← Book details Kuskuren Baya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 160 OF 160

Sashe 160

Kuskuren Baya Part 1 Complete Hausa Novel · about 3 min read

Cikin dakinsa ya turasa "da gaske da bindiga ajikinka ka shigo ?daita na shigo mana ,lallai hakarmu zata cimma ruwa yau zamu taki saa gabadayansu suna nan yanzu sojoji da polisawa da dss zamu kira suyiwa gidan diran makiya na godewa allah yau aikina yazo karshe matsayi na mai gadi ya qare ya dauki waya ya tura sako ,”
suna cikin wannna tautaunawar jaguwa ya fito ya nufi lambu yana zukar wiwi har zai shiga sai kuma adaidai lokacin mai gadi ya fito tare da bakonsa “kaga mu zauna anan kafin su qaraso suna zama sai ga jaguwa yana tafiya yana zukar wiwi yayinda hannunsa daya ke cikin aljihun wandonsa a hankali idanunshi ya kai bakin kofar dakin me gadi mutun biyu yagani zaune yayi mamaki matuka dan haka cikin tsananin tashin hankali ya yar da Karan sigarin hannunsa yana kokarin qarasowa inda suke “tun daga nesa me gadi yace “gashi nan fa shine jaguwa bakinsa kawai jaguwa ya kalla ya fahimci abinda ya fada .”

Yana gama karasowa yace “waye wannan?yallabai kanin abokina ne ya kawo min ziyra byn tsawon lokacin da yayi baya qasar Sa’ad ga gaishesa mana wanda aka kira da Saad ya gaishesa jaguwa bai amsa ba dan haka nan yaji maganar me gadi bata shigewa ba bugu da kari faduwar gaba me tsanani dake kai kawo a qirjinsa kuma ya kasa danganta hakan da matsalar tanwer juyawa yayi ya nufi hanyar baya bai tsaya a koina ba ya sai inda tukunyarsa take kallo daya yayi mata yaga alamun an taba koma yace an canza mata zama daga yadda ya ajiye dan shi mutun ne da ko yaya ka taba masa abinsa zai gane duk kuwa tsawon lokacin da yayi bai waiwayi abun ba .”
Tsaye daya yayi kasancewar dogo ya dauko nan yaji wata sabuwar faduwar gaba sakamakon ganin madubinsa da mahonsa sunyi bakin kiri sabanin yadda ya ajiyesa kuma baba ya fad’a masa duk sanda yayi haka akwai damuwa da sauri ya zagaya ta dayan hannun ya koma bangarensa hankalinsa a tashe yana kiran layin baba yana masa bayani “tabbas aiki aikin wannan alama da kagani alama ce da polisawa zasu iya shigowa gidanka a duk sanda suka so ,haka zalika Wacan aikin na saduwa da yarinyar nan ma ya lalace shiyasa nace ka aureta ka tsaya jayayya danj “kokarin da nake yi kenan ba saboda na kamu da tsanani soya …”bai qarasa maganar ba ya soma jin jiniyar yan sanda a guje ya fito daga dakin sunan Ana’s ya fara qira da karfi sannna sunayensu sauran ya biyo baya cikin kankanin alokacin suka hallara agabansa “ku kulle gbdy windows din part din nan da duk wata kofa da zata fitar da mutun waje akwai da…”

Mmm sudais
Chapter 160 · 0% Book details