aka zalinta hakinsu "nasani amman su mutane wani irin kallo suke muku.
"ku barsu a haka amman babu wani bambamci mu din kamrku muke idan ma akwai bambamci kadan ne "haka ne allah ya muna min ranar da zaka ajiye wannan aiki ,wallahi da har aikin haji zan koma domin muna farincikina da godiya ga allah ".ta karasa fadar haka tana sakar sakar masa murmushi , yay mugun tsareta da rikitattun idanunshi yana kallonta kafin daga bisani ya sakar murmushi sannan yay mata sallama "zan wuce zan kiraki da daddare naji lafiyarki ya soma taku a hankali tabi bayansa da kallo tafiyarsa kamar ta maaikaci kaki sam bayi kama da dan fashi ba uniform yafi dacewa dashi .
Ahankali ta lumshe idanunta tana jin wani iri yanayi ajikinta bata jin zata iya hakura dashi ko tayi fushi dashi na wani lokaci né zata huce komawa tayi ta kwanta tana tuna moment din da suka kasance tare mumy kuwa bayan shigarta daki soja kaninta ta kira a waya byn ya dauka suka gaisa tace “acikin abokanka da kukayi karatu a NDA waye adnan ?a zaune yake amman sai daya zauna saboda tmbyr datai masa ta kusan mintuna shabiyar tana sauraronsa akarshe sukayi sallama ta katse kiran ta koma inda tanwer ke kwance ta kira sunanta.
Ta bude idanunta da kyar sannan ta yunkura ta mike ta zauna tana cewa “mumy ya kika ga adnan dina?mumy tayi murmushi “tanwer kenan gbdy soyayya ta caczaki idan aka ce min zakiyi kaca kaca a soyayya zan karya sai gashi ina gani da idanunta allah yasa kar soyayyar wannan mutumin ya zautar dake.
Allah ma bazai sa ba mumy ai ya cancaci aso ne har ma fiyye da haka mumy ta dauki pillow kujerar da take zaune akai ta wurga mata “lallai tanwer allah ya shirye ki ya kuma tsare min ke daga sharrinsa “Ameen mumy amman ya kika gansa yayi ko bai yi ba ?.
“Perfect! mumy ta fada tana mikewa tsaye bari na zuba miki abinci dan soyayya ta mantar dake yunwar da kika kira kina ji ta karasa ta bude kular abincin data kawo tanwe ta mike ta soma tafiya tana dingisa kafarta daya ta karaso inda mumy take tsaye tana zuba mata abinci a plet “mumy dan allah kiyiwa dady mgn kema ki yarda da aurena dashi ni kuma zanyi kokarin naga ya canza .
“abinda nake ta kokari fahimtar da dad dinki kenan yaki ya kafe akan lallai bazai yarda ba intakaice miki yace ko mutuwa zakiyi abarki kiyi amman bazai yarda da wannan auren ba “haba mumy kiyi duk yadda zakiyi dady fa naji dake yana kuma jin maganar ki ,wannan karon yaki ya lashi takobin yaki matsalar dai aikinsa ta juya ta ajiye plet din abincin akan karamin table ,zoki zauna kici kasa bin umarnin mahaifiyarta tayi ta tsaya tana kallonta ranta duk a dagule,mumy ki tsaya min dan allah ni kuma nayi miki alkwarin bazan auri adnan da wannan saba’ar ba wallahi dana auresa a matsayin dan fashi gara na mutu …”
Shiru mumy tayi tana dubanta tare da nazarinta tabbas maganarta da yanayinta ta nuna har cikin zuciyarta haka take nufi ,”zanyi kokari tanwer nima yaron ya kwanta min arai.