← Book details Kuskuren Baya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 95 OF 160

Sashe 95

Kuskuren Baya Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Wannan littafin na kudi ne mai bukata karanta shi ya tura 500 ta wannan account number din 1438775094 Aishat Abdullahi Access bank ,Idan an tura sai a turawa wannan number+234 703 534 8686alert domin tabbatar da an tura ko wadan nan number's din 09136918331 or 08059623096 Idan Kuma vtu za'ayi sai a tura ta wannan number 09136918331 domin sauraran littafaina a tuntubi Channel dina ta Hausa bakwai.

🅿️30

……….Jaguwa yaja tsaki wannan na daya daga cikin abinda yasa ya tsani zahra da soyayyar da take masa ,a ganinsa sam wannan rayuwar bata dace da diyar bahaushe ba ‘d’abiar arna ce ko yarikan da suka sha bam bam data hausa fulani, amman yanzu an wayi gari wasu daga cikin yaran hausa sun maida zina ado sai su baro gidajen iyayensu dan kawai ayita iskanci dasu ana biyansu kudi,basu lagos basu abuja most especially abuja ma da suka maidata tamkar kasar yuganda wad’an da zina ba’a bakin komai take agurinsu ba saboda rashin sanin ciwon kai.
Ahankali ya janye kwayar idanunshi akanta ya sauke akan ajirebi wanda ya samu nasarar ciro bindigarsa, zaro idanu yayi waje tare da kiran sunan anas da karfi .
cikin tsananin tashin hankali da tsinkewar zuciya bai bari ajirebi ya kai ga harbin anas ba ya sakar masa bulet a hannunsa.
ajirebi ya saki wata razananniyar qara da tasa hotel din ya amsa kuwan ihunsa wanda hakan ya janyo hankalin abokan aikin jaguwa data ma’aikatan hotel din har ma da jama’ar dake cikin sauran dakuna.
nan hankula mutane bila’adadin
ya tashi ,su jubi suka firfito daga cikin mota suna mazura had’e da gyara bindigarsu ,take wani daga cikin ma’aikatan hotel din ya nufi dan karamin d’aki wanda aka tanada domin manager ya sanar masa da abinda ke faruwa “sir da alamun barayi sun shigo hotel din nan ” .
“haka ne joy bama alamu bane sun shigo “ cikin sauri ya fad’a haka sannan ya juya inda wayarsa take ya d’auka ya fara neman number jami’an tsaro.”

Jaguwa ya tako har inda anas yake cikin tsananin tashin hankali , shima anas din shi yake kallo zuciyarsa cike da fargaba da tashin hankali “da yanzu shine kwance acikin jini koma yace ya mutu , kallon juna suke yi cikin yanayi na tsananin tausayawa ,
shima kamil cikin tashin hankali da kidima ya matso ya dafa jaguwa yana cewa “ya kamata muyi abinda zamuyi mu fece mu bar gurin nan“.
jaguwa ya gyada masa kai kawai batare daya ce masa komai ba illa rungume anas da yayi ajikinsa yana jin wani irin tausayinsa mai had’e da soyayya “kaga yadda gangancinka yaso na rasaka ko?” me yasa baka maida hankali akan aiki ne?“ ka daina min irin wannan gangancin please dan zuciyata bazata iya daukar damuwar rashinka ba ,ruhina zai shiga matsanancin damuwa idan ta rasaka’bana son na rasaka anas…”ya karasa maganar cikin raunanniyar murya kamar zaiyi kuka shima anas rungumeshi yayi tsam ajikinsa yana shafa bayansa yana sauke numfashi “is okay inshaallahu bazan mutu ba sai na bar maka magaji da zai dinga debe maka kewata “allah yasa amman nafi bukatarka a raye akan magajinka banason ka tafi ka barni wallahi idan ka tafi duniya zata min zafi dan allah ka dinga kula da kyau tuni ruwan hawaye suka cika idanun anas yana me sake jin qaunar jaguwa aransa .
wani irin naunayen ajiyar zuciya kamil ya sauke bai yi mamakin wannan qaunar da sukewa juna domin ba wannan bane karo na farko da jaguwa yake daga hankalinsa akan anas ,akoda yaushe yana nuna qaunarsa koda kuwa agaban waye haka shima anas din ,ya amince da qaunar da suke wa juna .
“Suna cikin wannan halin kiran jubi ya shigo wayar jaguwa ya zare anas ajikinsa ya ciro wayar ya danna koren maddanin sannan ya manna wayar a kunnesa ,jubi najin ya d’auka ya sauke naunayen ajiyar zuciya da numfashi atare sannan yace “ya akwai matsala ne “?munji qarar harbi ?”
Muryar jaguwa can kasa yace “allah ne ya taimakeni yau da na rasa anas amman yanzu komai normal yanzu zamu fito ya karasa maganar yana disconnecting din kiran.
ya juyo ya maida hankalinsa sosai ga ajirebi dake kwance rike da hannunsa dake tsiyayar jini a tsanake ya motsa lips dinsa tamkar baya son yin magana “ka godewa allah kana da sauran numfashi a duniya da harsashina ya samu iya hannunka ,da kayi gangancin harbin anas da wallahi yanzu ba wannan maganar ake yi ba, dan ba a hannu zan harbeka ba anan zan harbeka kasheka lahira yana magana yana tsaita daidai zuciyarsa da bakin bindigar pistol’take ajirebi ya had’iye numfashinsa ganin kallon tsanar da jaguwa ke masa wanda yake nuni da zai iya rabashi da rayuwarsa”.

Jaguwa ya d’auke bakin bindigar a qirjin ajirebi ya juyo ya kalli anas dake tsaye jiki a sanyaye “janyosa muje ,kai kuma kamil ka taho da wayarsa, da akwatin can ”okay “ya fad’a sannan ya fara aikin da’aka saka shi .
Wani dogon ajiyar zuciyar anas ya sauke cikin fargaba yace “tashi muje kamar jira ajirebi yake anas ya bashi umarnin tashi yayi sauri ya tashi tsaye yana zazzare idanuwa ,Jaguwa ne ya fara yin gaba sannan anas da ajirebi suka biyo bayansa kamil ne ya fito a Karshe batare daya tsaya rufo kofar ba.
Cike da izza da jin kai jaguwa ya karaso reception yana gama karasowa ya tsaya ya saita bindiga a kasa yayi harbi take duk wanda ke cikin hotel din suka sake yin kasa da kansu dan dama a matukar tsorace suke tun harbin farko da yayi ,anas yayi gaba rike da kwalar rigar ajireba yayinda kamil ya tsaya ya fuskanci kofar baya da zata kai mutun swimming pool side da bindiga koda wani zai kawo musu hari.”

Fuskarsa jaguwa babu tsoro ko fargaba ya tsaya yana kallon mutane kwance sunkuye da kasa suna kyarma tamkar masu jin sanyi ,taku yayi cike da qasaita ya isa gaban kujera mai zaman mutun daya kana ya juyo ya zauna kan kujeraar hakan yasa ya fuskanci office din manager ya saita kofar yayi harbi yana furta sunan manager da karfi,kamar walkiya manager ya bayyana agabanaa dan daman baya cikin offi din ya rigada ya fito , wani mugun kallo jaguwa yake binsa dashi har ya tsugunna a gabansa ya shiga juyawa jaguwa kai alamun ya tausaya masa “ka kira police ko “?manager yayi shiru jikinsa na wani irin rawa tamkar mazari, a matukar fusace ya buga masa wata hadaddiyar tsawa yana cewa “ka bud’e baki ka bani amsa”.
A kidime yace”no sir ban kirasu ba taya ma zan kirasu ai ban isa ba ?“.
“Ka sani ko dama ka kirasu kayi aikin banza ne , yadda kasan idan gobara ta kama kafin masu kashe wutar suzo gobarar taci ta cinye har wasu ma sun jigata haka ma jami’an tsaro suke a wannan kasar tamu , bazasu zo ba sai byn mun gama abinda ya kawomu mun wuce ka gansu da jiniyar karya domin su din karnukan farauta ne kuna takama dasu ne kawai abanza amman babu abinda zasu iya muku “. ya karasa maganar yana jan tsaki .

Shiru reception din yayi baka jin motsin kowa sai na numfashin mutane da takun takalmin kamil dake kai kawo kowannensu dake duke sun kasa kwakkwaran motsi sai wani irin hadiyar zuciya suke sauke wa , jin shiru har tsawon minti gomashabiyar bai sake cewa komai ba yasa manager ya d’ago a hankali yana ganinsa yay saurin dauke idanunshi akan shi dan bazai juri kallonsa ba ,a halin da yake ciki yanzu ji yake kamar numfashinsa zai bar gangar jikinsa , aran shi yake mamakinsa“ wannan wani irin dan fashi ne”? gbdy yanayisa babu tsoro ko fargaba,gsky yana da dakakiyar zuciya ko shi da ba d’an fashi bane a matukar tsorace yake bare shi mai laifi ‘a lissafinsa yanzu police sun isa su karaso dan babu wani tazara atskaninsu amman har yanzu shiru babu su babu alamunsu ,”tabbas maganarsa ta tabbata bazasu zo ba sai byn sun wuce zasu zo da jiniyar banza idan ma kashesu zaa yi sai dai yayi allah ya kyautawa kasar nan .”

Sai da jaguwa ya gama shan kamshinsa sannan ya mike ya nufi kofar glss kamil ya marasa baya ahankali manager ya dan juyo sai dai bai daga idanunshi ba yana kallon tafiyar jaguwa cike da kasaita sam bazace dan fashi bane daga shi har shigarsa abun burgewa kai shi bai ma yarda dan fashi bane zuciyarsa na fada masa ba dan fashi ba mai kyau dashi ,
Skin dinsa sai sheki yake ga wani kamshi na musamma dake tashi ajikinsa dan har yanzu daya bar gurin kamshin turarensa na nan.”
Jaguwa na fita wani harbin yayi
sai dai wannan karon a sama yayi,manager yay saurin runtse idanunshi tare da zubewa kasa.
Chapter 95 · 0% Book details