← Book details Kuskuren Baya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 24 OF 160

Sashe 24

Kuskuren Baya Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

......Cike  da   dakiyar    zuciya   alqali   ya   cigaba  da   bin  bayan motar   jaguwa    land  cruiser   prador   yana sake   neman   layin  IB  domin  bashi  direction  din  Inda  yake a daidai wannan   lokacin   sai  dai  Kiran  na   shiga   ba'a  d'auka   ,ya   kira  ya  kai sau   goma    bai    d'auka   ba  wanda a  wannan    lokacin   nazifi  da  alhj  Tahir  da    hjy    baseera    ne  tsaye a kanshi     nazifi   na  qakokarin   bashi  taimakon   gaugauwa ,   haushi  ya  kama   alqali   ya   ciza   gefen  lips dinsa   yana    dukan    sitiyarin  motarsa  "oh  my goodness   ko   me  yasa  yaki  d'aukar  Kiran yanzu bayan  bamu  gama  wayar  ba ya  ajiye   ? yayiwa   kanshi   tambaya  yana  d'an  rage  gudun  motarsa   dan  kar  jaguwa  ya  fahimci su yake  bi  ."

yayinda   a hankali  motar  jaguwa  ke  sharara  gudu  akan  titin  onipan a natse    ya  d'an  juyo  gefen  da  tanweer   ke   zaune   shiru   sanye  da   doguwar   riga   pinky  colour  ta  yane kanta   da  mayafi   baki   haka ka'fafunta   sanye  suke cikin   baby  shoe  baki  masu  matukar   kyau  tsintsiyar  hannunta  d'aure da agogo fata   baki   duk  jaguwa ne  ya  bata  su a  wannin da  suka  gaba tare da yi mata  albishir  din  maidata  gidan iyayenta   ,  kayan  sun   amshi   jikinta  sosai    kamar  dan ita aka  yisu .
a hankali itama  ta  juyo  cike da  natsuwa  fuskarta  d'auke da  murmushin  jin dadi zata  gida  taga iyayenta  cikin  sa'a shima ya Kalli Inda  take  idanunsu ya tsarke   cikin  juna  wani  irin  bugawa  qirjinsu yayi , alokaci  d'aya  sukai  shiru tare  da  tsurawa  juna idanu   gbdy  suka  kasa  d'auke   idanunsu .
a cikin  zuciyarsa yake  yabawa kyawunta   "hakika   tsarki  ya tabbata  ga ubangiji  daya halicci   wannan  yarinyar ,  kallo   d'aya  zaka mata kasan  kyakkyawa ce ajin  farko  ."

a natse   ya d'auke kyawawan  idanunshi  acikin  nata sakamakon ganin  yadda ta kafe shi da nata  idanunta da suka  wadatu da zararan gashi  Ido  gashi  ko kifta su  bata yi  shi  kuma mutun  ne  da  bai fiyye son  kallo  ba  bare kallo irin  nata  dake saukar  masa  da kasala tare da  sha'awa  me  tsayawa arai  , dan  nan take   kallonta  kesa   yanayin  mutun   ya   sauya  batare daya  shiryawa hakan ba." kasa  d'auke idanunta tayi   daga  kallonsa saboda  baiwar  kyau da  Allah   yayi   masa ta sha jin mutane na yabawa kyawunta haka zalika  idan ta Kalli kanta a  mirrow tana  tabbatar da abinda mutane ke  yawon  fad'a  akan  tsarin jiki da  kyawunta  sai dai  ko kusa bata kai shi komai  ba ,  dan  idan  tana  gabansa  raina  komai  nata take domin gani take  ya  fita  komai  bama za'a a had'a  ba .

muryarsa  a  kasalance ta  fito kmr baya  son  yin  magana  "ki  daina yiwa  namiji  irin wannan kallon  domin  duk  macen dake  kallon  nmj  haka   yana  nuna alamun bata da  cikakken   tarbiya  ,mace  da  kunya da kauda Kai   aka  santa  " ya  qarasa maganar   yana   jan  dogon  tsaki  dake   'batawa   duk   wanda  akayi dominsa  rai , runtse  idanunta tayi gam  tana  zance zuci  "nice  mara tarbiya  sannan mara kunya ?"tayiwa kanta  tambayar  ranta na quna da tuttukin   bakincikin  daya  maye gurbin  farincikin  dake  kwance a fuskarta ,  idan  akwai abinda ta tsana a rayuwarta  bai  wuce wulakanci irin wannan  ba  , kusan    second  biyu  tayi  idanunta na runtse  kamar  bataji abinda  yace   ba  , cikin  natsuwa taje  d'aura   laulausan  tafin hannunta saman   kushin  din  kujera  domin gyara   zamanta  taji  ya sauka  akan  laulausan  hannunshi   nan  take  yaji  qirjinsa  ya  cigaba da  bugawar da yake , itama  qirjinta ya  shiga dukan uku  uku  dan  wani irin zirrrrrrrrr taji lokacin da hannunta ya sauka a nasa  .

ya  sauke  wani zazzafan   ajiyar  zuciya da  numfashi alokaci d'aya ,
a hankali tayi karfin halin d'auke hannunta  dake saman nashi  a dalilin  jikinta  dake  kyarma  ta soma magana  cikin  fushi da bacin rai   "karka  sake  furta  min  wannan kalmar  domin  kuwa kallon  nmj    bashi  ke  nuna  rashin tarbiya ko  rashin  kunya   ba dan haka bana son sake jin   kalmar  gareni  domin ni din macece  me tarbiya da kima  idan Kai baka  ganin kimata akwai dayawa masu gani  ta  k'arasa  maganar hawaye  na  gangarowa akan quncinta ,ta sake kawar da idanunta sosai  tana goge hawayenta dake tsiyaya  "wani kallon banza ya watsa  mata mai  hade da harara  " lallai yarinyar  nan  ma  ta sameshi  yadda ya  kamata  ,shi take maidawa  magana ?ai duk  laifinka  ne da baka gyara mata zama ba  ka  tsaya  kana  tattalinta,  yarinyar da yaka mata ka  wulakantata   ta hanyar keta  mata  haddi  tunda abinda yasa ka d'aukota kenan "  zuciyarsa ta fad'a masa
haka  numfashi  ya  fesar yana jin  zafin  acikin zuciyarsa , sam bai ji  d'acin  Kalmar  daya   fad'a mata  ba, dan  haka  yayi tunani sake musguna  mata   jikinsa a sanyaye ya Kai  bakinsa   daidai saitin  kunnenta yana sake watsa mata kallon  bazan    tayi  saurin   gocewa   tana  furzar   da  numfashi  tare da  hura  hanci  sannan taki waigowa  ta Kalli Inda yake bare taga kallon banzar da yake mata zafin da zuciyar ke yi yasa wasu hawaye masu zafi da ciwon  sake zubo mata ita daya kamata ya farantawa adalilin zata tafi ta  barshi  tafiyar da ba lallai su Kara haduwa ba kamar yadda  ya  sha fad'a mata  ."

ya matso  kusa  daita Sosai yana busa mata iskar  bakinsa , bakinciki da takaici yasa   tayi  saurin  janye jikinta  daga nashi  tana  kallon  gefen  titi ,shiru  yayi  yana kallon  gefen  fuskarta  numfashi   ma  da kyar take   fesarwa  bai san yadda akayi ba  ya sake matsowa  sosai  ya d'aura kanshi a saman  kafad'arta  ,shiru  tayi taki   motsi   sannan taki waigowa, jin  shiru  taki  motsawa  ya tabbatar masa da lallai  fushi  tayi dashi  tsintar Kansa  yayi da rashin  jin   dadin yanayinta can Kuma ya furzar da iska had'e da jan dogon tsaki    "me  yasa   zan ji babu dadi  araina  dan  tayi fushi dani  ?ya  jefawa kwakwaluwarsa  tambayar  " Kiran  daya  shigo  wayarsa ya  katse masa zance zucin da yake bare ya samu amsa daga  wankakkiyar zuciyarsa , ya lalu'bo wayarsa daga cikin aljihun  wandonsa   ya mannata a kunnensa  batare  daya duba me Kiran ba.
jin sautin muryar  amminsa ce yasa shi  barin   jikinta  da hanzarinsa dan yana expecting  jin dadd'adan labari  daga  bakinta dan  jiya   da  sukayi  waya yake  sheida  mata ya kamata ace  yaron dake son  shefiqa  ya  turo iyayensa  ayi maganar aure  ,a lokacin ammi  ta  tabbatar  masa da zatayiwa shafiqa  din  magana   ,  ai kuwa abinda  yake expecting ji  shi  ta fara fad'a  masa  yasa wayar a hands free ya d'aura wayar a  kafad'arsa  ya  jingina jikinsa sosai a kujera."

  "yaron   nan gali  wai  zai  turo  iyayensa  ranar   lahadi  tare da saka rana   gbdy "  murmushi   jaguwa  ya saki  na  farinciki   yana cewa  " Allah ya  nuna mana  ranar  lafiya so nake na  aurar dasu gbdy kafin nawa auren . "a'a ban yarda da wannan  tsarin  ba ,idan ma  son samu ne a had'a  auren  da naka ba qaramin  farinciki zanyi ba "shinkenan ammina yadda  kikace  haka za'a yi  bani da za'bin da ya wuce naki  zanyi   k'okari naga anyi auren da nawa sai dai  ki qara  addua akan wanda kike  min     Allah  yasa  na samu me sona tsakani da  Allah  "zaka  samu da iKon allah dan  baka  da  makusar da wata diya mace   zata  kika  ni dai  fatana kayi kokari  ka  cika min alkawarina  Ina  son kyakkyawar  suruka me nagarta   idan   son samu ne   wacce  ta  fika kyau". wani  narkakken  murmushi    ya   saki  kamar  yana gabanta  kana yace "kin samu kin gama  ammina  dan sai na  kawo   miki  irin matan  hurul'ain  dan irinta  kike  bukata ta zama  surukarki   ya k'arasa  maganar yana dariya    tare da  matsowa  ya kamo  yatsun  hannun  tanweer  ya rike gam  cikin  nashi yana massaging a hankali  ,   itama ammi dariya take sosai tana sake tabbatar masa da hakan  take  so  , ita Kuwa tanweer  gbdy  ranta  a dagule  yake  sbd haushin   abinda yayi mata da Kuma haushin maganarsa da mahaifiyarsa  dan  duk  tana ji abinda mahaifiyarsa ke fada masa   sannan tana   Jin amsar da yake  Bata    cike da  fushi ta  soma k'okarin zare  hannunta  cikin  nashi  tana sauke wahalalle numfashi  sai dai ta kasa  kwatar hannunta dan haka tayita jan  tsaki babu kaukautawa ganin  hk  yasa yayi  sallama  da ammi  tun  kafin  ta  tunhumeshi  ,ya  katse Kiran yana  cewa   "ki  daina wahalar da  kanki  bake  ba ko namiji dan'uwana na rike bai Isa  ya kwace ba bare ke    " ko   kina tunani ni din irin  lusaran  samarinkanki ne da zaki gwada  karfi  dani   ..?"ya karasa  tmyr  yana furzar da  iska mai zafi daga bakinsa."

danne abinda taji ya tsaya mata arai tayi  tana zance zuci" shi take  mutuwar so amman shi burinsa kullum ya cusguna mata tare da nuna mata ita din ba kowa bace ,  tunda suka  had'u  yake kyautata mata  ta hanyar  bata  kulawa  sai dai a fahimtarta bashi da burin daya wuce   ya 'bata  mata  rai  ta hanyar fada  mata  baqaqen  maganganu . tasan  ba lallai ta zamo test dinsa ba amman at least itama tana da daidai nata  kyau sama  sama ta dinga fidda numfashi  tana danne damuwarta  "dan  Allah  direba ka taka  motar nan da sauri  Ina son d'aura kwayar idanuna  akan  iyayena wad'anda   suka zamo min bango abun ma jingina  kuma  farincikina   nasan suma  nice farincikinsu rashina baqaramin  babban  tashin hankali bane  garesu  suna can suna mararina"
Chapter 24 · 0% Book details