← Book details Kuskuren Baya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 128 OF 160

Sashe 128

Kuskuren Baya Part 1 Complete Hausa Novel · about 3 min read

Tana zaune taji ya bude get daga yanayin sallamar da yayi suka tabbatar mata shi kadai ne musamman kafin a shigo babban falon gidan akwai kofa a farko to yana budewa taji lokacin daya mayar yasaka mukulli ya rufe dan haka ta cire dankwali kanta ta baza yalwataccen gashin ta daya sha gyara akan saman kujera tayi tsam tana jiran knowking dinsa
Yana ji ta gyara zazzakar murayarta tana cewa waye ?
“Ki bude mana zaki ga ko waye ?ta dan ji babu dadi amman sanin idan tasa hakan aranta zata gaza abinda tayi niyya ta saka hannu ta bude ta koma ta juya bata tsaya ba sai daya shigo bataji takun tafiyarsa abayanta ba dan haka ta juya idanusnhi kyam akan mazaunnata yana binsu da kallo bai ma san ta juya ba ganin tsayuwar ta ya fuskanci ta juyo shi take kallo .
Ya wani basar kamar ba ita yake kallo ba ya nufi gefe yana cewa “daman tana ta allah allh na dawo na sake kallon film din nan ya fad’a cikin wayamcewa ya dauki remut murmushi kawai tayi , yna bin film da kallo yana son yayi magana amman ya kasa ya dago ya kara kallonta itama shi take kallo ya sauke idanuwanshi akanta tayi saurin cewa “ka fita dazu baka ci abinci ko laifi nayi maku ne kai da yaya shi gaisuwar ma da kyar ya amsa min tayi mgnr a shagwbe Kmr zatayi kuka .”
yayi shiru ya kalli table din duka kamshin turarenta ya cika falon ita kanta tana jin dadin kamshinta ya sunkuyar da kansa “yanzu ma bana bukatar cin abinci ya dan yi gaba zai shiga dakinsa ta sha gabansa da sauri ya dago ya kalleta itama ta kallesa duk da bata iya jurar kallonsa amman haka ta kafeshi da idanunta ya dan gyara tsayuwar da zai wuce ta gefent kara shan gabansa tayi yaci karo daita yaja burki ya tsaya jikinsa yana gugan nata yayi mata kallon mamaki “dan me ka fita bakaci abinci ba mai nayi maka “?Ta fad’a cikin muryar shagwaba ya dan ka baya “hally kema fa rigimammeya ce na rigada naci abinci ai ,kuma meye laifina dan banci abincinki ba ?
Bata karaya ba ta kara shigewa jikinsa sosai kamar zata masa numfashi tace “nifa ban yarda ba dan meye zakaje wani guri kaci abinci ni kuma nawa fa?”
Ya dan yi murmushi yace “to gani nayi har yanzu ina nan amatsayina na wanda bashi da aure kinga dole na koma inda na saba cin abinci naci ta fuskancesa Sarai ta kawar da mgnr “ni dai kaje kaci abincina kuma ka gaya min laifin me nayiwa yayana yake fushi dani”no no bakiyi masa laifin komai ba …” allah nayi masa baka lura da kallon da yake min ba alamun yana jin haushina nace miki bakiyi masa komai ba amman zan masa mgn batasan lokacin data rike hannuwmasa cikin nata ba ta fara murzawa cikin wani irin salo “dan allah ka taimakeni ka kirasa yanzu naji laifina ni bama sai ya fad’a min ba ka bashi hakuri dan allah bana son yayi fushi dani dan nasan nayi wani katoton laifi shiyasa yaki kulani kace masa yayi hakuri ya yafe min bazan sake ba kai ma ka yafe min abinda nayi maka bazan sake ba muje kaci abincina .”

Ya dan murza hannuwanta da dan larfi ta saki kara mara sauti tana hararasa cikin salon wasa gbdy jikinta ya kamo ya rungumeta a qirjinsa “kinyi min kyau my princess ko baki ban hakuri ba bazan Iya fushi dake ba a wannna daren “muje muci abincin ya zareta ajikinsa tare da rike hannuwanta farinciki ya cika qalbinta , tabbas nmj sai da kissa gashi cikin dan lokaci kadan ta samo shi yanzu datasa girman man kai fa ta tabbatar zasu jima a haka a yadda ya dauki fushi daita .”?
Chapter 128 · 0% Book details