← Book details Kuskuren Baya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 25 OF 160

Sashe 25

Kuskuren Baya Part 1 Complete Hausa Novel · about 6 min read

  "shiiiii......." munafurcin  banza kawai   kina dai  son kije kiga wad'an can  rubabbun  samarin naki   barin wancan  me murya  gangarin da bata  dadin  saurara "ya Allah ta furta dan sai  lokacin ta fahimci  a fili tayi maganar , muryarta qasa qasa tace "kafa  san  irin maganar da zaka dinga fad'a  min dan ni din ba motar haya bace bare  kayi tunanin Ina tara kwashe  kwashen  samari Ko da yake yau ne final  kasancewata    da  kai zaka  mayardani  gidanmu  na  gode da  taimako  ta k'arasa maganar tana murgad'a masa  'karamin bakinta "karki gode min ki godewa Allah sannan  na fiki jin dadin zan rabu dake na huta da ganin wannan fuskartaki .
muryarta a raunane tace " aikin banza  kawai  Nima daga yau ai  bazaka sake ganin ko me kama dani bane tayi mgnr tana jan  dogon   tsaki shiru yayi yana ciza gefen lips dinsa can kuma ya murtuke   fuskarsa    yace "wannan shine Karonki na farko Kuma Ina son ya zamo Karo na karshe karki yarda ki sake min tsaki a rayuwarki , ko ni sa'anki ne da zaki dinga ja  min tsaki yayi tmbyr  yana murd'e mata hannu qara ta saki mara sauti tare da cewa "a'a kayi hakuri hannuna zafi  bai mata  magana ba ya sausauta rikon da yayiwa hannun  tare da bud'e tafin  hannun  ya tsurawa tsakiyar hannunta   kyawar Idanunshi yana kallo , a hankali ya d'aura dayan hannunsa ciki  ya fara  mata tafiyar tsutsa wani  irin tsalle hade da bugawa zuciyar tanweer yayi  take tsigar jikinta suka mike kasa cewa komai tayi illa numfashin  da take saukewa  da kyar  tare da jin wani sauyi na dabam  a sansar jikinta.  Shima  wani  irin abu  yake ji yana masa yawo a gbdy ilahirin jikinsa wanda ya haddasawa qirjinsa tsananta bugawa wani tunani yayi gara ya sake musguna mata kafin su rabu   ,wayarsa  ya d'auka ya soma danne  danne bayan kmr second biyu ya kira sunan eku remo dake  tukasu  ."eku ka duba wayarka na  tura maka sako  eku yace "noted  boss ya  tura wa su anas  dake   bayansa  Sako  kamar yadda ya turawa eku sannan ya  koma ya jingina bayansa ya runtse  idanunshi .."

motar    bata  tsaya a koina  ba  sai   gaban   katon    get   din  Rita Lori hotel   dake  onipan  , get  din   already a bud'e yake kamar Koda yaushe security's  ne  tam ciki da wajen  hotel din saboda manya  masu kudi da kusoshin  gwanati  dake zuwa  da manya manyan yan fashi da makami , gurin  fitowa daga ciki hotel  din  dabam haka zalika  gurin shiga dabam , eku ya  sanya  hancin  motarsa  cikin Rita Lori,  d'aya daga  cikin security's din gurin  ya mike da sauri  ya  zare karfen da sakale  Wanda  ke  bawa  mutun damar shiga,   eku  ya   samu  guri ya soma k'okarin  parking  adaidai   lokacin  da motar  alqali  danasu anas   ya shigo
haraban    hotel  ne  dake da  bangare dabam  dabam  dan  shakatawa sam  tanweer  bata fahimci  Inda suke ba saboda ranta dake 'bace .
a natse jaguwa ya fito ya zagayo bangaren da take zaune  ya bud' mata   kofa "fito ko ".ya fad'a  yana furzar da iska mai  zafi  daga bakinsa
ta  yunkura a hankali ta fito  tana  jiran ta ganta a haraban  gidansu kawai ta  ganta a Rita Lori hotel a hankali ta dinga bin gurin da kallo qirjinta na dokawa da matsanacin karfi  tana son gano Inda take bata Ankara ba taji ya riko tsintsiyar  hannunta  ya fara tafiya daita  zuwa cikin had'ad'd'en  club din dake ciki,   banda sautin kidi da waka  baka Jin sautin  komai "Ina ne nan ka kawoni  ? tayi masa  tambayar muryarta a tsarke  "gurin  shakatawa yayi  maganar a dake  yana cigaba  da tafiya daita  yayinda har lokacin  hannunta  na cikin nashi jikinta  na rawa taja ta tsaya  qirjinta na wani irin  bugu fiyye da kaida   juyowa  yayi  ya tsaida  idanunshi  a kanta  take ya fahimci damuwar data shiga adalilin ganinta a Inda suke  "gida  mukayi  da  Kai zaka Kai ni me yasa zaka kawoni nan ?shiru yayi kawai yana bin qaramin bakinta da kallo yana jin kmr ya rungumota jikinsa ya hau  sotsan  lips  dinta  ." ni gaskiya gida nake son  zuwa  ba nan ba ka Kai   gidanmu  tayi maganar  kamar zatayi kuka  dan  tuni hawaye sun gama cika mata Ido kafin kace me hawaye sun shiga turereniyar zubowa har da shesheka  hankalinsa ya tashi dan hk cikin tsarkewar murya yace  "Kinga  dan  Allah ki kwantar  da hankalinki bazan cutar dake ba Kuma bazan bar kowa ya cutar dake ba domin ba haka yasa na d'aukoki ba dan haka ki natsu ki kwantar da hankalinki ya dan yi shiru dan jin me zatace itama shiru tayi saboda jin  maganrsa  " kennan idan ta fahimci maganarsa shine d'an fashin daya d'aukota daga gaban iyayenta  ? wani irin bugu gabanta ya sake yi  da karfi kafin daga bisani qirjinta ya shiga dukan uku uku da numfashinta dake k'okarin  tsayawa hankalinta  yayi matukar tashi ta  dinga maimaita kalmarsa  ta karshe daya furta ."

a hankali ta shiga girgiza Kai "no no impossible bashi  bane sam bai yi kama da irin wad'an nan mutane ba dukkanin  alamun sun nuna shi din mutumin kirki ne ya dai taimaketa daga hannun yan fashi ne   zuciyarta ta  tsayu akan haka ,cikin natsuwa ya juya ya cigaba  da tafiya  cikin Isa da  izza ya barta tsaye adaidai lokacin da alqali ya fito daga cikin motarsa  wani  yawu ta hadeye   tana  qoqarin daidaita  numfashinta da  natsuwarta  ta biyo hanyar da ta ga yabi tana waige waige karaf idanunta ya sauka akan alqali da hannunsa  yayi mata alamar ta tsaya amman dake a tsorace take cikin sauri ta  shiga d'aga ka'fafunta  kmr walkiya ya nemeta  ya rasa Yana nan tsaye su anas  suka fito daya bayan daya suka wuce ta gabansa  kowanne ya kama gabansa kasancewar  kowannensu akwai bangaren  da  yafi so  ."

*******
Tsaye   tanweer    tayi  aguri d'aya  kamar wacce aka dasa tsabar tashin hankali Inda  ta tsinci kanta a yau din nan ,  ta rungume hannuwanta duka aqirji har loakcin sauti ne ke tashi  akoina acikin Rita Lori yayinda jaguwa tuni ya samu guri ya zauna  akan  d'aya daga cikin fararen kujerarun dake gurin  ta waiga bangarenta  na dama tsaye  taga  wasu  matasan   mata  su  biyu    akan  stage  daya  sanye  da kaya  wando da riga yellow dinki gbamu gbamu ka'fafunta sanye da sander  shima baki hannunta rike da speaker  tana rera waka yayinda yaranata ke mata amshi  dayar mata  itama sanye da wando da riga sai dai nata  kalar ja ne gbdy  haraban gurin   shirye  yake  da  fararen kujeru da table a tsakiya ."
tun daga nesa mawakiyar  ta fara bud'e hakoranta dan ganin anas  na shigowa nan take salon wakar ya canza salo  ta soma  masa waka tana sake fad'ada fuskarta da  murmushin  irin nasu na gogaggun  yan  duniya  Shima  murmushi ya sakar mata  sannan  ya soma   qarasowa  Inda take itama ta nufo shi   suka rungume juna har da kiss ta manna  masa a goshi    kana  ya  nufi gurin  empty  chairs   ya samu  guri  ya  zauna zamansa ke da wuya  ma'aikatan gurin suka qaraso garesa  tare da kwalaben giya da soyayyen nama da yaji yaji   domin sun san irin abinda yake bukata kenan  sa'banin  jaguwa da malt  kawai yake sha idan yazo.
Chapter 25 · 0% Book details