← Book details Kuskuren Baya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 6 OF 160

Sashe 6

Kuskuren Baya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Shhhh! yayi saurin katsesu tare da cewa "tare da ita zamu tafi idan kuka yi kuskuren sheidawa police tabbas zaku rasa d'iyarku har abada " Jaguwa ya fad'a tare da fusgar Tanweer wacce tunda suka fito idonta ke rufe saboda tashin hankali, jin da tayi zai tafi da ita yasa ta bud'e idannunta ta soma ko'karin gudu, cak Jaguwa ya d'agata ya da'ura a saman kafad'arsa tana ihu tana kiran suna iyayenta tana dukan bayansa sai dai bai direta a ko ina ba sai a cikin motarsa, pito jabir yayi da bakinsa duk suka hallara suka shiga motocinsu suka ja da k'arfin gaske ..

Hajiya zainab najin barinsu gidan ta soma buga kanta da kujera tana ihu tana kuka "shikenna sun tafi min da yarinya minister ya mike ya nufi dakinsa ya dauko wayarsa ya soma zagaye parlou'n yana neman number police ta mike a firgice ta fixge wayar tayi jifa dashi " idan ka kirasu zasu kashe min yata shikenna na saura bani da kowa ta karasa maganar tana zaman dirshan a kasa tana dukan cinyarta , ya karaso gareta ya dafa kafad'arta "ki kwantar da hankalinki dole sai hukuma tashiga cikin wannan matsalar babu abinda zasu yi sun fadi haka ne saboda su tsoratarmu yana gama fadar haka ya mike ya sake ɗaukar wayarsa ya kira number IG cikin Sa'a bugu daya ig ya ɗauka ko cikkake minti goma ba'a yi da tafiyar su jaguwa ba police suka karaso har da Ibrahim daya amsa Kiran minister sun so subi bayansu Hajiya zainab ta hanasu tana tabbatar musu da abinda yan fashi suka sheida mata "wannan ba wani abun damuwa bane zamu san abin yi ina Camera gidan take ta haka zamu samu sauƙin bincike ,kai tsaye minister yayi hanyar waje dasu yayinda Ibrahim yayi mutuwar tsaye qirjinsa na wani irin mahaukacin bugu ,nan police suka shiga bincike gidan sai dai babu wata hanya dasu jaguwa suka bari domin ganosu sun bata komai jinjina kai sp yayi "wadan nan yan fashi sun san abinda suke sannan sun kware matuka a gurin taaddanci sai dai duk da haka zamu san abun yi suka ci-gaba da zagaye gidan inda suka dinga cin karo da polisawan dake tsare da gidan a kwance da alamun wani abu aka shaka masu .....

Wani irin gudu motocinsu ke yi a saman titi kamar zasu tashi sama yayinda Tanweer take wani irin kuka a jikin Jaguwa har da cizonsa sai dai ko gezai bai yi ba ganin ta damesa yasa yayi mata mugun bugu a kafad'a nan take ta sulale ajikinsa ta sume kamar matacciya bata k'ara sanin inda kanta yake ba har suka iso gidansa ,Jabir yayi ko'karin da'ukarta zuwa ciki Jaguwa yayi saurin dakatar dashi ta hanyar buga masa muguwar tsawa ya zaga da kansa ya d'auketa ya sabata a kafad'arsa zuwa cikin gidan.

"Meke damunsa ? me yasa ya daukota?"Jabir ya tambaya Anas dake tsaye kusa dashi yana ƙoƙarin cire face marks din fuskarshi "Uhm nifa Ina tsoron kar dauko wannan yarinyar ya samu a matsala fa yar Minister ce... "Shhhh! duk Ku yi shiru boss yasan me yake ba abunda zai faru" Anas Ya basu amsa yana cire Safar hannunsa duk suka kalli juna da sauran da kusan a tsorace suke sannan suka nufi wani bangare na gida da jakunkunan kudi ..

Kai tsaye d'akinsa ya wuce da ita direct ya k'arasa da ita bakin makeken gadonsa ya shimfid'eta kamar wata baby yana ko'k'arin d'agowa idannunsa suka Kuma fad'awa kan 'yan nonuwanta da rigar baccinta ta janye zuwa gefe guda har yana iya ganin kan nipples dinta dake tsaye cikakku gwanin burgewa.
Wani irin yawu ya had'iya Kamar wanda aka taba yayi saurin mik'ewa yana mai runtse idannunsa na second biyu sannan ya bud'esu ya sake k'ura mata ido , yarinya ta had'u sosai ya furta hakan a kasan ransa , girgiza kansa yayi ya shiga bathroom dinsa dake manne da d'akin ya dibo ruwa a cikin roba ya dawo ya zauna kusa daita ya shiga shafa mata ruwan a fuskarta zuwa qirjinta ,a hankali ta sauke naunauyen ajiyar zuciya sannan ta cigaba da sauke numfashi da kyar ,fuskarta tayi jazir saboda kukan data yi, gashin kanta ya kwanto gefen fuskarta ,sauko da kyakkyawan idanushi ya yi akan cinyoyinta dake waje a dalilin rashin sakowar rigar baccin sosai , Kallonta yake har sanda ta takure jikinta guri daya tana turo masa karamin bakinta ya kai hannunsa ya ja blanket dake gefe ya rufe mata jiki yana furzar da iska mai zafi daga bakinsa .

sanyin A/c d'in dakin yaji yayi yawa ya d'au remote ya rage maimakon ya fita sai ya tsinci kanshi da zama kan side chair dinshi me laushi da kyau, fuskarshi na fuskantarta har wani lumshe ido yake yana cigaba da kallonta kwance a takure yayinda numfashinta ke sauka a hankali ya jima zaune daga bisani ya kashe light d'in da'kin sai hasken corridor dake haskata ,cike da jarumta ya soma cire kayan jikinsa ya nufi bayin ya tsaya yana sakarwa jikinsa ruwa bai dade ba ya fito ya sauya kaya ya fita daga dakin zuwa wani dakin dake kallon wanda take kwance ya kulle kansa daman kuma ka'ida ne duk sanda yayi operation Sai yayi wannan wanka tare da kebe kanshi .. .

Washegari

A hankali ta soma motsa idanunta da mika har ta farka tana buɗe idanunta kadan kadan , ganin inda take yasa ta karasa bude idanunta da sauri, tana kallon dakin data tsinci kanta , babu abinda babu na more rayuwar duniya ,ga wani sihirtaccen kamshi na musamman dake tashi mai haɗe da sanyi ac lokaci daya zuciyarta tayi wani irin bugawa da karfin gaske runtse idanunta tayi saboda motsin taɓa kofar dakin data ji anyi dan bata son ganin fuskar mutumin daya daukota daga gidan iyayenta , tsawa taji an buga mata "ke dan ubanki zaman me kike yi fito min a daki cike da razana ta bude idanunta wanda ta gani tsaye a gabanta ne yasa ta zaro idanuwanta waje cike da mamaki , yana tsaye a gabanta rike da gefen kugunsa ya haɗe gira sama data kasa idanunta ta murza domin tabbatarwa kanta mafarki ne ko kuwa a zahiri shi take gani a gabanta ...

DARLING'S

💗💗💗💗💗💗
KUSKUREN BAYA
💖💖💖💖
💗💗💗💗💗💗

WRITING BY
*BAGUDO& MIMI'S QUEEN*

WATTPAD @HAUESH

bismillahirrahmanirrahim

https://my.w.tt/lcJskJdtpbb

🅿️04

Ganin tabbas mutumin da idanunta suke kwad'ayin sake had'uwa dashi ne a gabanta, yasa ta mike tsaye tana fad'ad'a fuskarta da murmushin da ita kanta bata san dalili yinsa ba , ta tsaya a gefensa bata damu da yanayin yadda ya daure fuskarsa ba ta kamo hannunsa ɗaya cikin nata ta shiga murzawa ,a hankali ya ɗan waiga inda take tsaye yana sauke wani wahalallen numfashi tare da ƙoƙarin zare hannunsa cikin nata, tayi saurin matse hannunsa wanda d'uminsa ya soma ratsata ,kafin daga baya ta dawo gabansa ta tsaya suna fuskantar juna ,ta kamo dayan hannunsa ta rike tana kallonsa shima tsura mata kwayar idanuwanshi yayi fuskarsa a haɗe tamkar hadari yana kallon yadda sumar kanta ya hargitse, kasa yayo da idanunshi suka sauka akan pinky lips dinta kana ya lumshe idanunsa sannan ya zare hannuwansa ya juya zai bar d'akin zuciyarsa na dokawa da matsanancin karfin gaske, tayi saurin shan gabansa tana murmushi har fararen hakoranta suka bayyana cikin siririyar muryarta mai daɗin sauraro da jan hankali tace "kana kallona like baka gane ni ba ko ?

ya furzar da iska yana kawar da kanshi gefe dan Kallonta nasa shi jin wani irin kasala gashi har lokacin sanye take da kayan bacci , ta kai hannuwanta duka
ta kamo fuskarsa zuwa gareta ta sanya kwayar idanunta cikin nashi tace "please don't tell me baka gane ni ba nice wacce na kusan bigeka koma nace na ....
yadda ya kafeta da sexy eye's d'insa ko kiftawa ba yayi yasa ta kasa k'arasa maganarta ,yanayin yadda take makale ajikinsa yasa zuciyarsa jin wani abu akanta, wani irin sanyi ya dinga ji a sansar jikinsa kamar ana masa wanka da ruwan sanyi , ta sake shige masa tana son ya tunata "idan ba zaka tuna ni ba ka fada min how did I end up here with you? How?!". Nan ma shiru yayi mata ya kasa bata amsa ta d'aga idanunta sama alamun tunani can ta dawo dasu gareshi tace" ko ka sake taimaka min ne a karo na biyu ?" still shiru yayi mata zuciyarsa na harbawa da karfi "please help me dan Allah ka da'ukeni daga gun wadan nan robbers d'in ?"tsura mishi ido tayi cike da muryarta kamar zatai kuka ta bud'e k'ananun lips d'inta. "Please ka mun magana dan Allah"ta karasa maganar tana zura yatsun hannunta cikin kunnenshi , da sauri ya janyo wani dogon numfashi ya sauke har lokacin bai iya bata amsar tambayoyinta ba saboda bashi da abinda zai ce mata ,idanunshi ya ɗan lumshe tare da matsawa daga jikinta da yake jin kamar ana tsira masa allura kasancewarsa matashi kuma mai karfin sha'awa , sai dai duk da wannan karfin sha'awar nashi ba kowani duri yake iya ci ba ,ita kanta abinda yake cin zuciyarsa kenan ya azabtar daita da baiwar da Allah yayi masa sai dai a daren jiya yaji bazai iya aiwatar da nufinshi akanta ba tausayin mahaifiyarta ne ya d'arsu a zuciyarsa yadda yaga hankalinta ya tashi a lokacin da zai bar gidan daita ,bugu da kari shi kansa yasan illar abinda zuciyarsa taso aikata daita.

a hankali yaja tsaki tare da sake dubanta sannan ya had'iye wani wahalallen yawu gata dai da gani yarinya ce da bazata wuce shekara sha tara a duniya ba amman komai yaji ajikinta , ba komai yafi daga masa hankali ba kamar dukiyar fulaninta dake tsaye suna nema rikitashi da neman zautar dashi gata yar siririya amman duk taku daya sai qirjinta ya motsa ,cike da natsuwa ya raba gefenta zai wuce yana magana can kasan makoshi "me zaki ci ? "bana bukatar komai "Well it seems like baki buk'atar komai bye then". Ya wuce abinsa batare daya sake furta komai ba .
Chapter 6 · 0% Book details