← Book details Kuskuren Baya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 32 OF 160

Sashe 32

Kuskuren Baya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

a hankali ya dinga nuna mata komai daki daki kitchen  din  very Niet  kamar mace ce ke amfani dashi  babu abinda babu na kayan abinci  komai gashin nan  ajiye   yasa  an  kawo," ki duba ko akwai abinda bai miki ba a canza akawo miki wanda kike so ".  idanunta  da suka canza kala sukayi jazir  tsabar kishi ta d'ago ta sauke su akan fuskar  jaguwa dake tsaye a gabanta  yana kare mata kallo ,Shep dinta yafi komai daukar hankalinsa irin  matan nan ne masu  shep din cocakola   "dan tani da baka tanadin wad'an nan abubuwa ba dan ba sune abinda nafi bukata ba bukatata na .." ".shiiiii ya d'aura yatsansa akan lips dinta yayi kusa kusa daita har suna iya jiyo numfashin juna wani irin tsalle zuciyoyinsu yayi  wanda har sai da hakan ya haifar musu da tsayuwar numfashi , take jikinta ya soma kyarma   rungumeta   ajikinsa  yayi tsam yana busa mata numfashinsa .
 tuni zuciyarta ta karye hawayen kishinsa da kewar gida   ya soma zuba bisa kuncinta ya rungumeta  sosai ajikinsa kamar zai mata numfashi yana shafa gadon bayanta .

wani irin haushi  ne  da bata ta'ba  jin irinsa  ba  ya diran mata a kahon zuciya  ,kullum yana ikararin baya sonta amman ya iya nesanta kanshi daita yana son maidata yar  iskar karfi da  yaji   ta soma mutsu mutsun kwatar  jikinta domin zuwa wannan lokacin   zuciyarta  ban da zafin  kishinsa babu komai aciki ,ganin yaki sakinta yasa ta soma dukan qirjinsa da iyakacin  karfinta amman yaki sakinta  ya kamkameta tsam  yana son yaga karshen karfinta   "Kai dai wallahi mugu ne Kuma azalumi inshallahu yadda kake quntata min wallahi Kai ma sai Allah ya  quntatawa  kannenka ".  cak  ya saketa   yana furzar da numfashin mai zafi  daga bakinsa   idan  akwai abinda ya tsana bai wuce a ta'ba kannensa ko aibantasu da mugun abu ba . ta zube kasa bisa gwiwowinta tana wani irin kuka tare da Kiran sunan iyayenta , muryarsa  a tsarke yace"tan ...."bata d'ago  ta kallesa ba "karki sake sako kannena cikin shirmenki   idan kina son ki zageni kiyi amman kannena karki sake ."
"Dan Allah malam ka min shiru daga yanzu  muddin  baka maidani ga iyayena ba  wallahi na dinga ma kannenka  mugayen fata kenan , ada na dauka ka taimakeni  ne sai dai a yanzu taunina ya  Kashi dabam dabam tare da tambayoyi masu wuyar amsawa "waye Kai Adnan ? Ka fad'a min waye Kai Ina son sani kai din  waye ?cikin sauri ya juya ya bar kitchen din   zuciyarsa na rawa bai ta'ba Jin tsoron wani yasan sana'arsa ba ko sanin ko shi waye  sai yau , bazai iya sheida mata shi din waye ba , zai barta a matsayinsa na me taimakonta  bazai ta'ba yarda tasan ko shi waye ba yana tafiya yana jan tsaki ji yake kmr zuciyarsa zata buga .
ya rufe kofar falon ya fita zuwa  haraban gidan , tuni su  kamil ,anas, jubi, da jabir  da sauran yaransa sun hallara har wasu ma sun shiga mota sun zauna  shi kadai suke jira yana daf da karasowa eku ya  bud'e masa gidan baya ya shiga yana  cewa "hope  kowannenku  yayi shiri  me  kyau? "  sosai  suka bashi amsa  motarsu na kokarin fita daga gidan Idanunsa  ya sauka  akan wani dattijo  zaune a gindin bishiyar dake gefen gidansa nan take yace wa eku "stop ! ".eku  ya tsaya   nan take mutumin ya mike tsaye yana kallon motocin  jaguwa masu shegen kyau da  daukar hankali da hannu ya yafito  me gadi  ya k'araso  da d'an saurinsa  ya   tsaya yana rusunwa  "wacan mutumin fa me yake yi  anan ? "wallahi oga gurinka yazo wai yana son ganinka tun jiya byn fitarka yazo nace baka nan shine dazu byn dawowarka sai gashi ya dawo  na  shiga domin nasar maka sky  yace Kuna meeting shine na dawo na sheida masa ya dawo Koda karshen sati ne amman yace lallai sai ya ganka ."

shiru  jaguwa yayi  yana nazari sannan ya dan Kalli Inda dattijon  mutumin yake tsaye cikin kod'ad'un kaya marasa fasali  yana cigaba da nazarinsa ,a hankali ya fito ya soma tafiya   har ya k'araso garesa , dattijon na ganinsa ya shiga rawar jikin "barka da fitowa ranka ya dade  "barkanmu  baba ya kwanan iyalin ?" Alhamdulillah duk muna Lafiya  ,
jaguwa ya kad'a Kai sannan yace  " baba fatan  dai lfy kake son ganina ?"dattijon ya marairaice murya  kmr zai yi kuka sannan ya fara mgn muryarsa na rawa gwanin tausayi "daman matsalace ke tafe dani gareka a wajen mutane na samu labarin irin taimakon da kake yiwa mutane ".  jaguwa na jin haka ya sauke numfashi yana dubansa a tsanake  " Ina Jinka baba wacce irin matsalar ce ?"daman akan yarona ne  shekararsa biyar kenan da kammala karatunsa  na  degree sai dai  yadda kasar nan tamu ta  dawo yasa  har yanzu yake gida zaune, duk Inda yaje apply din aiki sai ace sai ya biya kamin dubu dari biyar kudin office kafin a daukeshi  gashi  bashi da hanyar da zai samu kudin,  ni ya kamata na biya  masa ya samun aikin  to ni din ma babu dan na abinci ma da kyar muke samu, dan Allah ka taimakeni kamar yadda Allah ya taimakeka  ka samo masa aiki ko Kuma  ka yarda ya kasance a karkashinka ya karasa maganar yana zubar da hawaye ."

jaguwa yayi shiru yana sauraronsa har sanda ya dasa aya "karkayi kuka baba    inshallahu zan yi iyakar kokarina  yanzu dai Ina kan hanya ne zani wani  aiki amman ka dawo zuwa  karshen sati da yaron   inshallahu matsalarka  tazo karshe dattijon ya soma k'okarin durkusawa jaguwa domin yi masa godiya, jaguwa  yay saurin sa duka hannuwansa ya taresa "haba baba karka min haka  mana " na gode  d'ana Allah ya albarkaci rayuwarka , Allah yasa ka gama da duniya lafiya ,Allah ya jikan iyayenka  idan sun rigamu gidan gsky, idan Kuma suna raye Allah ya Kara musu Lafiya mai amfani na gode na gode  daman da gaske ana samun mutane irinka  ?karka damu baba ya k'arasa maganar yana tsaida dattijon bisa kafafunsa ya Ciro  dubu goma  a  aljihun wandonsa ya mika masa "ga wannan kayi kudin  mota  yana gama mikasa ya juya ya shiga mota suka bawa motacinsu wuta suka bar unguwar ,da sauri dattijon ya Ciro  wata rubabbiyar   wayarsa ya shiga neman  number d'ansa  domin yi masa albishiri  ."

******

Bangaren  minister of health  kuwa  gbdy  hankalinsa yaki kwanciya   kullum yana manne da hjy zainab yana rarrashi wacce kuka ya zame mata abincin ruhinta , yanzu ma zaune yake kusa daita  yana aikin daya  saba tare da babban  amininsa alhj Tahir  dake k'okarin shawo kanta   "kada kiyi fushi  da hukuncin  Allah  zainab  wannan  abu daya faru gbdy bai mana dadi ba sai dai  bawa  baya wuce qaddararsa  Allah ya rigada ya  qaddaro surayya zata fad'a cikin wannan tashin hankali bamu Isa mu canza mata qaddararta ba,  fatan mu  dai Allah yasa bata cikin tsanani cikin muryar kuka tace "na kasa  jurewa   dady  dake hk take kiransa kmr yadda Ib ke kiransa "  yau  da mutuwa tanweer tayi na binneta da  zan fi samun natsuwar zuciya  amman Ina raye tanweer  tana hannun  'yan fashin da ko labarinsu ba'a samu ba , taya kuke tunanin hankalina zai kwanta ?".  Suma kiramu muji me suke  bukata daga garemu sunki  ta k'arasa maganar tana kallon saman falon hawaye masu zafin gaske na gangaro mata wanda zafinsu da rad'ad'insu ya wuce tunanin mai karatu .
"wannan haka ne  amman duk da haka  addua zamu  taru muyi allah ya bayyanata cikin koshin lfy "amen ta furta a kasan makoshi tana cewa ya jikin Ib kuwa?   kullum Ina sa ranar zanzo na dubasa   mutanen dake shige da fice agidan nan  zuwa jaje ke hanani  fita ammn inshallahu zan samu lokaci na  leko na dubashi  .
"to jikinsa dai da sauki zamu ce Allah dai ya iya mana  da iyawarsa dan rayuwar Ibrahim na daf da fuskantar matsala da Kuma qalubalin rayuwa ya kasa jurewa rashin tanweer  "Allah  sarki ib yana qaunar  tanweer  kmr yadda yake qaunar rayuwarsa  inshallahu zata dawo har ma suyi aure  ta k'arasa maganar tana sake matso ruwan  hawaye sun dade suna tautauna wa akarshe  minister ya  kira  cp  yaji halin da'a ake ciki  ,byn  cp   ya d'auki Kiran  suka gaisa "wai ya ake ciki ne da batun yarinyata  shirun fa yayi yawa zuciyata ta fara tsinkewa Ina Jin kamar Allah ya d'auki raina  na huta ? na kasa jurewa rashin diyata da rashin kwanciyar hankalin matata ".naunayen ajiyar zuciya cp  ya sauke sannan ya fara magana a natse"mun baza mutanen mu  cikin   gari    yanzu haka mun  fara  samun improvement akan lamarin   "to alhamdulillah   Allah ya taimaka   yasa aga  yarinyata  cikin koshin lfy "karka damu inshallahu komai yazo karshe ka kara mana lokaci kad'an "na gode na gode "  sukayi  sallama minister ya  fuskanci  hjy zainab tare da yi mata albashiri da abinda cp ya fad'a masa  nan take farinciki ya mamaye zuciyarta  shi kuwa alhj Tahir  cikinsa ne  ya duri ruwa gabansa ya  shiga  fad'uwa hankalinsa yayi kololuwar  tashi .
babu shiri yayi musu sallama   ya  shiga motarsa direbansa ya ja suka  kama hanyar zuwa gida ,yasan ya taro wa kanshi  match tunda yayi sanadin da'aka d'auke tanweer  wayarsa ya Ciro yanata  Kiran number jaguwa  ana ce masa akashe  take har ya k'araso gida bai samesa ba ,  ya rasa yadda zaiyi da rayuwarsa  yasan muddin  su jaguwa sukazo  hannu   kashinsa ya  bushe domin asirinsa ya tono ."
Chapter 32 · 0% Book details