← Book details Kuskuren Baya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 79 OF 160

Sashe 79

Kuskuren Baya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Tana tafiya tana sake jin faduwar gaba tare da jin motsin tafiya a bayanta ta tsaya cak ta juyo bayanta a natse wayam babu Kowa sai ita kad'ai sai mutanen Dake kai Kawo ta gabanta ta cigaba da tafiya adaidai bakin corridor da zai Kaita office dinta suka hadu da doctor muyis cike da fara'a ta tsaya suka gaisa yana k'okarin janta da magana ta wuce ganin fara'a a fuskarta yau yasa shi jin sanyi aranshi dan haka yabiyota abaya  har ta karaso bakin kofar office dinta bata daina jin faduwar gaba ta tsaya tana k'okarin   bud'e  jakarta ta ciro key  Dr muyis ya amshi jakar hannunta dan ta Samu damar  bud'e kofar a tare suka  Shiga ya maida kofar ya rufe batare da yasa key ba .
Ya ajiye Jakarta akan makeken table din dake office din ta  zagaya ta zauna shima ya samu guri ya zauna suna fuskatar juna office din ya dauki shiru na minti goma sannan ya fara magana zuciyarsa na rawa dan fargaba. "jiya  dr Safina bata fad'a miki sakona bane ?" sai da tayi jim sannan tace "sakon me Kenan ?tayi mgnr batare da ta d'ago ba. ya gyara zama yana sakar mata murmushin sai lokacin ta d'ago ta dubeshi suka had'a Ido
"ya'akayi Dr muyis ?"yace "babu komai Kawai so nake muyi hira "ta sauke numfashi tana cewa "Ai yanzu ba lokacin hira bane lokaci ne na aiki zai fi kyau ka kama gabanka kaje kayi aikin gabanka" ta maida Kanta ta sunkuyar tare da numfasawa.

"nasan kin fahimci wani abu akaina , ta sake d'ago ta dubansa tace "ban fahimci komai ba idan akwai wani abu ka sanar min ina da tarin ayyuka a gabana ya sauke numfashi yace "nasan kin fahimci yadda nake sonki Ko?"ta numfasa sai dai bata ce uffan ba "wallahi ina sonki tanweer kuma da aure ta runtse idanunta tausayinsa ya kamata tayi sauri ta bud'e idanunta a sanyaye take cewa" kayi hakuri kayi addua Allah ya sauya maka wata dan ni zuciyata tayi nisa a soyayyar waninka inshaallah nan kusa za'a shafa fatiha
"inshaallahu Ke rabona ce bata Wani ba ba kuma zan hakura ba har sai an shafa fatiha wanda nake fatan da ni ne "to wannan kuma yana ga Allah domin shi Ke shirya yadda yaso amman dai ina maka fatan samun wacce ta fini domin Ko da zan zamo mallakinka gangar jikina Kawai zaka rayu dashi amman zuciyata baza ka taba galaba akanta ba ".
Ya gyara zama yana kallonta "shikenan na fahimceki amman fa bana jin zan hakura dake ki bani dama mu dinga zantawa koda kuwa a office ne kafin nasamu matsayin zuwa gida .
ta kallesa sai ma ya bata dariya  "kaje ka nemi mata tun kafin a fara kiranka da gwaro dan nasan shekarunka sun kai hamsi ta k'arasa maganar tana murmushi "ki bari na rasa wacce nake so tukun na sai na rufe ido na kwashi Ko wacece inyi maneji "no karkayi haka ai ita rayuwa .."
turo kofar office din akayi tare da  shigowa  ya katse mata maganarta aka   maida kofar  office din aka  rufe garam cikin zafin nama da zafin zuciya .
a natse ta d'ago zuciyarta cike da mamaki rashin neman izini da ba'a yi ba kawai idanunta ya sauka akan jaguwa tsaye ya soke duka hannuwansa ciki aljihun wandonsa ta gaba ,ya balain kafeta da rikitattun idanunshi   yana jifanta da mugun kallo ,
yayinda take  zuciyarta ya soma  bugun tara tara ganin yaki dauke idanunshi akanta yasa ta sunkuyar da Kanta Kasa sannan ta cigaba da duba file din data fara aiki akansa sai dai gbdy komai nata ya  tsaya  dan batayi tsammanin ganinsa ba ji tayi kmr an zari wani abu ajikinta " me ya Kawo Shi gurinta ?" tayiwa Kanta tmbyr da babu mai bata amsa sai Shi .
Dr muyis ya juyo a hankali ganin Kowa ye ya shigo babu neman izini ,shima sai da gabansa yayi mugun bugu da karfi ganin ingarma nmj tsaye sai dai cikin kamala yake sanye cikin bakaken kaya har facing cap dinsa da takalmin kafafunsa da agogon dake d'aure a tsintsiyar hannunsa , ya juyo a hankali ya dubi tanwer fuskarsa da alamar tmbya "dr muyis nayi bako  ka dan  bamu guri ".
"okay my tanwer zan dawo
zuwa anjima mukarasa mgnrmu ya mike tsaye tare da juyawa ya mikawa jaguwa hannu amman kememe  yaki  bashi hannu illa kallon hadarin kaji da yayi masa yana yatsina face, dr muyis yayi mamaki active dinsa zuciyarsa  cike da damuwa ya d'aga kafadunsa ya bud'e kofa ya fita  .
kusan minti biyar shi  bai fita ba sannan shi  bai karaso inda take ba, dan haka  ta mike tsaye da zumar bar masa office din  idan ya gaji yasan inda dare yayi masa ta gefensa tabi zata wuce cikin zafin nama yasa hannunsa daya  ya dawo daita ya tsayar daita a gabansa batare daya ce mata komai ba ya tsura mata rikitattun Idanunshi masu bugar mata da zuciya ....."
wani yanayi mai tsarkakiya da wuyar fassarawa ya ziyarci gangar jikin duka masoyan guda biyu a bangaren tanwer tsantsar soyayyar da qaunar jaguwa ne yake bin dukkan ilahirin sansar jikinta ,ji take Kamar ta mutu ta huta akan wahalar da take sha akansa . "
Shim abinda yake ji Kenan a sansar jikinsa  ji yake Kamar ya zarta dukkan maza sa'a  a duniya data makance akanshi, sun shiga wata duniya wanda ma'abota so da shauki ne  suka san zakinta a hankali yake Jin qaunarta na sake huda zuciyarsa yayi taku biyu ya had'eta da qirjinsa yana fidda wani wahalallen numfashi.."
saurin dauke numfashi tayi tana so shi kamr ranta ita Kanta tana mamakin zazzafan soyayyar da take ma jaguwa mai tafiyar da dukkan wani motsi  da bugun zuciyarta da numfashinta .
yadda soyayya Ke walagigi da zuciyar tanwer haka ne yake faruwa da zuciyar jaguwa a sukwane ya motsa lips dinsa ",waye wancan mutumin daya tasaki gaba kamar zan ciyeki "? ya k'arasa maganar cikin zafin rai ."
Shiru ya biyo bayan tambayarsa dan bata jin zata iya bashi amsa idan tace lallai sai ta bud'e bakinta to kuka ne zai biyo baya ta juya a hankali zatabi ta gefensa hannunsa ya kai ya rike tsintsyar hannuta gam ya karasa gaban table dinta ya d'auki handbag dinta ya makala mata a kafad'a  ya soma tafiya daita har ya fito daga cikin office din  magnata  take  son yi amma  bakinta ya kasa furta komai   illa jikinta dake wani irin rawa sakamakon had'uwar da jikinsu yayi , bai tsaya a koina daita ba Sai a inda yayi parking din motarsa ya bud'e mata gidan gaba  ya Sanyata ya rufe ya zagaya ya Shiga ya tada motar  ya bar haraban hospital din."

Sosai yake gudu akan titi  batare daya Kalli inda take ba ,itama bata Kalli inda yake ba idanunta na kallon gefen titi ,dan cija lips dinsa yayi yaso tayi masa mgn  amman yaga ta sharesa saboda taurin kai irin nata dan haka bai yi mgn ba  shima ya yatsina fuskar ya cigaba da tukinsa sunyi tafiya mai nisa still bata juyo tace masa ina  zai Kaita ba har ya karaso bakin get din gidansa yayi hon aka bud'e masa get ya shiga da motarsa ya k'arasa inda aka tanada domin ajiye motoci yayi parking sannan ya kashe motar ya bud'e bangaren da yake a hankali ya fito ya zagayo side dinta ya bud'e mata kofa ya tsaya yana kallonta muryarsa a kasalance  yace "fito !
"Na fito nayi me ?" sai lokacin tayi mgnr cikin karfin hali da dakiyar zuciya .
"Bansani ba kuma Karki kara bani irin wannan amsar Oya  fito" .ya fad'a yana zabga mata  harara kin fitowa  tayi ta makale  handbag dinta ta  cigaba da zama tana girgiza masa jiki tana yatsina fuskar .
on-expecting taji ya sunkuceta ya fito daita ya shiga cikin gida daita  suna shiga babban falon gida ya sauketa  yana cewa "daman abinda kike so Kenan jikina ya hadu da jikinki gashi nan  nayi miki abinda kike so ."
Ta kallesa idanunta cike da bacin rai  ta rasa me yasa yake mata haka "ki samu guri ki zauna doctor na zuwa ta duba min lafiyarki idan aka dubaki  baki dauke da ciki sai kinga yadda zanyi dake a gidan nan  duk sai na fanshe d'aga min hankalin da wahalar dani da kikayi".
still dai bata ce uffan ba sai tagumin  da tayi cike da zullumi abinda zai mata .

Byn minti shabiyar sai ga doctor tayi sallama ya bata umarmin shigowa ta shigo suka gaisa da jaguwa Kawai dan ita tanwer Ko kallon inda take batayi ba .
ya mike tsam  ya k'arasa inda tan take zaune cikin tashin hankali  ya riko hannunta cikin nashi batare daya ce Mata komai ba ya fara tafiya doctor na biye dasu Abaya  yana mata bayani abinda yake bukata tayi masa  har cikin bedroom dinsa  suka shiga ya zaunar da tan sannan yaja ya tsaya tare da rike kugunsa da hannun daya yayinda dayan hannunsa Ke qirjinsa yana shafawa a hankali .
Doctor  ta ajiye kayan aikinta  ta kalli tanwer sannan ta mika mata wata karamar roba "ki shiga bathroom kiyi fisari aciki ki Kawo". kin amsa tayi sai da jaguwa ya maka mata harara sannan ta amsa ta nufi bayi bata jima ba ta fito ta mikawa doctor roba ta samu guri ta zauna tana mamakin karfin halinsa da rashin tsoronsa .
Chapter 79 · 0% Book details