← Book details Kuskuren Baya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 138 OF 160

Sashe 138

Kuskuren Baya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

“Shikenan naji amman sai dare zakazo ka daukeni ?ya dage mata gira ,muje kayi wanka kaci abinci ,
Wanka dai amman abincin nan no space kamar jiya suna tsaka da hirar soyayyarsu aka kira sallah ya fita zuwa masallaci a daren ma kwanan farinciki sukayi rungume da juna sabanin tanwer da adnan .
washegari da safe ta tashi ta hada musu break suka ci suka fice ya bude mata gaban mota ta shiga ta zauna ta rufe ya zagaya ya shiga ya kunna motar suka bar gida bini bini zai jiyo ya kalleta sai murna take zata gida ,ya lalubo tafin hannunta cikin nashi yana murzawa yana janta da hira da tsokana har suka karaso unguwarsu yayi parking adaidai kofar get din gidansu zata bude bangarenta yayi saurin cewa “no my princess bari karki wahalar da kanki ya fita da sauri ya bude mata a hankali ta fito ya kulle motar suka jera suka shiga gidan ,”

A haraban gidan anas yaja ya tsaya ta shiga falon bakinta dauke da sallama ammi na zaune bisa kafet ita da haseera suna breakfast ammi ta dago ta kalleta ta kuma kalli bayanta “ina bin malik din yake ?ta karaso ta tsugunna a gabanta tana gaisheta ammi bata damu da ansa gaisuwar ba ta sake tmbyr anas “yana waje ammi ta bata rai “dan sakarci irin naki me yasa zaki bar min yaro a waje maza ki tashi kice ya shigo cike da mamakin irin wannan qaunar da ammi take masa ta mike tana riko hannun haseera “aunty hasera ya kwana biyu ?Lafiya lau auta duk kin wani canza kinyi kyau Kmr wata india tayi murmushi ta nufi kofar fita ta tsaya a gabansa “muje ko dan kasa mamanka tana min fada tai mgn tana zumboro masa baki yayi murmushi ta juya yana biye daita .”

Cike da ladabi da biyaya ya shigo bakinsa dauke da sallama ammi ta amsa tana fadada fuskarta da murmushi dan shima yayi kyau kamar yadda diyarta tayi hally ta dauko dadduma ta shimfida masa ya zauna kusa da ammi “anas ya aiki da hakuri da auta ? Alhamdullahi ammi babu abinda zance sai Godiya hasera na kallonsa amman bata ce masa uffan ba abun ya dan tsotsa ran hally shi dake mai saukin kai ne yace “hasera ina yini fuska a hade ta amsa da “Lfy! atakaice dan gani take har dashi acikin masu zuga adnan kar ya aureta hasera ta maida hankalinta gurin hally “hally uwar kyau wannan ai kinfi karfin akiraki mai kyau sai dai uwar kyau hally tayi mata banza “kinga kuwa yadda kika kara kyau kika murje?da kyar tace “na gode mumy kuwa abincin gabanta ta turawa Ana’s tana bashi umarnin yaci babu mutsu ya fara ci hally tasan ya koshi amman bazai iya mutsu daita ba ta tsura musu ido kawai tana jin dadin yadda ammi take qaunarsa byn ya danci kadan suka koma kan kujera suna hira ita ammi da anas da ita kanta hasera sunyi hira sosai cikin haka anas yayi wa ammi sallama ya ajiye mata kudi bandir din yan dubu day day na 50k “ga wannan babu yawa ni zan wuce ,haba anas har da wata hidima?babu wani hidima ammi ki samin albarka shine abinda nafi bukata daga gareki ,allah yayiwa rayuwarku albarka gbdy ya daukakaku a idanun duniya ya rufa muku asiri duniya da lahira Ameen ammi na gode sai anjima ya sa kai zai fita hally ta biyo bayansa domin masa rakiya ,”

A haraban gidan haseera ta samesu kamar zasu shige jikin juna ganinta yasa suka dan bawa junansu tazara ta karaso tana cewa hally ki dan mana exuse bata damu ba sai ma shigewa ciki da tayi haseera ta gyara tsayuwa tana tsura masa ido “ada tunanina kana cikin wadan da suke zuga adnan akan kin aurena amman a yanzu na fahimci Kai mutumin kirki ne sannan nasan kasan matsayin da nake dashi azuciyar abokinka ko zan iya sani wani abu karka min karya ka fad’a min gsky sbd allah ?” yayi shiru yana kallonta d’an ta dauresa tunda ta kira allah ,
“Adnan yana da burin aurena ko kuwa wata can yake da burin aura?Kamar yace mata eh sai kuma yayi shiru” idan ma bashi da burin aurena gara ya fada nasan matsayina ba nayita jiran gawon shanu ba “kibi komai a hankali haseera Kinsan shi alamarin na aure nufi ne na allah da zarar lokaci yayi kuma kece matarsa zaa yi idan bake bace haka zaki hakura“.

“Bama zai zamo bani bace matarsa dan da yaje ya kwaso wata gara ace nice zan shiga gidansa kai ni aurensa ko ba alkhairi bane ina rikon allah ya mallaka min shi yayi shiru yana kallonta yana hadiye wani dunkukallen abu daya tsaaya masa a makoshi
“jikina yana bani zuciyarsa naga wata amman nasan kowacece bazata fini da komai ba sannan bazata zamo min natsala ba ,ga sako ka fada masa idan ma zai dawo da hankalinsa gareni yayi idan bazai dawo ba sai dai ya mutu bai yi aure ba amman ko zanyi yawo tsirara sai na zama mata agidansa domin shi din nawa ni kadai , idan baka sani ba na fada maka wani abu mahaifina ne ya taimaka masa har ya kawo matsayin da yake a yanzu amman dake shi dan adam masu manta alkhairi , yanzu kai a ganinka ya dace sakayyar taimako da mahaifina yayi masa ya fada akan wata bani ba …?

Sai allah ya kaimu byn sallah ayi sallah lafiya karku manta da naman sallahna lol love you guy’s

Mmn sudais

💗💗💗💗💗💗
KUSKUREN BAYA
💖💖💖💖
💗💗💗💗💗💗

PAID BOOK

WRITING BY
AYSHA .A BAGUDO

WATTPAD @HAUESH

bismillahirrahmanirrahim

Wannan littafin na kudi ne mai bukata karanta shi ya tura 500 ta wannan account number din 1438775094 Aishat Abdullahi Access bank ,Idan an tura sai a turawa wannan number+234 703 534 8686alert domin tabbatar da an tura ko wadan nan number's din 09136918331 or 08059623096 Idan Kuma vtu za'ayi sai a tura ta wannan number 09136918331 domin sauraran littafaina a tuntubi Channel dina ta Hausa bakwai.

🅿️39

......Tunda ta  fara magana yake kallon bakinta yana jin wani irin zallar'bacin rai mai tsanani  ,dan idan akwai abinda ya tsana  a rayuwarsa bai wuce yaga ana shiga rayuwar jaguwa ba ko ai bantashi , bai sake ce mata komai  ba har  sanda ta  gama  magnrta , sai dai kallo daya zaka masa ka fahimci fuskarsa ta canza daga farinciki da yake ciki zuwa bakinciki ,tayi shiru ta zuba masa idanunta tana kallon fuskarsa da sam babu annuri kwance akai
a hankali ya dauke kansa daga kallonta .”
cigaba da kallonsa tayi tana jiran taji mai zai ce mata ,ganin yayi shiru yaki cewa komai yasa
ta gyara tsayuwarta tace "da fatan zaka fada masa sakona?."bai kalleta ba ya furta "a'a bazan fada masa wannan sakon ba amman idan ke kinji zaki iya to Ki samesa da kanki ki fad'a masa watakilla ma zai fi fahimtarki akaina ". yana gama fadar haka bai tsaya jiran me zata sake cewa ba ya juya a natse  ya nufi get din  gidan, bayansa tabi da kallo  yana taku a hankali shima kamar adnan din yake ta  fada a kasan ranta ,komai nashi mai kyau da tsari to ya ma za’ayi abokansa ba zasu kasance kamarsa ba ?."Jiki a sanyaye ta juya ta nufi cikin gidan tana nazarin yanayin daya shiga a lokacin da take masa magana akan adnan "kamar bai ji dadin maganarta ba ?tayiwa kanta tambayar  ,tabe labbabta tayi  tana cewa "kar allah yasa kaji babu dadi  aranka tunda zaginsa nayi da zaka wani ‘bata rai taja tsaki tare da shigewa ciki ."

Ahankali anas ya bud'e motarsa ya shiga ya zauna da kamar ya kira hally ta fito suyi sallama  sai ya fasa ya kira layin ta yana kokarin yiwa motar key  har ya bar unguwar suna waya tana zuba masa shagwaba lokaci daya yaji ta yaye masa dukkanin damuwarsa ,bai tsaya akoina ba sai a kofar gidan jaguwa yayi hon mai gadi ya taso ya bude karamin hujin get, ganin shine ya soma kokarin bude masa babban get ya sanyo hancin motarsa cikin haraban gidan mai gadi na daga masa hannu ,ya karasa inda yake parking din motarsa yayi parking ya kashe motar ya fito yana gyara zaman rigarsa adaidai lokacin da mai gadi ya gama rufe get ya karaso gurinsa cike da girmamawa har zai rusuna masa Ana's yayi saurin dakatar dashi yana cewa "haba baba sau nawa zance maka ka daina duka min ? ai ko baka haifeni ba kayi kani kusan na biyar dani please ka daina bana so ,ya fda yana mika masa hannusa ,gaishesa mai gadi yayi yana murmushin jin dadi dan ba yau bane karo na farko da anas din ke hanashi rusuna masa sabanin sauran ya amsa masa gaisuwar a mutunce kamar koda yaushe sannan ya nufi ciki gida yana shafa sumar kanshi ,binsa mai gadi yayi da kallo gabadaya rayuwarsa ta sake sauyawa ,kamala da natsuwa sun samu kyakkyawan zama ajikinsa har wata yar kiba yayi ta kwanciyar hankali ."

Zaune ya iske jaguwa zaune akan kujera a parlour ya daura kafafunsa saman table jikinsa sanye da jajayen kaya wando da riga yana operating laptop , cup din coffee na daga gefen laptop dinsa ,yayinda jabir ,
kamil da jubi suke zaune suna kallon wani film din  soyayya mai suna kuchi kuchi hotahe, sai faman murmushi suke ,sallamrsa ce ta dawo da hankalinsu bakin kofar shigowa   har shi jaguwa sai daya dago kanshi a natse daga kallon laptop da yake ya maida idanunshi kan anas dake tsaye yana dubansu alokacin murmushin farinciki bayyane akan fuskarsa  yace "da dai kunje kunyi aure da wannan kallon da kukeyi ,a aure ne kawai zakuji gardin soyayyar gaskiya  ba irin wannan na film ba  wanda nishadi kawai zai dinga saka ku .” ya karasa maganarsa yana mikawa jubi dake kusa dashi hannu domin su gaisa  still fuskarsa dauke da murmushin tsokana ."
Chapter 138 · 0% Book details