Sashe 56
Kuskuren Baya Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read
jaguwa ya sake watsawa sadiq harara yana cewa "Allah ammi karki amince da maganarsa ba budurwata bace taimako nayi "taimako! ?ta tmbyesa tana tsura masa idanunta domin gano gaskiyar dake zuciyarsa ,ya gyada mata Kai alamun "eh ".
to ai shikenan idan dai har ka bata lokaci Allah auren dole zan maka na huta da wannan shan kamshin da kakewa aure ta k'arasa maganar tana cewa shafiqa "jeki zubowa yayanki abinci da sauri ta mike ta fita ko cikakken minti biyu batayi ba ta shigo rike da plet ,hally ta mike ta janyo karamin stood gabansa shafiqa ta ajiye abinci tare da bude masa cike da farinciki suka dinga Ina na Saka Ina ajiye da yayansu kowannensu na kokarin faranta masa, cike da matsanacin farinciki da soyayya jaguwa ya kai loman shikafa da miya bakinsa ya ajiye spoon shima sadiq ya matso ya d'auki spoon din da jaguwa yayi amfani dashi ya Kai bakinsa ,ya ajiye spoon jaguwa ya sake d'auka Sadiq yace "gsky father ya dace yadda kayi kyau din nan na rakaka gurin yarinyar nan zance Allah Kun dace ban ta'ba ganin mutanen da suka dace da junansu ba kmar ku ba ......"jaguwa ya wani kallesa shekeke yana cewa menene Kuma zance ? yayi mgnr tare da ajiye spoon din hannunsa ya d'auki tissue yana goge bakinsa "haba father karka waske mana ni dai dan Allah ka auri yarinyar nan wallahi tayi min "na fika sanin tayi aurenta ne dai bazan yi ba kwarya tabi kwarya ya fad'a a zuciyarsa .
"kasan Allah Sadiq yayanka Adnan yafi karfin zuwa wani zance ko menene kace sunansa Allah dai ya tsareni da ..."wani kallo da ammi tayi masa yasa shi katse abinda zai ce ya yamutsa fuska yana lumshewa ammi Idanunshi "duk kagama cika bakinka Muna nan zaka zo kayi auren ai duk dan sunan dole zai so aure "Allah ammi ko zanyi aure bazan je wani zance ba wannan zuwa zance fa kauyanci ne " agurinka ba me ra'ayin rikau amman meye na kauyanci aciki ?"
Allah ammin bayan kauyanci har da lalata Yara yake shi yasa kikaga bana son yaran nan nayi zance "a'a ban yarda da mgnrka ba zance baya wani lalata yaro sai dai can yaron dan iska ne Amman irin zance da shafiq ke yi taya yaro zai lalace a parlour'n nan suke zama gashi mutane ma na Kai kawo Kai dai ka Maida hankali ka tsaida matar aure ,
ni jikina ma ya fara bani lokaci yayi ".sadiq yayi tsigil yace "sosai ma kuwa ammi sai ma Kinga yarinyar dana ganshi daita Allah cewa zakiyi ya aureta kawai "Nan fa hirar ta juye zuwa ta aure jaguwa ya wani shagwa'be fuska kamar karamin yaro yace "ni dan Allah ka rabani da zance aure nan ,nifa auren nan ban ta'ba Jin zanyisa nan kusa ba Kuma ma idan zanyi zanyi ne dan ya zama sunnah da faranta ran ammi Kuma ko zanyi sai na nemo wacce zatayi hakurin zama dani ba wacce zan dinga rage murya ba Ina kaskantar da kaina ba, kasan fa mata idan suka ga ka damu dasu sai salo da iskanci ya tashi babu ma abinda ke bani takaici kmr kaga katon nmj a gaban karamar yarinya yana rage murya da kaskantar da Kai wai duk akan a amsa masa soyayyarsa Kai Allah bazan iya ba ni kawai idan ma ya zama dole Allah umarni kawai zan bata tunda ya fara mgn sadiq da kannensa mata har ma da ammi suke dariya.
Shi kuwa jaguwa yayi dip kmr anyi ruwa an d'auke ,duk yadda sadiq ya so acigaba da mgnr tanweer jaguwa yaki sai ma ya kawar da hirar ya shiga tmbyrsu abinda basu dashi a gida anan yayi sallahr magrib da isha'i
Hira sukayi sosai har lokaci yaja ya duba agogon hannuna karfe shadaya saura ya mike yayiwa ammi sallama byn ya ajiye mata bandir din kudi yan dari biyu biyu suka fita tare da sadiq domin yi masa rakiya ya shiga motarsa ya kunnata ya bata wuta sai da sadiq yaga tashinsa sannan ya koma gida ya rufe .
Koda ya koma gida bai bi ta kan kowa ba har ma tanweer ya shareta ,ita Kuwa idanunta shi suke son gani ta sake neman afuwansa amman yaki shigowa Inda take ranar da kyar ta runtsa kwana tayi juyi da kuka .
Washegari ta shigo d'akinsa bakinta d'auke da sallama yana kwance a akan doguwar kujera a falonsa dan tun bayan daya dawo sallah asuba yake kwance agurin ta ra'be gefe guda tana dubansa ,a hankali ta k'arasa ta tsugunna a gabansa tana kallon gefen fuskarsa Inda ta maresa ,saukar numfashinta akan fuskarsa yasa shi bude Ido eyes to eye's suke kallon juna "sorry for my active kayi hakuri nasan har yanzu kana fushi dani "ya juya mata baya yana jan tsaki ta sake matsowa sosai ta Kai hannunta jikinsa ya buge mata hannu da karfi ta rike hannunta tana runtse idanunta dan taji zafi sosai har cikin ranta taji dukan .
take gumi ya shiga tsatsafo mata a goshi da karan hancinta muryarta a shagwa'ba tace "yanzu bazaka yafe min ba ?banza yayi mata kamar bai san da wani halitta agurin ba "ki tashi ki bar d'akin nan tun kafin na tashi nayi miki abinda banyi niyya ba . "ka yarda nayi nadama "dan ubanki karkiyi nadama maza ki tashi ki bar d'aki ya fad'a yana mikewa tsaye da sauri itama ta mike tsaye"oya out of this room "dan murmushi gefen baki tayi tare da matsoshi sosai ta rungumeshi tsam ajikinta kamar za'a kwace mata shi, jinta ajikinsa yasa shi Jin wani iri muguwar kasala ,tayi lif a faffadan qirjinsa tana shakar numfashinsa da kamshi turarensa me d'aga hankali.
a hankali kowannensu ke sauke ajiyar zuciya muryarta a matukar sanyaye tace "karka sake zagin ubana ko zan d'auki komai ban da zagin mahaifina ka kiyaye harshenka " shiru tayi tana jiran abinda zai ce hannusa yasa ya zareta ajikinsa "tunda shine abinda kika fi tsana daga yau shi zan dinga fada miki "zan kuwa rama tunda uba bai fi ba "bar d'akin nan ya fada a fusace yana nuna mata kofa "karki sake shigo min daki "Kai ma haka karka sake zuwa Inda nake "wai ni sa'anki ne da ina fada kina fad'a?yayi mgnr a matukar hassale yana kokari damkota ta zame tayi baya da sauri tare da yi masa gwalo da karkad'a masa kunnuwanta.
tsura mata tsumammun idanunshi yayi kawai ya kasa cewa komai taku d'aya yayi ta kwasa da gudu ta bar d'akin ya ja dogon tsaki "zanyi maganinki ne ."Tun daga ranar bai sake shigowa Inda take ba hatta abinci ya daina kawo mata , lura da so yake yayi punishing dinta da yunwa yasa hankalinta ya tashi sosai ta shiga damuwar halin da zata shiga idan ta wuce kwana daya nan gaba batare data sakawa cikinta wani abu ba .
Sai da yayi kwana biyar yana fushi daita sannan ya sauko ya shigo domin kawo mata abinci ya ajiye mata farar leda zai fita tace "malam ka dawo ka d'auki abincinka bana ci duk kwanakin nan da baka kawo min abincin ba na mutu ne ?"ban mutu ba dan haka ka dauki kayanka ba zanci ba zan cigaba da zama haka har na bar gidan nan.
wani murmushin gefen baki yayi sannan ya juyo ya fuskanceta sosai yaga ta rame acikin kwanakin da yayi bata ci komai ba taku d'aya ya K'ara ya fara mgn cike da dakiyar zuciya "Kinga rashin cin abincinki ko rashin walwarki bazata dameni ba ,saboda bana sonki bakya cikin rayuwata bakya gabana ,kisan Allah ko nemanki na sake yi na rasa yanzu bazan damu ba saboda na lura baki da mutunci, bakida kirki ,baki da biyayya biki san komai ba sai zallar rashin kunya ,ada Ina matukar jin tausayinki da gudun abinda zai cutar dake amman a yanzu duk babu wannan , zan cigaba da rikeki ne dan na musguna miki dan fahimci kina qaunar komawa gida kamar yadda kike qaunar rayuwarki". yana dasa aya ta fashe da kuka tana cewa "Allah ya Saka min wallahi sai hakina ya bibiyi rayuwarka ni wallahi dama kasheni kayi na huta .
"bazan kasheki ba zaki zauna ki cigaba da ganin rayuwa a gidan nan , sannan babu abinda zai bibiye rayuwata bakinki bazai kamani ba danke ba uwata bace
yana gama fad'ar haka ya fice daga dakin ya barta tana kuka yana fita ta hau share hawayenta da hannuwanta duka ta Isa Inda ledar takeway yake ta bud'e ta fito da takeway jikinta har rawa yake ta soma cin abincin tana zubar da hawaye ."