← Book details Kuskuren Baya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 139 OF 160

Sashe 139

Kuskuren Baya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

     jubi ya hade hannuwansu guri daya  ya tsarke sosai yana cewa "kai ma ba wayonka ne ya baka auren  ba ,  taimaka maka akayi aka baka ko kuma nace shishigi da nemana gindi zama da kutse acikin arayuwar wasu yasa akabaka aure if not da haka zaka mutu babu aure dan babu wacce zata aureka da irin rayuwar da kake ,ko ka manta kai din dan giya ne ? sannan kuma mane min mata ?."
"Idan ka manta na tuna maka wane ne kai ,mu ka barmu a yadda muke din nan yafiye mana  dadi da wata rayuwar aure can wanda babu komai acikinsa sai takura ,wani dadi kake ji a aure da mu bama ji ?." ya tambayesa yana kafesa da jajayen idanunshi
“kwana kake da mace muma idan muna bukatar kwana da mace zamuyi ko ba haka ?”saurin maida idanu jaguwa yayi akan jubi wanda ke maganarsa hankali kwance yana duban sauran abokansu babu wata shakka ko fargaba daya nuna a fuskarsa .”
jubi ya cigaba da magana a zafafe "shasha yana da kyau ka dinga iya bakinka akan komai dan zakewarka tana dada yawa idan ba haka ba zaka tsinci kanka cikin nadama .”ya saki hannunsa ya fusace ya maida idanunshi kan kallon da yake wanda hakan yasa sauran basu samu damar furta abinda ke cikin  ransu ba dan duk abinda suke son fad'a jubi ya rigada ya fad'a masa hakan kuma ya wanke zuciyarsu."

  hakan nan maganar jubi ta caki zuciyar jaguwa sosai  har ya kasa dauke idanusnhi akansa bare ya cigaba da aikin da yake sai daya maimata maganar jubi kusan so uku acikin ransa kafin ya dauke idanusnhi ya kalli anas da yake tsaye kikam yana kallonsu jiki a sanyaye ,a kallon da yake masa ya fahimci jikinsa da kafafunsa rawa suke ,shi kansa cikin tsananin kaduwa da bugawar zuciya yake cigaba da kallonsa yayi sam bai ji dadin kalaman jubi garesa ba haka zalika yasan anas din ma bai ji dadi ba dan gabadaya yanayinsa ya sauya amman yasan babu matakin da zai dauka ,nemo jarumta Ana's yayi ya sanyawa jikinsa.”

"Friend !".

Ana's ya  kira jaguwa a natse yana sakar masa murmushin dole dan da zaa bude zuciyarsa bakinkirin zaa gani tsabar bacin rai ,jaguwa bai
amsa ba illa kallonsa da ya cigaba da yi ,shi kuma ya samu guri ya zauna a kusa dashi  yana basarwa tamkar maganar jubi bata ta’bashi ba a kallon da yakewa jaguwa ya Karanci damuwarsa ,hargaginsa yake gani tamkar daminsa daya ga abinsa kuma yake shirin rasashi domin nuna masa bai ji haushi ya ba ya maida hankalinsa gasu jubi yace "kuyi hakuri frindes ban san maganata zata bata maku rai ba da banyi ba amman ni da wasa nake muku tunda nasan komai yana da lokaci shi aure kamar mutuwa ne idan .." dan allah malam ka rufe mana baki kasani mana “. Kamil ya katseshi yana  zaro masa ido kamar zai cinyesa tare da jan tsaki ,anas ya dan kallesu a firgice zuciyarsa na buguwa da karfi ".
“Tunda kayi aure ka karo sabon wulakanci akan wanda kake yi ,sai  wasu abubuwa kake yi kamr akanka aka fara aure ko zinariya ka aura iyakcin abinda zakayi kenan bare ba zinariya bace mutun ce dai kamar kowa da zaka wani damu mutane ."

tsam jaguwa ya tashi daga shi har laptop da coffee dinsa ya soma tafiya tun kafin zuciyarsa ta tarwatse  dan bazai dauki wannan rashin mutuncin akan jininsa ba ,idan kuma yace zai cigaba da zama to lallai zasaka bakinsa kuma hakan zai sa su yi korafi akan yayi side din anas ,shima Ana's ya tashi tsam ya biyosa zuciyarsa ta tafarfasa sai dai yana ta kokarin tausarta.”
kusa atare suka shiga dakin jaguwa ya samu guri ya zauna a kujerar falonsa qirjinsa na zafi da ciwo shima Ana's ya zauna a gefensa ,jaguwa  bai kalli inda yake ba haka zalika bai ce masa komai ba dan bakaramin haushi ya bashi shi kansa anas ya fahimci haka dan haka ya motsa bakinsa "kayi hakuri ya fad'a yana kallonsa cikin tsananin damuwa ."
Jaguwa ya dan ciza lip's dinsa na kasa da karfi  "me yasa Ana's ?"
"Me yasa kake yin abinda banaso ?"Am so sorry adnan bazan sake ba kuskure ne ya fad'a jiki a sanyaye yana gyara zamansa yana qawalo murmushin dole "tunda sun nuna basa son kana shige musu me yasa bazaka hakura ba ? .”
“Ko dole sai ka tsokanesu? shiru anas yayi yana dubansa “.ya kamata zuwa yanzu ka san yadda zaka dinga yin muamula dasu tunda sun nuna basa son kana masu irin wadan nan zantuttuka na tsokana please ka daina ." murmushi stil anas ya sake yi yana cewa "shikenan an daina inshaallahu "kai fa baka daukar tsanar da suke  maka a kwanakin da mahimanci ,ni kuma na dauke shi da mahimancin daya zarta tunanin jama'a ,a nawa tunanin ma gani nake sun tsaneka ne tsana mai muni amman dai nasan yadda zanyi da...... ".

"Kai haba dai kai kuwa karka yi wani tunanin dabam akansu nifa bana ganin laifinsu ko kadan sai namu,duk kai ne ka jawo komai daga lokacin da'aka boye musu maganr aurena na fahimci basu ji dadi hakan ba shima dalilin sauyawarsu gbdy ,kuma ko ni ne haka zanji  babu dadi araina."
"  duk da haka bai kamata idan ma haka ne ai bai kamata su rike abun  acikin zuciyarsu har haka ba ."lumshe ido anas yayi "babu komai zan sake basu hakuri kai ma ka basu hakuri mu cigaba da rayuwarmu kamar yadda muka saba babu jin haushin juna babu kyashi ko hassada a junanmu sannan ya dauko wayar jaguwa dake ringing ya mika masa sunan da ya gani ne yasa ya ajiye wayar ya dauki cup din coffee ya kai bakinsa yana kurba a hankali.”
kallon mamaki  Ana's ya zuba masa sannan ya dauki wayar yana duba screen din wayar  nan yaga sunan tanwer yana yawo ya waiga ya kalli jaguwa  "ban fahimci kin daukar wayarta da kayi ba?  batare daya kallesa ba yace "bashi da amfani ne shiyasa  naki dauka "ya kamata kayi hakuri adnan haka ,komai na rayuwa fa mai wucewa ne wallahi this duniya is noting adnan yau idan mune gobe bamu bane yarinyar nan tayi nadama dan allah ka yafe mata tana sonka dayawa bazata iya rabuwa da kai ba yana da kyau kasan darajan soyayya me ye laifin wanda ke sonka ?.

"Babu !.
Ya bashi amsa atakaice "to why adnan kaima fa baka kyauta mata ba ,dan bai dace abinda kayi mata a gaban mutane ba ,kamata rashin mutunci a gaban saurayin da bata so sannan ka hadata da kalmar useless ai kowa ma kayi haka zai iya haukace maka .”jaguwa ya saki wani murmushi da ajiyar zuciya atare yana shafa gefen fuskarsa ko yanzu fuskarta ke masa yawo acikin kwakwa luwarsa ,ita kadai ce ta samu wannan matsayin acikin arayuwarsa, dan bai iya mantata duk abinda yake tana nan makale a ransa tana yawo a jinin jikinsa  tun yana mamakin matsayin da take dashi a zuciyarsa har ya zo ya daina."
Sai daya numfasa kana ya motsa lip's dinsa "kenan ta kiraka ta fada maka na kirata da useless?".sosai kuwa dan abun ya dame ta matuka tana min bayani tana kuka "idan har ta fada maka daidai a maganata babu inda nace mata useless ,i said that who is doing that they will be thinking that is useless that's ol ,duk da haka dai bai dace ka fadi haka ba ,a natse Ana's ya dinga rarrashinsa yana bashi hakuri ya yafewa tanwer sannan ya amince da soyayyarta shi kuwa sai murmushi yake yake wa anas yana jijiga kafarsa daya ."

Ana's ya sauke ajiyar zuciya yana dubansa "ka hakura ta kiranka komai ya wuce ?"Kira kuma na  sau nawa ai tun jiya take kirana ban dauka ba dan banga amfanin kiran ba bare na dauka ,dazu da safe ma naga shigowar sakonta ya karbi wayarsa yana nuna masa sakonta ,"Assalamu alaikum ,Good morning how are you doing my love"how was your night ? hope you had a great night?let us thank allah for the gift of another day and please forgive me and forget what I did to you  " girgiza kai kawai anas yayi yana cewa "kai  dai anyi mugu mai taurin zuciya ,
yanzu kai bakajin tausayin yarinyar nan ?ya girgiza kai batare daya kallesa ba .
“Kaga kuwa ni ina jin tausayinta wallahi har hawaye nake zubar mata dan tana mutuwar sonka ,kaso mai sonka adnan ka tausaya mai sonka ko da yake ai kana sonta soyayyarta ma ta musamman ce a zuciyarka ya fada ta tsigar tsoka , jaguwa ya waigo ya kallesa a natse sai dai bai ce masa komai ba hakan kuma ya nuna bazai ce din ba “allah dai ya shiryeka sarkin zuciya da taurin kai jaguwa yayi murmushi yana shafa sumar kansa ,bari  naje na sake bawa friend's hakuri magana ta wuce banason ina tare da mutane naga na bata musu rai “jaguwa yace “sauka lafiya aminin kirki .”anas ya mike ya fita daga dakin shi kuma ya cigaba da aikinsa yana murmushi yana tuna tanwer ".

Suna zaune har lokacin a falon ya samu guri ya zauna yana fuskantarsu sunga shigowarsa da zamansa amman sukai masa banza tamkar basu san da zaman mutun agurin ba ya gyara zamansa ya kirasu "friends!" amman babu wanda ya juyo daga cikinsu ya kallesa bare yasa rai zasu amsa masa "please kuyi hakuri idan akwai wani laifi da nayi muku yasa kuka tsaneni yanzu ,ni dan adam ne ta yiwu nayi muku Kuskuren bisa rashin sani amman ni atunanina idan nayiwa daya daga cikinku laifi kamata yayi ku kirani ya fad'a min domin in gyara kuskurena ,dan idan ni ne bazan rikeku araina ba zan fada muku komai ya wuce mu cigaba da rayuwarmu cikin soyayya da walwala ,dan allah kuyi hakuri ku yafe min ."
Chapter 139 · 0% Book details