← Book details Kuskuren Baya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 58 OF 160

Sashe 58

Kuskuren Baya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

bayan sati d'aya taga alamun jaguwa ya dan fara saukowa dan har d'akin da take yake shigowa , bata kallonsa haka zalika bata ce masa komai har yayi abinda zai yi ya fita.
da yammacin ranar juma'a a bakin kofa suka yi karo dashi zata fita shi Kuma zai shigo d'akin garin ta matsa masa tayi baya zata fad'i da sauri ya Kai hannunsa ya taro bayanta , ita dake jiran ta ji bayanta ya daki kasan tayis taji saukar hannunsa ya tare ta sauke wahalalle numfashi suka tsurawa junansu Ido suna kallon kwayar idanun juna cike da shauki ko kifta idanunsu basa son yi yayi mata kyau matuka cikin shigarsa ta kullum yake wando da riga sai kamshi turare yake.
sun kusan minti biyar a haka sannan yayi k'okari janye kwayar idanunshi acikin nata
ya tsaidaita bisa kafafunta yana cewa"kin dinga kula ki daina wannan haukan tafiyan "
"haka zalika kaima ka dinga lura da naka haukan shigowan tana gama fad'ar haka ta wuce ta barshi nan yana kallon bayanta tsaki yaja ya gyara zaman rigarsa sannan ya shiga d'akin ya d'auki abinda zai dauka ya zauna zaman jiran dawowarta d'akin ya samu damar cin ubanta la'ada waje amman taki dawowa mikewa yayi ya biyota Kai tsaye falo ya nufa har zai wuce yaji motsin ta a kitchen ya k'araso ya tsaya a bakin kofa ya rike kugunsa da hanun daya wani irin kallo yayi mata na rainin wayo fuskarsa babu alamun wasa ya had'e girar sama data kasa tunda ta waigo taga irin kallon da yake mata Tasha jinin jikinta tare da rikicewa ta d'auke idanunta ta juya masa baya muryarsa a harzuke yace . "ni kike cewa mahaukaci ?
"to menene kake mamaki ?tayi mgnr a dake tana kokarin cire tsoro yayi taku d'aya yana ƙoƙarin damkota ta juyo da sauri qirjinsa ya hade danata  atare suka sauke numfashi wani irin abu sukaji ya bakuncin zuciya da gangar jikinsu sakamakon haduwar da jikinsu yayi ,kasa yayi da sexy eye's dinsa suka sauka akan qirjinta tsurawa qirjin Ido yayi yana kallon tudun dukiyar fulaninta duk da cikin riga suke amman a zahiri yake kallonsu .
wani zirrr yaji lokacin daya tuno yadda yayita murzasu a wancan ranar Ina ma zai sake samun dama irinta ranar ? iya murzasu ma kawai ya ishesa ba sai ya Kai ga saduwa daita ba .
a hankali ta soma k'okarin juyawa ganin yadda yake ma qirjinta kallon kurrilla, yasa hannu ya juyo daita ta sake fuskantarsa ya hade fuskarsa tamau "har Kin isa ki juya min baya ?batace umm ba bare Uhm uhmm illa qirjinta dake dokawa fiyye da kaida "ba'a min back to back sai dai nayiwa mutun ya Bude Baki zai sake yin mgn kira ya shigo wayarsa ya janye jikinsa ya soma received call yana mata gargardi da hannunsa alamun zai ka mata sannan ya fara amsa wayar "okay to shikenan gani nan just give me 10 minit yanzu zaka gani ya juya da sauri ya fita wani naunayen ajiyar zuciya ta sauke ta cigaba da abinda take .."

Mmn sudais

💗💗💗💗💗💗
KUSKUREN BAYA
     💖💖💖💖
💗💗💗💗💗💗

PAID BOOK
FREE PAGE
 WRITING BY
AYSHA .A BAGUDO

WATTPAD @HAUESH

bismillahirrahmanirrahim

Wannan  littafin na kudi ne  mai bukata karanta shi  ya tura 500 ta wannan  account number din  1438775094 Aishat Abdullahi Access bank ,Idan a tura sai a turawa wannan number+234 703 534 8686 alert  domin tabbatar da an tura ko wannan number 08059623096 Idan Kuma vtu za'ayi  sai a tura ta wannan number 08059623096 kada ayi vtu  a number MTN ,domin sauraran littafaina a tuntubi Channel dina ta Hausa bakwai.

🅿️19

Da  misalin  karfe  tara na   daren  ranar  laraba  tanweer   tana    bathroom   tana  wanka  jaguwa   ya   shigo  d'akin  hannunsa  rike  da tabar wiwi    yana   zuga  a hankali  cikin kwarewa   ,warin   bai  tsaya iya d'akin  ba   har  sai daya iskota   bayi  ,   abinda   tafi  tsana  kenan  ta gansa yana  shan  wiwi   Kuma  ta lura ya fahimci  bata son   hakan shi  yasa cikin kwanakin   dan  iskanci  idan zai shigo  sai  ya shigo mata daita  yana sha  ,Idan   ta   kulle  kofar d'akin   ya zama  balai  . "
cikin  fushi  ta  fito sanye  da  doguwar  riga  hannunta rike  da  towel  tana cewa "dan darajan  Allah   ka  daina  shigo  min  kana  Shan wannan abar bana son warinta "kana  da  ilimi amman  kullum   kamar   dabba  kake  abubuwanka,  tsabar shagala  kullum cikin  aikata   abinda  Allah ya  haramta  kake  , wallahi   Koni da  bani  da wani  sani  akan  naka ba zanyi  lalacewa  irin taka   ba, Kaine  Zina , Kaine  sata , Kai ne sha......."

Wani gigitacen mari ya wanka mata  yana  huci   ta  dafe  kuncinta  daidai Inda hannunsa ya sauka  tana  dubansa Ido fal  da  hawaye "akan na fad'a maka gaskiya  shine   ka  mareni ?" to karya ne baka  sata ,baka bin mata , baka..."a tsawace  yace " Kada  ki  sake fad'a min  maganar   banza  idan  kika  sake fad'a  min maganar  banza   wallahi zanyi miki  abinda har ki mutu  ba  zaki manta  dani  ba  ko ubanki  bai Isa  ya Kalli  idona  ya fad'a  min maganar da kika  fad'a min   ba bareki"  .
tayi  shiru   tana   kallonsa ta  kasa  cewa   komai  kafin daga bisani  tayi  kasa da muryarta  ",Allah   ka saka min " ya  sake d'aga hannu zai sauke mata  wani  marin  tayi  saurin kaucewa ta dube shi Ido cikin Ido "da gatana da komai  amman ka d'aukoni  ka rabani da gatana  ka  maidani  jaka to wallahi  na barka da Allah duk abinda ka min ka jira sakamako  " tana gama  fad'ar haka ta juya zata bar d'akin ya biyota  ya shakota ",Ina  zaki  ki dawo ki  gama  tsine min  ",ni ka sakar min wuya  ,bazan saka ba muddin kina son zaman Lafiyarki  a gidan nan  ki iya bakinki  akan abubuwana dan wannan   halin   naki  yana d'aya daga  cikin  abinda  yasa na tsaneki yanzu  sam baki  da  kunya ".
"naji  kaima ka daina abinda zai sa na dinga   maka rashin kunya ,  da  kyar ta sanya  gbdy karfinta ta kwaci kanta tana haki fixgota  yayi  ya maka   akan gado yana mata  wani  irin  kallo  mai  firgitarwa bayan second biyu ya sawa  kofar key  ya d'auki towel din data  fito  dashi  ya   wuce   ya  shiga  bayi    yana  jan tsaki  .
tanweer  ta dafe kanta tana  jijigawa "na  shiga  uku  ni tanweer wani irin iftilai   ne haka  ya fad'a min ?  yawon  zagin  ubana  da yake yana mugun  bata min    rai  kusan  yafi duk wani wulakanci da yake mata  ,da  kyar  ta  rarrashi   kanta  ta  kwanta tana  tunani  adadin   kwanakinta a gidan a lisafinta ta share  wata  biyu kenan  zata  shiga  na uku a hannunsa  tana kwance lamo
 ya fito kungunsa d'aure da  towel  yana goge  jikinsa da alamun  wanka  yayi  gajeren  wondo ya  d'auka  ya saka ya  kwanta kusa  daita  tana ganin haka tayi  saurin  ta matsawa daga kusa dashi dan har lokacin warin wiwi  bai  bar  jikinsa ba  ."

ganin abinda tayi yasa  haushi ya kamashi  cikin fushi ya  fixgota   jikinsa da karfi  ta sake janyewa
ya sake rikota  sosai  "ke kin isa na kwanta kusa dake ki tashi ? "dame kike takama  dashi ? ta  bud'e  idanunta  sosai "bana takama da komai Amman gaskiya ka daina taba min jiki dan ni ba  matarka bace sannan ba karuwa  bace  da zaka dinga had'a jikinka da nawa  bazan  iya irin wannan  rayuwar ba, kawai ka kyaleni  idan bazaka  maidani gidanmu  ba zan hakura  na zauna amman bazan iya wannan shirmen da haukan ba wallahi idan baka farga ka tuba ba ka jira mako.." "ya Isa ! ya isheki haka    jaguwa ya fad'a a  fusace  "ke ni zaki  gayawa maganar  banza   akan  abinda  isana  ya bani  dama  ba".tayi  saurin tashi daga  jikinsa ta  zauna tana dubansa  tace "ban fahimceka ba ?   menene Isan naka ya baka ba ? Yayi  mata  kallon banza kana  yace  "ke mana ni gani nake  kin zama mallakina duk  da  bana sonki kuma dole nayi abinda na gada  dama dake ".ranta ya dugunzuma a fusace tace  "wallahi karya ne , wiwin da kasha ya fada maka  karya  baka Isa  kayi abinda kaga dama dani  ba,  Kuma daga yau ka daina taba koina a  jikina  har sanda zan bar gidan nan tunda bana Uba.. ..."
Ji tayi ya zabga mata mari  a fusace  tare da durowa daga kan gadon Yana  dubanta" Ina gargadinki  da ki iya bakinki  da furta min duk Kalmar  da kika ga dama domin idan  ba haka   zan miki rashin mutunci dan ni ko kusa ban d'auki mace   a komai ba illa abun  bukatata  ki sani Ina da halin da zan aje irinki  guda  hamsim idan naso  dan ma Kinga na barki  haka batare da na aikata wani abun asha dake   ba shine  zaki kawowa  mutane  salo ?
"to ni Ina ruwana idan kaga dama ka cika gidan nan  makil da karuwai   wannan  matsalarka ce  ni  dai  karka  tabani  ".
Ya Isa Inda ya ajiye wayoyinsa  ya  d'auki daya  daga ciki ya duba  lamba  pretty  ya  kira ya sa  a handsfree ringing biyu   muryata ta fito  tana cewa "Allah ya taimaki  jaguwa  uban gidana  , jaguwa yace "pretty  kina Ina ? Ta lankwashe murya kmr tana gabansa  tace "Ina gidansu ogechi yanxu muka shigo gida  "kuzo ku  duka  bai  gama maganar ba tanweer ta k'araso  ta fixge waya  hankalinta  a matukar tashe  da abinda ke Shirin  faruwa, a gabanta zai  kira karuwarsa wannan wacce irin rayuwa ce  ? "Wacce irin rayuwa ya saka kanshi  "ita da wasa tace ya cika gidan da karuwai   shine  zai  kirasu wayyo  Allah na shiga uku "  akansa an kirata da  Kalmar karuwa ,yanzu km zai gayyato karuwai zuwa gidan "to me zai hana ka maidani ka samu damar yin iskancinka  da tushe tunda shine a gabanka ?  tayi maganar a matukar tsorace  dan tunda ya fara da maruka  tasan duka ma bazai masa wuya ba.
Chapter 58 · 0% Book details