← Book details Kuskuren Baya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 67 OF 160

Sashe 67

Kuskuren Baya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

***""
Washegari Jaguwa zaune sanye da riga t shirt da bakin wondo trouser a d'akinsa kayan jikinsa sun balain yi masa kyau  sun haska fatar jikinsa yayi shiru yana fuskantar tanweer dake sanye cikin doguwar riga  data Saka  tun jiya dan ko wanka batayi ba shine dai yayi wanka.
kowannensu zuciyarsa cike take da fargaban rabuwa da juna suna kallon juna ko kifta idanu basa yi , farinciki ne fal a zuciyar tanweer zata gida sai dai kuma wani bangaren na zuciyarta na alhinin rabuwa dashi bangarensa Shima haka ne zuciyarsa cike take da jimamin rabuwa daita yana Jin kamar ya fasa maidaita yabi umarnin baba  suna cikin wannan halin anas ya turo kofar d'akin ya shigo bakinsa d'auke da sallama sam Basu ji motsin shigowarsa ba sai tsayuwarsa akansu sukaji a tare suka d'ago suna dubansa tanweer tayi kasa da kanta sosai taji kunyar ganinsa saboda yasan komai daya faru a tsakaninsu .
shi Kuma jaguwa ya tsurawa anas Ido, cike da farinciki anas ya samu guri ya zauna yana cewa "masoya Kun tashi Lafiya ?"amsarka  ya tafi gurin  koyon sallama zaka wani shigowa mutane babu sallama"
anas ya kwashe da dariya "ai baka cikin haiyacinka Taya zaka San nayi sallama ko banyi ba?idan Kai bakaji ba nasan tanweer taji ko ba haka ba ? yayi mgnr yana dubanta bata ce Komai ba ta sukunyar da kanta Kasa .
"tsaki jaguwa yaja "Kai dai kana son damuwa yanzu me ya shigo da Kai ?idan wani Abu kake bukata ka dauka ka kama gabanka "bana bukatar komai Kuma bazan fita ba zan zauna na cigaba da kallon masoya "oh my goodness anas kana da damuwa ya fada acikin ransa tanweer ta bud'e baki da kyar ta gaishesa "Ina kwana ?"Lafiya lau our tanweer ya hakuri da wannan sarkin zuci....."? saurin katse maganarsa yayi sakamakon take masa kafa da jaguwa yayi  da kargi har sai daya saki qara  ya waigo da sauri inda jaguwa yake zaune  suka hada idanu dashi , jaguwa ya sakar masa katuwar harara yana cewa "our tanwer kai da suwa kenan ?anas yayi saurin cewa "kai kadai ".
"No ka dai gyara maganarka.
"me kake son nace ?nace tamu kace a'a nace taka shim ban tsira ba "ta iyayenta ce karka sake cewa tamu okay ya k'arasa mgnr yana dauke kafarsa ya fuskanci tan .

shiru dukkaninsu sukayi  anas ya zuba tagumi  yana kallon yadda jaguwa ke kallonta  , kowani motsi tayi idanunshi na kanta ,ta mike zata fita ta basu guri da sauri  ya riko tsintsiyar hannunta ya dawo daita "Ina zuwa  ? zani daki na gyara "ki zauna zan sa ayi komai ta koma ta zauna tare da yin shiru ya zuba mata Ido yana Jin wani iri a gabad'aya ilahirin jikinsa "wannan kallon fa kamar zaka cinye yarinyar mutane ayi magana kace ga zance ga magana anas ya fad'a cike da zolaya ..." Kallonsa kawai jaguwa yayi yana  girgiza Kai tare da yi masa alamar ya bar d'akin murmushin gefen baki anas ya sakar masa yana sake bajewa akan kujera alamun babu inda zashi .
daga tanweer har anas suka zubawa jaguwa Ido suna kallonsa anas ya bude baki zai sake magana jaguwa ya d'aga masa hannu "dan Allah malam ka tashi ka wuce na sallameka "kasan Allah babu Inda zani sai naga damar fita zan fita kama bari kaji me zance ka wani katseni "nasan abinda zakace din ne shiyasa kaji nace haka ".
Ya karasa maganar a daidai lokacin da tanweer ta sake mikewa bai Ankara ba sai hangota yayi ta soma tafiya gbdy suka bi bayanta da kallo har ta bar d'akin idanun jaguwa na kanta tafiyarta na matukar Burgesa tana tafiya kamar bata son taka kasa anas ya kwashe da wata  dry yana cewa "mutumina fa ka mugun kamuwa, ka fa shiga cikin wannan fage dayawa baka Isa ka fita ba " jaguwa ya ja tsaki yana kallon fuskar anas "Kai dai wallahi anyi dan matsala".
"Nine ma gidan haya  karewar matsalar jaguwa ya mike yana dafa kafadar anas "bazaka gane ba anas duk yadda zan maka bayani ya mike yana kallonsa "ka fad'a min zan gane kasan fa nafi kowa fahimtarka "ka kamu da son yarinyar ko ?girgiza masa Kai yayi alamun a'a "ai fa matsalarka kenan taurin Kai tsiya  yanxu ko abinda ya faru tsakaninka da yarinyar nan  bai sa kaji wata alama ta soyayyarta ba ?"banji komai ba amman ban sani ba ko byn mun rabu, idan na fara Jin wani Abu akanta I will let you know yana gama fad'ar haka ya juya ya soma tafiya anas ya bishi da kallon banza  "dan iska me shegen taurin Kan tsiya kowa ya ganka yasan Inda ka dosa kana cikin soyayya tsundun amman kake wani kauce kauce ka dai bi a hankali wallahi . "
har ya fita ya dawo d'akin sai dai bai shigo ba "babu Inda na dosa sai Inda ammina ta turani ".
"kaji dashi bakin  munafuki kawai , tsabar mugunta kanka ma sai kayiwa murmushi kawai jaguwa yayi ya wuce Kai tsaye d'akin da take ya shiga bakinsa d'auke da sallama ,ta dago idanunta tana motsa bakinta alamun amsa sallama ya kalleta zaune tana tattara  kayan dake baje a dakin  "bana ce karki yi komai ba ?"naga babu Wanda zai yi ne "wa yace miki babu Wanda zaiyi ?ya karasa Inda wata katuwar jakarsa take me ruwan army green ya dawo Inda take zaune ya zauna ya d'auki kayan ya soma nikewa yana Sakawa cikin jakar"bari hada miki kayayyakinki acikin nan".

ta d'ago idanunta ta zuba masa bai dago ya kalleta ba ya cigaba da abinda yake ,miryarta a sanyaye ta fito "wai wa kake had'awa wadan nan kayan ?
"bakya  so ne"  tayi shiru tana cigaba da kallonsa  "idan kin tafi kin barshi me zanyi dashi ?"ni dai da  ka barshi Ina da Kaya da yawa a gida wasu ma ban taba sakasu ba "wad'an dabam wadan can dabam "sauran minti nawa mu bar gidan nan  ? "kina sona amman kum kina Allah Allah ki rabu dani da wanne zan yarda ? "ka yarda da son da nake maka shine gsky"  ya fesar da numfashi batare daya sake cewa Komai ba.

ta mike ta shiga bayi ta d'auki lokaci sannan ta fito rike da towel tana goge gashin kanta har lokacin yana nan sai dai zuwa lokacin ya shirya mata Komai nata , ta wucesa ta zauna gaban dress mirror ta d'auki cum tana k'okarin taje gashin kanta.
ta cikin mirror taga ya mike kafin ta sauke numfashi har ya k'araso bayanta ya tsaya ya amshi cum din hannunta yana kallonta ta cikin mirrow sosai ta xuba masa Idanunta .
ya d'auke kwayar idanunshi akanta ya  cigaba da taje mata  gashinta baki sitik me sheki ga tsawo kmr na yaran larabawa yana mugun qaunar gashi a rayuwarsa  , ya d'auki man gashinsa ya shafa mata yana jin tsinkewar zuciya ba zai raba d'ayan biyu ba na rabuwa daita ne bayan ya gama shafa mata mai ya cigaba da taje mata gashin ita Kuwa Jin take kamar yana sake kunno mata wutar soayyyarsa ce ,ajiyar zuciyar data sauke da karfi yasashi  sake kallonta ta cikin mirrow murmushi ya sakar mata har dimple dinsa na lotsawa  ganin yadda gbdy yanayinta ya canza wani iri take ji ajikinta ."

a hankali ta rike hannusa da yake taje mata gashi  dashi  ta waiwayo gbdy ta fuskancesa Shima ita yake kallo yana jin wani sanyin na ratsa sansar jikinsa yatsina fuska tayi tana cigaba da kallonsa"ya'akayi ko Ina miki da zafi ne? Kamar bazata fada masa abinda take ji a gabobin jikinta ba Amman yadda ya kafeta da idanu yasa ta mike tsaye tana motsa labbanta "wani iri naje ji a sansar jiki...."
bata k'arasa maganar ba tajita a faffadan qirjinsa ya rungumeta tsam ajikinsa yana fidda numfashi atare qirjinsu ya dinga bugawa da karfin gaske tayi yunkurin barin jikinsa taji ya sake matseta gam idanunshi a lumshe kamar yadda nata yake a hankali ya dinga jin kasala me had'e da sha'awa yana kashe masa duk wata gaba ta jikinsa yana jin kamar ya canza lokaci komawarta ko yaki maidata gbdy su dangwama a haka "lokaci na tafiya  fa ..."
"nasani kin matsu ki tafi kou ?
ya fada yana zareta ajikinsa tare da had'e girar sama data kasa "Allah ba wai na matsu bane Ina son naga dad dina ai zamu dinga had'uwa "Bai zama lallai ba tunda bazaki iya auran dan fashi ba " ya fad'a tare da  juya wa ya bar d'akin.
shiru tayi cikin damuwa ita dai duk runtse bazata auresa da wannan sana'ar da yake ba amman muddin ya canza aiki  sai Inda karfinta ya kare itama zatayi confused din iyayenta akan aurenta da ib su amince ta auresa .
"zaka daina wannan sana'ar  tabbas zaka daina Kuma kana sona tunda har kayi tunanin zaka iya aurena  inshallahu zamuyi aure sai mun Tarawa amminka  jikoki masu yawa kwanciya tayi akan gado tana fidda numfashi sama sama . abubuwan da ya dinga mata daren jiya suka shiga dawo mata daki daki .

Sai laasar sannan jaguwa ya shigo ya kamota ya rungumeta na kusan minti goma sannan ya zaunar daita akan stood ya tattara gashin kanta ya tamke mata da ribbon ya d'auki mayafin rigar jikinta ya yafa mata ya d'auki jakar kayanta ya nufi kofar fita "muje ko jiki a sanyaye ta soma d'aga ka'fafunta kmr wacce ake tsomawa acikin ruwa sanyi  ,duk sai taji kuzarinta yayi kasa komai ya fita aranta a falo ya tsaya ya ajiye jakarta ya bud'e fridge ya d'auki fresh milk da chocolate cake ya mika mata ta girgiza masa Kai alamun bata ci bai sake cewa Komai ba ya zauna ya fara ci ,haushi kmr ya kasheta taso ya sake yi mata mgn dan yadda ya had'e fuskarsa abun har tsoro ya bata ,bai gama ci ba ya ajiye sauran ya mike tana ganin ya mike ta juya kawai taji ya fixgota ya had'eta da jikinshi yana sauke numfashi tanweer ta dan lumshe idanunta tana Jin yadda numfashinta dana jaguwa ke gauraya kusan minti goma suna rungume da juna sannan ya sausauta rikon da yayi mata ya had'e fuskarsu guri d'aya suna shakar numfashin juna .
Chapter 67 · 0% Book details