← Book details Kuskuren Baya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 50 OF 160

Sashe 50

Kuskuren Baya Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

shigowarsa ke da wuya  d'akin  ma ya kaure da warin wiwi  dana turarensa wani  irin  haushi ya kamata idan akwai abinda ta tsana shine warin wiwi ko ta'ba , kallo d'aya tayi masa ta d'auke kanta  ta mayar wani gefe  tana wasa da yatsun hannunta .
Ya  ajiye  ledar  hannunsa yana cewa  "ga  abinci nan kice ki sha  magani  kin ma kuwa yi sallah isha'i  ?  "ban yi ba Kuma bazan yi ba, wallahi idan ka sake min magana akan sallah sai na kashe kaina    "Allah  ya bada sa'ar tafiya  dadin abun  idan kin kashe kanki  bazaki rataya a wuyan Adnan ba kice zaki mutu kafura ".
"Kai ne dai  kafuri  Kuma Kaine  zaka mutu a wannan  rayuwar da kake.  "are you out of your sense ? ya fad'a a fusace " ni  kike  fad'awa haka  ?" shiru tayi tana dubansa kafin idanunta ya kawo ruwa "amman  Kai me yasa kullum sai kayi min magana akan sallah kamar wata kafura ? "Alama na gani na bakin son yinta " .
shiru ta sake yi kamar me nazari numfashi ya fesar ya juya zai fita 
yaji sautin  muryarta a raunane  "kazo  ka d'auke  banzar abincinka dan  ba zanci  ba"  kad'a kafad'unsa  yayi yace "daidai kenan Ina son haka  ,Kinga  rashin cin abincinki ko rashin walwarki bazata dameni ba saboda bana sonki bakya cikin rayuwata  kisan Allah ko nemanki nayi na rasa bazan damu ba dan bayan mahaifiyata da kannena ban san ciwo kowa ba, bayan darajan kannena dana sani ban San darajan kowace mace ba Kinga Kenan  Kema kina cikin matan da bana ganin darajansu  ,yana gama fad'ar haka ya fice daga daki ."Kuka ta rushe dashi tana Kiran tashi uku sai da tayi me isarta sannan  ta janyo ledar daya ajiye mata  dan yunwa take ji sosai , taci kad'an ta bar sauran ta shiga bayi tayi wanka ta fito ta sha magani tayi sallah ta  kwanta lamo akan bed  tana tunanin  iyayenta, "Allah sarki dadynta  muryarsa ta nuna yana cikin damuwa " dad dinta da bai iya cikakken awa d'aya ba tare daita ba ,ko zuwanta  turai karatu baya jimawa batare daya ganta ba, kullum Kuma cikin video call  suke  ,ko ya dad dinta zai ji idan ya ga ta dawo garesa ? tasan rungumeta  zai yi a karshe ya  d'auketa sama   yayita juyi daita yana cewa "my tan ta dawo  I really  miss  you my tanweer  wasu hawaye masu zafi ne suka biyo gefe da gefen idanunta.
"Ko waye wanda ya tura musu yan fashi ?waye wannan ? ta tambayi kanta "waye cikin family dinmu ?dangin mumcy dina ne ko dangin dad dina  ne ?"dangin dad dina basa zaune a lagos tunda shi din haifafen garin Kaduna ne, mumcy dina Kuma yar d'aura ce ",ai daga koina mugu zai iya idar da nufinsa ya farmaki rayuwarka,Allah sarki mugu bashi da kama  suna  tare dashi Amman  basu  san cewar shi din makiyinsu bane  "shiru tayi  tana  sake zurfafa tunaninta ,babu abinda ya shiga
yawo acikin kwakwaluwarta kamar hirarsu jaguwa a wacan ranar data san dan fashi ne "tabbas taji sun ambaci sunan Alhj  tahir a hirarsu .
a lokacin ta zurfafa  tunanin domin sanin  me sunan a karshe  zuciyarta ta tsayu akan mahaifin Ib shi kad'ai tasani me wannan sunan, tashi tayi zaune ta zauna "tabbas shine me sunan Ibrahim Tahir ta furta a fili  "Kai ba dai shi ba bazai ta'ba aikatawa mahaifinta haka ba sai dai idan suna ne ya zamo daya , to Kuma ai maganar  Adnan ta nuna Wanda ya turasu na tare dasu to meye gaskiyar lamari ? take zuciyarta ta shiga wasi wasi wata zuciyar tace shine wata zuciyarta ta karyata hakan .
wasu hawaye ne masu zafi suka
zubo akan kuncinta " tana bukatar ganin iyayenta tana son ganin dad dinta da mum  dinta tana bukatar Jin dumin jikinsu kamar yadda ta saba dan  girmanta bai hanata kwanciya ajikinsu  ba she really  miss  them .".
Daren  ranar  kasa runtsawa  tayi  jikinta yayi zafi rau  kamar garwashin wuta sai faman juyi kawai take akan mamaken bed din da take kwance tana tunanin mafuta kwakwaluwarta ta sake lula kogin tunani mai zurfi akan yadda zata bar gidan ta kowani hali  dan dole tasan yadda zatayi ta bar gidan tun bai canza ra'ayinsa akanta ba  ya fara kusantarta.
 da kyar bacci  barawo ya  saceta   washegari  da safe bai shigo yaga halin da take ciki ba yayita lamuran gabansa ita Kuma hakan ya  bata damar tsara yadda zata bar gidan kota halin balai,  ta fito sanye da doguwar riga baka har kasa tayi rolling kanta da mayafin  rigar   Kai tsaye  ta wucesu  a falo  zaune tare da abokansa har ta fito haraban gidan
ya fito ya biyota  yana  cewa " ke  Ina zaki kika wani wuce mutane dan iskanci  ?

"Bansani ba Kuma karka sake tambayata Inda zani dan ni ba diyarka bace sannan ba abar ikonka bace da zaka wani tsareni da banzar ta....." shiiiii  wuce  ki koma ciki" "bazan koma ba gidan nan  zan bari Kuma a yanzu ta fad'a tana cigaba da tafiya taku uku yayi ya riko tsintsiyar hannunta "muje babu Inda zaki sai wadin zamanki a gidan nan ya Kai .
ta juyo a fusace ta sanya kwayar idanunta cikin nashi cike da balai tace "Kai waye da zaka hanani tafiya?.
"ni Adnan amad ".ya bata amsa yana kallon cikin idanunta fuskarsa a had'e babu alamun wasa .
"wallahi baka  Isa ba  who the hell are you?  duk da me gadi gidan nan abun ikonka  ne zanyi duk yadda zanyi na bar gidan nan  Kuma  a yau .
jaguwa bai saurarata ba  ya jingina jikinsa  ajikin  motarsa ya tsura mata Ido yaga iya gudun ruwanta . tanweer ta Isa  Inda taga makulan motoci  rataye ajikin bangon rufar motaci  ta d'auki ta camery ta rike gam   zata bude  moto  tuni yaransa suka tareta bisa umarnin jaguwa da yayi musu umarni da Ido  sai dai hannunsu bai ka ga jikinta ba  suka hanata ta'ba kowacce mota a daidai lokacin su anas suka fito suka tsaya suna dubanta .

xagi ba kalar da tanweer  bata musu  ba da hausa da turanci Amman Babu Wanda ya kulata haushi ya isheta ta bar gurin mota ta nufi bakin get nan ma babu hali dan me gadi yaki bude mata get duk Inda tasan zata bi ta fita daga gidan babu hali ta shiga maseefa tana cewa " sai na bar gidan Kuma Babu wanda ya Isa ya hanani fita idan na bar gidan sai na sa ankamaku anyi muku hukunci me radadi,wallahi  da Kun San Koni wacece a garin nan da baku tsaya bin umarnin wannan ba Kun  hanani fita ba, ta juya ta Kalli Inda jaguwa yake tsaye jikin motarsa Idanunsa na kanta yana cigaba da kallon bakin tsiwa  "zan nuna muku ko ni wace acikin garin nan tare da juya masa baya.
"Kashi Amman na tausaya miki wannna shi ake kira da power less" juyowa tayi cikin fushi ta Kalli Inda yake idanunta ya sauka akanshi.
yana nan  tsaye sai dai zuwa wannan lokacin   ya harde  hannuwansa a qirji  yana mata murmushin mugunta fuuuu ta nufosa cikin tsananin  fushi da zuciya   tace "zan nuna maka wannnan power din kasa Ido ka gani"tayi  mgnr tana nunashi da yatsa  "me  zaki  iyayi ?ba abinda zaki iya yi min ,ki daina takama da wannan dan matsayin da mahaifinki yake dashi dan baki da wani power da zaki iya min koma" .

ba bata lokaci ta cukumi wuyansa "zaka ga abinda zanyi ".
Yaransa suka bishi da kallo haka ma abokansa me gadi kam saurin kawar idanunshi yayi kamar bai ga abinda ke faruwa ba  ran jaguwa yayi mugun 'baci sai dai bai ce mata Komai ba har sanda ta hau fad'a da maseefa  da zaginsa da fada masa bakaken maganganun ,sai da tayi mai isarta sannan ta  sakar masa wuya ta dukurshe ta zube kasa ta  runtse idanunta  wasu hawaye masu zafi suka zubo mata .
shi kuwa ya matsa gefenta ya tsura mata Ido ransa na quna kafin daga baya ya canza kallon zuwa natsana yayi taku biyu zuwa Inda take durkushe  dafe da goshinta "sorry tanweer bazaki iya komai ba sai da kiyita ihu kina kuka kina zagina
just like a baby ,the great tanweer, kyakkyawar matashiya mai ji da
kudi  yanzu ta zamo abar tausayi  agidan nan , gidan nan fa  ba yadda kike tunani bane dan ba  haka kawai yake ba ko mahaifinki da karfin masu karfin garin nan zasu zo  basu Isa su shigo ba, Ina tabbatar miki muddin kika bar gidan to nine na fitar dake amman rashin kunyarki da ihunki bazasu fitar dake ba cikin sauki ba  ."
Chapter 50 · 0% Book details